ABDULKADIR SALADIN 17

17. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.wordpress.com
...
YADDA GORDON YA MUTU
Da dare, ana gobe wannan bakar kaddara za ta faru, Gordon ya sa aka yi shela a Kahartum aka fada wa mutane su kwana bisa kan shiri. Don ya kara musu karfi, ya sa aka yi ta wasan wuta, ana harba albarushin takarda mai launi iri iri. Aka kare, ’yan badujala suka yi ta kida suna busa. Zuwa can su ma suka yi shiru, gari ya yi tsit, kowa ya shiga daki ya kwanta. Can sai Mahadawa suka yunkuro yuu kamar fara. Sun san duk inda soja su ke, sun kuma san wuri mai karfi, da mara karfi. Sai rabinsu suka zaga suka hudo wa garin ta fuskar Farin Nil, don a nan wajen ganuwa ta fi rushewa. Rabi kuwa suka tari sojan gwamnati gadan gadan. Da soja masu tsare da Farin Nil suka yi dan fufuf fufuf da bindiga, suka ga abin ya fi karfinsu, sai suka tsere.
A lokacin da babbar rundunar gwamnati ke fama da tsare wancan fuska, ba su sani ba ashe Mahadawan da suka bullo ta fuskar Farin Nil suna bayansu. Su dai ba su farga ba, sai suka ji harbi ta baya kurum. A gabansu ga mutane dubbai suna harbi, a bayansu kuma haka. Ganin wannan fa, sai sojan gwamnati suka tabbata am fi karfinsu. Amma duk da hakanan sai da suka dan tagaza, kana daga bisani suka ajiye makamai suka bi. An kashe Misirawan cikinsu da yawa, amma Bakaken Fata sai kadan aka taba. Su Mahadawa kuwa kila sun rasa mutane tamanin ne, intaha dai dari kadai cikin mutanensu dubbai. Aka bude kofar gari daga waje aka turo keyar kamammun nan, aka fito da su, sai sansani wurin Mahadi.
Mahadawa fa suka duru cikin Kahartum da ihu, Allah kadai ya san iyakar yawansu. Ko wanne yana kada bindiga ko mashi, suna guje suna cewa, “Lil Saraya, Lil Kanisa!" Watau, “Mu nufi fada, mu nufi majami’a.” A zatonsu a fada, inda Gordon ya ke, da majami’a, inda Kirista ke ibadarsu, nan dukiya ta ke tare. Suka tasam ma wadannan wurare haikan. A fada, yaran Gordon suka tare su a kofa, kafin kiftawar ido, duk suka kashe yaran. Mahadawa suka tattake gawarsu, suka duru a matakin bene, suka nufi sama inda Gordon ya ke. A can suka sami Gordon yana tsaye a bakin kofa yana jiran isowarsu. Ba shi rike da wani makami a hannunsa, ko sanda. Da zuwansu ya ce, “Ina shugabanku Mahadi ?" Ahaf, sun ma tsaya su ji abin da zai ce balle har su ba shi amsa ? Kawai sai daya daga cikinsu ya shirga masa katon mashi a ciki, ya tsire shi. Gordon ya yanke jiki ya fadi kasa. Mahadawa suka kamo hannunsa suka yi ta jansa a kan matakan bene har kasa. A nan aka sa takobi aka sare kansa, aka sa cikin kwando aka aika wa Mahadi a Omdurman. Gangar jikin kuwa, cikin ’yan minti kadan aka yi kaca kaca da ita. Mutum fiye da dubu suka zo, kowa ya caka mashinsa a jikin, wai abin fahari ne a ga mashin mutum ko takobinsa da jinin Gordon. Kafin a jima dai tsokar jikin ta hade da kashin duk sun yi rugu rugu kamar an daka a turmi. Allah mai girma, irin bakar mutuwar da Gordon ya yi ke nan!
Gordon ya yi iyakar kokarinsa ya tsirad da ran baki, kamar Misirawa da Turkawa da kabilun Turawa iri iri da ke zaune sabo da harkoki dabam dabam a cikin Kahartum. Shi kansa bai kula da nasa ran kamar yadda ya kula da na mutanen nan ba. Ya ba su damar fita daga garin. Ya ba su jirgin ruwa musamman wanda zai iya gudu da su zuwa cikin Masar, amma dai duk rana ta riga ta baci. Shi kansa kuma yana iya kawo rundunarsa ta tsare fada, amma kila in ya yi haka sai a ce yana son ransa ne kadai. Har wa yau ga jirgin ruwa bisa Kogin Nil kusa da fadarsa, tsakaninsu duk bai fi yadi dari uku ba In da ya so, yana iya shiga ya fid da kansa daga halaka. Duk dai bai yi ba. Ajali ya yi kira.
Bayan Mahadawa sun kashe Gordon, gari ya zama na Mahadi. Daga ranar faduwar Kahartum har zuwa kwanaki masu dama a gaba, irin bidiri, da tashin hankalin da ya faru a garin, ba ya misiltuwa. Baki dai ba zai iya fada ba, alkalami ma haka. Mahadawa sun nuna ayyuka masu munin gaske, na gwada wa jama'a azaba, da rashin imani, da mugunta. In ka ga wanda aka bari ba a kashe shi ba, to, yaro ne, ko yarinya mace. Amma babba, ko tsoho, ko tsohuwa, duk wanda aka gani sai kisa. Don tsananin azaba da bakin ciki, wadansu ma hadiye ransu suka yi suka mutu. Wadansu kuwa bayinsu na da, wadanda suka gudu suka koma gun Mahadi, su suka kashe su. Wajen maganar kisa ke nan.
Wajen maganar gwada azaba kuwa, ai sai a yi shiru kurum. Lokacin da mutanen Mahadi suka shigo Kahartum, kowa ya kama gidansa, sai suka shiga buruntu a cikin gari, su ga inda dukiya ta ke. Duk mutumin da aka yi zaton yana da dukiya, an dinga gwada masa azaba ke nan iri iri, azabar yau dabam, ta gobe dabam, sai ya nuna dukiyar. Mafi sauki cikin irin azabun nan, ita ce a yi ta yi wa mutum bulala a baya sai bayansa ya taye, tsoka tana reto. A kan kuma sami tsarkiya mai karfi a daure magamin farcen babbar yatsan hannun mutum, kana a daure a itace ya rika lilo. Don tsananin zafin wannan har wadansu su kan suma. Wadansu kuwa kwantad da su a kan yi rigingine su yi ta duban rana, tun hantsi har la’asar. Kai, sai dai a ce hanyoyin azabar Mahadawa sun wuce misaltuwa kurum. Wadansu cikinsu, ayyuka ne na ban kunya game da mata. Wadannan ayyuka ko dabba kila ba za ta iya aikata su ba, balle wai mutum mai hankali, kuma wai yakin jaddada addini ya ke yi. Saboda haka bari in saki maganar azabu, in ci gaba da labari kurum, don fadinsa ba shi da amfani.
Amma kafin in ci gaba, ya kamata in nuna wani aikin butulci na halin dan Adam. Akwai wani Kwara, attajiri, ana kiransa Fathalla Gehami wanda ya binne kudinsa jakankuna a gidansa. Babu wanda ya sani duniyan nan, daga shi, sai mata tasa, sai wani yaronsu. Shi kuwa wannan yaro, tsintarsa ya yi tun yana kankane, yana galabaita da yawon iska a titi. Gehami ya kawo shi gidansa, da shi da mata tasa suka raini yaron nan har ya girma. Su ne cinsa, su ne shansa, sutura, wurin kwana, duka su ne. Kai, ba shi da da uwa da uba duniyan nan sai su. Su kuma ba su yi masa rikon bara da ubandaki ba, sai suka rika shi kamar dan da suka haifa.
To, ran nan da Mahadi ya sauka a kofar Khartum, sai Gehami ya yi kiran yaron, ya ce da shi, “Kai Muhammadu, ka sani ni ne uwarka, ni ne ubanka. Tun kana dan kankane na ke rike da kai. Na yarda da kai kamar yadda zan yarda da dan cikina, har na nuna maka inda dukiyata ke binne. To, yanzu ka ga al’amari ya rude, kila gobe war haka gidan nan ba nawa ba ne. Kai kuwa dan kasa ne, kana da ’yanuwa. Sabo da haka sai ka tafi wurin ’yanuwanka. Idan Allah ya sa gwamnati ce ta yi nasara, shi ke nan sai ka dawo. In kuwa Mahadi ne, to babu wanda ya san abin da zai same mu, sai Allah. Amma na ba ka amana, kome ya faru, kada ka bude bakinka ka gaya wa kowa duniyan nan inda kudina su ke. Shi ke nan Allah ya tara mu.”
Kwana biyu tsakani, sai Mahadi ya shiga Khartum, A cikin ruguntsumin nan na waso da Mahadawa ke yi, sai yaron nan ya kwaso ’yanuwansa, ko wanne ya rike mashi, ya nufo gidan ubangidansa Gehami. Suka tarar an garke kofa kam. Sai ya shiga dukan kofa, gam, gam, gam, yana cewa, “Maigida bude, ni ne danka Muhammadu !" Da jin muryarsa, Gehami ya bude kofa. Yaro da ’yanuwansa suka kimsa kai ciki. Da shigarsu sai ya girgiza mashi, ya dankara wa Gehami a kirji, ya tsire shi, ya jefar waje guda. Suka nufi inda kudi su ke. Suka hake, suka kwashe su kaf.
Wai duk wannan butulci, da aikin rashin imani ba su isa ba, sai Muhammadu ya sake jawo mashi zai dirka wa matar Gehami. 'Yanuwansa suka rike shi, yana kyarma, yana cewa, “Ku bar ni in kashe ta.” Da kyar dai suka kwace mashi daga hannunsa, suka tura keyarsa waje, suka bar matar da bakin cikin mutuwar mijinta, da mamakin yadda za a saka alheri da mugunta haka.
Duk dukiyar da aka samu a Kahartum, da ’yam mata da yara maza an kwashe an kai baitulmali. Kashegarin faduwar garin, ran nan Mahadi da shi da Halifa Abdullahi suka shigo, domin a Omdurman su ke zaune. Sai ran nan suka ketaro Nil a wani jirgin gwamnati da a ke kira Isma'ilia, wanda suka kama. Mahadi ya tara rundunarsa duk ya shiga musu godiya. Ya ce wannan bala’i da ya fada wa Kaharturn ba abin tausayi ba ne, don kuwa Ubangiji ne ya saukar musu da shi sabo da martabarsa, shi Mahadi, sabo kuma da sabon mutanen garin.
Kwana biyu da faduwar Kahartum, ina zaune sai ga sojan Mahadi su biyar. Da zuwansu suka ciccibe ni, da ni da sarkata, suka aza a kan jaki, suka kora sai babban kurkuku. Na yi mamakin yin haka, ban gane dalili ba sai daga baya! Ashe cikin takardun Gordon da aka tarar har akwai wadansu da ya aika wa jama’a. A ciki ya ce na rubuta masa ga Mahadi nan, amma kada ya ji tsoron kome don Mahadi ba shi da karfi, kuma ba shi da makamai. Na tabbata Gordon ya yi haka don karfafa zuciyar mutanensa ne kurum. Wannan takarda ita ta sa aka kara zargina har aka jefa ni a kurkuku dungum. Zaman kurkuku duk ba shi da dad'i, ammna zaman kurkukun Mahadi ya fi na ko ina wuya a duniya. Wajen maganar wurin kwana da abinci, sai na ga ashe lokacin da na ke kwana kan keson karaunu, a aljanna na ke, a bisa yanzu. A babban kurkuku, tsabar hatsi danye a ke ba mu, kowa tafin hannu guda. Shi za mu tsuka mu yi kalaci, mu rage mu ci da rana, mu rage mu ci da dare. Tafi guda fa kadai!
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D61EAFAE
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)