Ba Rashin Kunya Ba Ne, Gaskiya Ce Zan Fada!!!

Ba Rashin Kunya Ba Ne, Gaskiya Ce Zan Fada!!!


 

Daga Hauwa'u Gidado.

Rayuwar 'ya mace akan siradi yake tun daga shekara 5 har zuwa girmanta.

A shekara 5 ana fara aiken mace zuwa siyan pure water biscuits ko kayan miya saboda a ganin iyaye cewa ta isa aike ne
amma da zarar taje shago sayan abu mai shagon in zai amsa kudi wurinta sai ya haďa da hannun ta ya matse ko ya shafa mata hannu, wanda in bata da wayo baza ta taba daukar hakan wani abu ba, idan mai wayo ce tana tsoron iyayenta amma baza ta iya fada musu cewa ana taba mata hannu in an aiketa ba.                                                                 

Ba iya masu shago kawai suke haka ba har da sauran mutane da ake da alaka dasu yau da gobe.

Daga wannan lokacin da yawa zasu rinka yaudarar ta da biscuits ko alawa da kudi don kawai ta rinka zuwa suna saka mata hannu a pant... Idan akayi mummunan rashin sa'a sai ayi raping dinta tana da kananan shekaru.                                            
Duk hakan yana faruwa saboda tana karama bata da wayo kuma tana tsoron sanar da iyayenta.
Da zarar ta kai shekara goma zuwa sha daya anan zata gane cewa ta fara girma abinda ake mata ba daidai bane ba.

Lokacin da jikin mace ya fara nuna alamun girma a shekara sha uku zuwa sha hudu surar jikinta ya fara bayyana, a hanyar makaranta ko aike ko wani abu zata rinka gamuwa da masu dangwale mata nono suna guduwa ...wata tayi kuka wata ta share amma hakan yana mata zafi a ranta.

Da mace ta kai 15 years samari zasu fara tururuwar zuwa wurinta wanda kashi 99.9% ba aure ya kawo su ba kuma ita ma a wannan lokacin ba lallai aure za'a mata ba...

A nan za'a samu wanda yafi kowa dadin baki da iya zance ya sace mata zuciya ita kuwa ganin ta duk duniya shi kadai yake sonta yake kaunar ta, duk wanda zai gaya mata gaskiya kawai gani take cutarta zai yi ya raba ta da masoyin ta.

Da ya samu dama daga 15-20years zai raba ta da budurcinta wurin amfani da kalamai kamar haka..

•Kin Fi So Na Je Na Nemi Mata a waje? 

•In Baki Taimaka Mini Ba, Waye Zai bani ?

•Ba kya Kishina ?

•Sau Daya Kawai.

•Muna Sabawa Allah Kuma In Mun Roke Shi Zai Yafe Mana.

•Ba Za'a Gane Ba A Gida.

•Ni Zan Aure Ki, Bazan Taba Rabuwa Da Ke Ba Har Abada!!!

Da sauran wasu kalamai na yaudara, Ya Allah ka kare 'ya'yanmu , iyaye kuma a kara kulawa!!
Post a Comment (0)