19. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.wordpress.com
...
Ko da ya ke Halifa yana kan jaki ne irin babban nan da a ke kira dambahar, amma da kyar ni ke iya cim masa. Kafata ta riga ta saba da tafiyar sarka, don wata takwas na yi cikin mari. Ga mu nan dai sai gidansa. Aka ce in dakata a kofa. Zuwa can ya ce in shiga. Da shiga ya kama yi mini gargadi, sa’an nan ya ce ya sami wasika daga sarkin yakin gwamnatin Masar, cewa sun kama dangogin Mahadi a yakin Dongola. Amma in ana so su sako su sai a sako duk Kirista da ke tsare a hannun Mahadi. Ya ce, “Mun yi shawara za mu ba su amsa, mu ce musu ku yanzu duk Musulmi ne, sabo da haka ba ku yarda ku rabu da Mahadi ba. Amma ko kila kun fi so ku koma gun Kirista?” Daga nan bai ci gaba ba, sai ya yi shiru. Ko da jin jawabin nan nasa na san wani tarkon ne kuma aka sake kafawa don a koma da ni cikin ukuba. Nan take na ce masa ni ai kuma da ni da komawa gun Kirista har abada. Jin dadin wannan zance nawa har ya ce a kai ni wurin Mahadi.
Rabona da ganin Mahadi an dade, tun ran da aka ce in rubuta wa Gordon wasika. Yanzu da na gan shi sai ya sake mini. Da mutum ne shi siriri, amma yanzu ya yi kiba mulmul. Haraji, malam! Na durkusa a gabansa na yi gaisuwa. Ya karbi gaisuwata, sa'an nan ya ce shi babu abin da ya ke so illa ya ga hankalina ya kwanta. Ya kuma tabo maganar ’yanuwansa da Ingilishi suka kama, da maganar hurhure. Ya ce, “Na ki maganar hurhuren nan, ko da ya ke ’yanuwana ne zan kwato. Ni na fi son ku da ’yanuwana.” Na san wannan duk game baki ne, sai na yi farat na ce, “Ya shugabana, mutumin da bai so ka fiye da kansa ba, yaya sonka zai shiga zuciyarsa ?” Sai ya ce, “Sake fadan abin da ka ce mu ji, Abdulkadir !" Ya juya wurin Halifa ya ce masa, “Saurara ka ji." Na ce, “Mutumin da bai so ka fiye da kansa ba, ya Mahadi, yaya sonka zai shiga zuciyar sa ?” Mahadi ya ji dadi, ya ce, “Wannan gaskiya ne, Abdulkadir, ka so ni fiye da kanka.”
Da muka koma gidan Halifa sai ya ce, “To, Abdulkadir ina ka ke son ka tafi ? Kana da wani wanda zai taimake ka, ya kula da kai a Kahartum?” Na ce, “Ban da Allah, da kai, duk garin nan ba ni da kowa.” Ya ce, “Abin da na ke zato ke nan. Daga yau kuwa ka zama dan gidana. Zan kula da kai, ba za ka yi kukan kome ba. Amma ka rabu da kowa, ban yarda ka rika cudanya da wadansu a waje ba, sai yaran gidan nan kawai. In gari ya waye za ka zo nan ka zauna a bakin kofa, in akwai wani sako a aike ka. Lokacin da na shiga, kai kuma ka koma gidanka. In na hau, za ka bi ni a kasa, ka shiga cikin barorina, ’yan amin. Ka yarda da sharuddan nan ?” Na ce, “Na yarda, na kuwa yi matukar godiya.” Za ka same ni lalle ni amintaccen bara ne.” Ya mike ya ce, “Allah ya taimake ka rike su. Ni zan shiga gida, amma sai ka kwanta a nan zaure har kafin gobe kuma mu sama maka gida.” Ya shiga ya bar ni ni kadai.
Ko da ya ke a yanzu ma da kadan na fi fursuna, amma na yi wa Allah godiya. Ni da ke da gidan kaina, da barori, yau ga ni ina kwana a zaure, na zama baran wani. Wata irin barantaka kuwa, wadda ba mu gada ba a kasarmu, watau ubangidanka ya hau doki, kai kuwa kana gabansa a kasa, kowa ya gaishe shi ka ce, “A gaishe ka.” In dai gajarce muku, na zama zagi.
Kashegari da Halifa ya fito, ya sa aka kira kanensa Yakubu, ya ce ya ba ni gida. Bayan am ba ni, ya tambaye ni, “Ya Abdulkadir, da ya ke kai Musulmi ne, ina matarka?” Na ce, “Ai mace guda ke gare ni, na kuwa bar ta a Dafur.” Ya ce, “Nasara ce ’yaruwarka ?“ Na ce, “A’a, mutumiyar nan kasar ce, ’yar mutanen Dafur. A yakin da muka yi da Sultan Haruna aka kashe uwarta, da ubanta, ta zama marainiya, ni kuwa na aure ta.” Ya ce, “Kun haihu da ita ?” Da ya ji na ce a’a, sai ya ce, “Ai mutumin da ba shi da da, kamar itacen da ba ya ’ya’ya ne, sai kaya. Ba shi da wani amfani. Sabo da haka zam ba ka mata, don ka ji dadin zaman duniya.”
Ran nan na dawo daga gidan Halifa da dare, sai wani yarona na da, wai shi Sa’adalla, ya zo ya ce wai ga wata kuyanga Halifa ya aiko mini da ita. Na yi dariyar wannan sakarci a raina, na ce Sa’adalla ya kunna fitila mu je in gan ta. Ko da na shiga dakin da aka ajiye ta, sai na ga. tarin abu kim, kamar tarin tsumma. Na tambaye ta asalinta, ta ce daga kudancin Kordofan aka kamo ta aka kai ta baitulmali. A lokacin nan ta kware lullubinta, ta bude fuskarta da kirjinta. Na ce Sa’adalla ya matso da fitila. Ko da na dube ta, saura kadan im fadi kasa don firgita. Na ga wata irin halitta wadda muninta ba ya misaltuwa. Ga ta dai baka kirin kamar bayan tukunya, ga hanci kamar an taka, ga ’yan kananan ido kamar na bera, can a kwarmi. Lebban bakinta sai ka ce an tsaga kabewa don kauri, bakinta kuwa don fadi kamar zai tabo kunnenta. Dan kanta kut, kamar na biri. A jiki kuwa ta yi girman katti uku. Tir! Wannan mace da muni ta ke! Na tambaye ta sunanta, ta ce Maryama. Nan da nan na ce wa Sa’adalla, “Fid da Maryama daga dakina, ka sake mata daki.”
Safiya na yi na tafi gidan Halifa. Yana ganina ya ce, “Abulkadir, ka ga sakona jiya ?" Na ce, “Na gani, ya shugabana, amma dai ba ta yi mini ba ko kadan. Duk duniya babu mai munin wannan mata da ka ba ni." Na bayyana masa duk yadda ta ke. Ya yi fushi gaya, ya ce a kira Ahmed Wad Sulaiman, ma’ajin Sudan, wanda bayi ke hannunsa. Da ya zo, ya diram masa da fada, ya ce ya je ya sake mini wata matar kyakkyawa. Ni a raina duk wannan aikin banza ne, don ba ta mace na ke ba, ta kaina na ke. Sulaiman dai ya sako mini wata yarinya fara, mai dan kyau. Na mika ta gun yarona Sa’adalla, na ce cinta da shanta suna hannunsa. Ni kuma na ci gaba da zuwa aikina na barantaka a gidan Halifa, daga wayewar gari zuwa kwanciyar barci.
MAHADI YA MUTU
Ana cikin masha’a, kowa na cin ganimar da ya samu, manyan sarakunan Mahadi ko wanne ya kama gida babba na sumunti, ya cika da mata da kwarakwarai. Ran nan kwaram sai ga wani sabon labari. Aka shiga rade raden wai Mahadi ba shi da lafiya. Wadansu suka yarda, suka yi ta rokam masa sauki. Jahilai kuwa suka ce karya ne ba shi yiwuwa Mahadil Muntazir ya yi ciwo! Ba a fara gaskata wannan labari ba, sai da aka yi kwanaki ba a ga ya zo masallaci ba. Duk da haka jahilai dubbai ba su yarda yana wani ciwo ne matsananci ba. Dalilin rashin yardarsu don Mahadi ya sha gaya musu, cewa am fada masa a wahayi, wai sai ya ci Makka da Madina, ya gyara addini sa'an nan zai wuce zuwa Kufa a Falisdinu, a can za a dauki ransa.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D61EAFAE
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada