ABDULKADIR SALADIN 18

18. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.wordpress.com
...
Kwana biyu da faduwar Kahartum, ina zaune sai ga sojan Mahadi su biyar. Da zuwansu suka ciccibe ni, da ni da sarkata, suka aza a kan jaki, suka kora sai babban kurkuku. Na yi mamakin yin haka, ban gane dalili ba sai daga baya! Ashe cikin takardun Gordon da aka tarar har akwai wadansu da ya aika wa jama’a. A ciki ya ce na rubuta masa ga Mahadi nan, amma kada ya ji tsoron kome don Mahadi ba shi da karfi, kuma ba shi da makamai. Na tabbata Gordon ya yi haka don karfafa zuciyar mutanensa ne kurum. Wannan takarda ita ta sa aka kara zargina har aka jefa ni a kurkuku dungum. Zaman kurkuku duk ba shi da dad'i, ammna zaman kurkukun Mahadi ya fi na ko ina wuya a duniya. Wajen maganar wurin kwana da abinci, sai na ga ashe lokacin da na ke kwana kan keson karaunu, a aljanna na ke, a bisa yanzu. A babban kurkuku, tsabar hatsi danye a ke ba mu, kowa tafin hannu guda. Shi za mu tsuka mu yi kalaci, mu rage mu ci da rana, mu rage mu ci da dare. Tafi guda fa kadai!
Ran nan sai muka ji hargowa a kofar kurkuku, ashe wai Halifa ne ya zo duba fursuna. Ni dai ko kadan ban saka zuciyar samun wani rangwame ko afuwa gare shi ba. Amma don gudun karin azaba, sai na kira duroba mai gadina, na tambaye shi yadda ya kamata in yi in Halifa ya zo wurina. Duroban ya ce kai dai ka tausasa harshenka, ka kuwa ba shi amsar ko wace tambaya nan da nan. Kada kuma ka yi kukan cewan wani abu ya dame ka, ko ka yi tsiwa.
Halifa ya shiga zagaya fursuna, ga mu an jera kamar awaki. Ya shiga yi wa ’yanuwana tambayoyi iri iri. Wadansu aka sake su, wadansu aka ce a cire musu sarka. Zuwa can ya iso kaina, sai ya ce, “Abdulkadir, anta tayeb ?" Watau, “Abdulakadir, kana laiiya ?" Na amsa masa nan da nan na ce, “Ana tayeb, Sidi." Watau, “Lafiyata lau, ya shugabana.” Sai ya shige, amma wani dan'uwansa Yunus Wad Dekeim da ke biye da shi, sai ya duko ya rada mini cewa, “Kada ka karai, sakinka za a yi.”
Haka kuwa aka yi, don bayan kwanaki masu dama, ran nan sai aka ce Halifa zai zo duba kurkuku. Jin haka sai na shirya jawabin da zan yi masa in na sami sarari. Na tsara zance mai kyau, mai ma’ana, a zuciyata, na yi ta maimaita jawabin nan sai da ya zauna sosai da sosai a kirjina. Kwamfa ran nan sai ga Halifa ya zo a wata safiya. Yana shiga ya sa aka kafa masa tanti ya zauna, ya ce duk a kawo daurarru gabansa. Aka kai mu aka jera mu, ya shiga tambaya da dai dai. Ya saki ’yan kadan wadanda shi ne ya daure, wadanda alkali kuma ya daure, amma ba su yarda da shari’ar da aka yi musu ba, ya ce zai bincika maganarsu. Duk ya kare, amma ni ko dubo ni bai yi ba. Sai na ji ya ce wa duroba, “Akwai sauran wani abin da zan yi kuma ?” Duroba ya ce, “Ya shugabana, sai yadda ya yi maka dadi.“ Har ya tashi, sai ya koma ya zauna ya dubo ni ya ce da larabci, “Abdulkadir, kana lafiya ?” Sai na taro hankalina wuri daya na ce, “Ya shugabana, in ka yarda zam fada maka halin da na ke ciki.” Ya ce ya yarda.
Na mike tsaye na ce, “Ya shugabana, ka tuna fa ni bako ne a Sudan. Na zo gare ka don neman tsira, ka kuwa karbe ni, ka tsirad da ni daga halaka. Maganar kuskure kuwa kada ka manta, ya shugabana, wannan gadon dan Adam ne duka. Muna saba wa Ubangiji, muna kuma saba wa junammu. Na san na yi laifi mai yawa, amma na tuba , ka yafe ni don Allah da Annabinsa. Ka ga yadda na ke cikin sarka. Ka ga yadda na ke cikin tsiraici. Ka ga yadda yunwa ta maishe ni fata da kashi. Kwanciya ma a kan doron kasa na ke yi, dan keson tabarma ma yau ya fi karfin arzikina. Na kuwa saduda, na bi, kuma na zuba ido har ran da ya yi maka dadi ka yafe mini. In har yanzu bai yi maka dadi ka sassauta mini wannan ukuba ba, ina rokon Allah ya ba ni karfin jiki da na zuciya yadda zan iya daukar abin da ka aza mini. Amma ni dai rokona da kai, ya shugaba, ka hakura ka yafe mini laifina, ka raba ni da wannan azaba.”
Na haddace wannan Jawabi ya fi sau goma, sabo da haka ko kwata ban yi ba lokacin da na ke magana. Ko da na dubi fuskar Halifa, sai na ga lalle zancen ya tsima shi. Ya ta da ido ya dube ni, ya ce, “Na Ji jawabinka, Abdulkadir. Amma ka sani tun ran da ka zo Darfur na yi ta maka iyakar taimakon da za a yi wa bako irinka, amma duk a banza. Ka nuna amincewarka da mu ta fatar baki ce kurum, ba ta kai zuci ba. Ka yi ta kokarin ka tsere mana ka tafi wajen kafirin nan Gordon, ku yake mu tare. Da ya ke kai bako ne shi ya sa ban ce a kashe ka ba, ba don haka ba da yanzu ba ka ma a duniyan nan. Amma zan yafe maka yanzu, in da gaske ka ke, ma gani, in kuma da munafunci ne, ma gani. Kai duroba cire masa sarka.” Kafin su kare bude bakin sarkar an yi minti ya fi talatin. Duk abin nan Halifa yana zaune. Da aka kare suka kawo ni gabansa. A nan ya ce duroba ya kawo Alkur’ani, aka rantsad da ni bisa kan ban gaskiya ga Mahadi har zuciyata. Na rantse, ya mike ya ce im bi shi.
Ko da ya ke Halifa yana kan jaki ne irin babban nan da a ke kira dambahar, amma da kyar ni ke iya cim masa. Kafata ta riga ta saba da tafiyar sarka, don wata takwas na yi cikin mari. Ga mu nan dai sai gidansa. Aka ce in dakata a kofa. Zuwa can ya ce in shiga. Da shiga ya kama yi mini gargadi, sa’an nan ya ce ya sami wasika daga sarkin yakin gwamnatin Masar, cewa sun kama dangogin Mahadi a yakin Dongola. Amma in ana so su sako su sai a sako duk Kirista da ke tsare a hannun Mahadi. Ya ce, “Mun yi shawara za mu ba su amsa, mu ce musu ku yanzu duk Musulmi ne, sabo da haka ba ku yarda ku rabu da Mahadi ba. Amma ko kila kun fi so ku koma gun Kirista?” Daga nan bai ci gaba ba, sai ya yi shiru. Ko da jin jawabin nan nasa na san wani tarkon ne kuma aka sake kafawa don a koma da ni cikin ukuba. Nan take na ce masa ni ai kuma da ni da komawa gun Kirista har abada. Jin dadin wannan zance nawa har ya ce a kai ni wurin Mahadi.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D61EAFAE
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)