Eznah 23

*_EZNAH_*🌹
       _wattpad@mamuhgee_





*23*


Komawa yayi kusada general ya tsaya yana kallonta gabansa na fa'duwa coz idan har itace tayi bazata ta6a yarda tace itaceba
Idan Kuma ta amince that explain alot but Bari yagani...

Yawu ta ha'diye wasu hawaye masu zafi suka gangaro Mata Dan kuwa tana tsaka Amma batajin zata iya Bari wani Abu yasamu saheeb Dan haka ta bude idanuwanta dabata ganin komai murya na rawa tace,

I don't know how i....
Shiru tayi takasa qarasawa sbd rawar da muryarta keyi..

Uhumm..... general yace Yana jiran sauran maganar.

Bansan ya akayi naturaba sbd bansan Kan laptop dinba....

Idan bakisan Kan laptop ba meyasa Kika dauka mezakiyi dashi...

Kusan atare itada zayyan suka ha'diye wani mugun yawu zufa na qoqarin karye musu cikin tsananin tashin hankali dan shidai zayyan yasan dazarar hakan baiyi aikiba sun Kade suma Dan kuwa Sai sunyi prison...

Qura Mata ido yayi Yana adduar Allah yasa tanada qwaqwalwa....

Ita kuwa Sai yanxune taqara sanin dalilin kashe Mata idanuwa dankarma taga mutanen dake gurin ko kuwa taga zayyan yayi Mata wata alamar....

Ha'diye yawu tayi cikin rawar murya tace,

Na dauka ne sbd nayi game.....

Rintse idanuwa zayyan yayi cikin tashin hankali da fargaba yace,

We're dead...sbd yasan za'a Duba laptop din kuma bawani game aciki.

Dama kinayin game da laptop din ne?

Eh""""tace Kai tsaye....Amma jiyan kodana Duba ya gogesu duka sbd dama ya hanani dauka..

Meye sunanki....?

Hassana salisu 'danja.

Miss hassana salis We've known Kanal major abdulshakur saheeb for almost fifteen years and for all these years bamu ta6a ganin wasarsaba ko fara'arsa infact bama gane farin cikinsa,,baqin cikinsa,damuwarsa kowane irin yanayinsa ma so ke from the barground of wat you're saying kin shaqu dashi ta yanda kike iya daukar laptop dinsa datake daukeda sirrika da dama da abubuwa masu mahimmanci wat is your relation with him?

Sister"""ta fa'da Kai tsaye...

Kanal has no sister...cikin muguwar tsawa da qarfi yace,

Who are you to him..? Sbd so suke su rikitata ta fa'di wani abunda zasu iya gano wani Abu Amma the girl seems to be very smart and clever.

Wata gigitacciyar tsawar yakuma sakar Mata Yana cewa,

Speak,,who are you in kanal abdulshakurs ho.....

I'm his fiance, his wife to be'''
Ta fa'da da qarfi cikin kuka sbd gaba 'daya sun birkita Mata qwaqwalwa batasan Mai zataceba Dan gaf take da fa'dar gskia gashi ba mutum daya ke Mata tambayarba sbd su qara rikitata.

Tsit sukayi Sai sautin kukanta dake tashi cikin room din ahankali..

Zayyan mutuwar tsaye yayi Jin abinda tafada saidai fatarsa Allah yasa hakan yayi aiki sbd already akwai camera datake daukarta direct zuwa can headquarter inda manyansu gaba daya suna gani Nan aka hau fafata zance ana qara tsananta bincikawa.

Sai yamma ris suka kafin aka budeta wasu soldiers Mata suka riqota danko tsayuwa Bata iyayi gashi Bata gani suka fito da ita har cikin motar zayyan yatada motar ahankali ya nufi gida da ita.

Jabiru Maigadi na ganinsu yaje yakirawo gwaggo datu safe take matsar hawayen neman ananon hakama Kamal ga farin cikin samun nasara ga takaicin rashin ganin ananon haka yafita nemanta.

Gwaggo kamar zata kife ta fito tana ganin fuskar ananon duk akumbure ga gefen bakin jini daya bushe ga Kuma idanuwa basa gani.

Hannu ta Dora akai tareda fashewa da kuka tana cewa,

Yau ni hindatu nayi mugun gani mezan gani Anano tashin bomb akayi kina kusa?

Cikin kulawa zayyan yace,

Gwaggo akula da ita idon zai bu'de kafin safe ki neme qyalle ki jiqa da ruwan sanyi ki Dora Mata agurin ni Lagos Zan wuce yanxu mutaho da saheeb.

Duk da tana cikin mummunan Hali saidatai saurin dagowa murya can cikin maqoshi tace,

karka fa'da Masa komai Dan Allah.

Dole zai sani...
Girgixa Kai tayi hawaye na gangaro Mata asanyaye tace,

Koda zai sani karkace nice sbd banyi danya San ninayiba.

Janta gwaggo tayi tanata matsar hawaye tana cewa,

Shikenan ni yanxu kin makance yazanyi mezan cewa baffa.

Kallo yabita dashi cikin tsananin mamaki Dan kuwa Sai yanxu yatabbatarda qwaqwalwa basai Mai waye da ilimi kawaiba kowa da baiwarsa Allah ke halittarsa koma meyene zaiji zai sani idan yadawo.

Acan headquarter kuwa cikin awanni ashirin saheeb ya 'dandani baqar azaba Dan kuwa kusan awanni goma yayi cikin 'dakin qanqara gashi he's allergic to sanyi ko ka'dan jikinsa Bai son sanyi Amma dayake zuciya tagama cinyesa haka aka sakashi Nan take fatarsa tafara wani iri kamar zatai sa6a awanni goma aka fiddosa aka mayar shocking room nanma dai Kam yaci mummunan azaba Amma yaqi yarda ya amsa laifinda baimasan ta inda yafaroba.

Washe gari
Bayan anyi duk binciken daza'ayi dakuma bayanan Anano ankai ruwa Rana da wasu manyan dabasa son saheeb din kafin aka Kai qarshe aka yarda dabashi yayiba aka sakesa tareda kar6e star dinsa biyu cikin hudu daga kanal major yadawo qasa major kawai....
Aiko Nan 'yan jarida da talabijin suka fara yadawa musamman da aka fito dashi Nan aka fara kakkaresa sbd Yan jarida gashi gabaki 'daya ko tsayuwa sosai baya iyayi direct jirginsu aka shige dashi akayo gida dashi.

Motocinsu na sojoji suka daukesa aka nufi gida dashi cikin mugun gudu masu motoci da mashin Sai kaucewa suke Dan labarai sun gama yada ko'ina ansan yau sojojin yola kaf ransu a6ace yake anta6a kanal major saheeb Dan kuwa suna tsananin sonsa.

Tunda jabiru yajiyo jiniyarsu ya bu'de gate yabarsa bu'de Dan idan yayi wasa yau duka da tsallen kwado zaici Dan sun Saba horar dashi idan suka dawo agujen Nan yayi sanyar bu'de gate...

Abu kuwa dama Yana Jin yaune dawowarsu yayi sauri gyara parking motocin Abba yashigar dasu qurya danshima yaficin wahalarsu sbd shegen tsoronsa.

Tunda motocinsu suka shigo gidan Abba yafito cikin tsananin damuwa Dan kuwa tun jiyan yake cikin wani Hali na damuwar saheeb din.
Abba da zayyan ne suka kaisa har bedroom dinsa suka kwantar Nan zayyan yayi gaggawar Kiran Dr sbd saheeb din nabuqatar Dr sosai.

Mum asee datun safe da labarin sakin saheeb din yakusa sheqata lahira sbd baqin ciki ta fito tareda qaqalo murmushi da farin cikin Dole na ku6utarsa nufi part dinsa.

Dr na zuwa ya dubasa yayi Masa allurori masu qarfi da magunguna kafin aka sallami kowa sbd baason kowa ya damesa for now.

Soldiers biyu sukaja suka tsaya bakin qofar part din duk Wanda yazo basa barinsa shiga harsai oga saheeb din yatashi yabada umarnin abar mutane shiga.

Zayyan kuwa mota Yakoma ya aika jabiru yakira Masa Anano.

Zaune take tsakiyar dakin tanacin abinci kamar batasonci itada abdul Sai wasarsa yake  idanuwanta sun bu'de Amma a kumbure suke sumtum har wani nauyi suke Mata.

Gwaggo kuwa tana kicin tanata hidimar dafawa saheeb abinci.

Tunda taji dawowarsa gabanta ke fa'duwa zuciyarta na tsananin son ganinsa Koda daga nesa ne Amma batajin zata iya.
Sallamar jabiru ce a qofa ta katseta ta amsa Masa cikin sanyin murya yafada Mata oga zayyan nakiranta tayi saurin kallon qofar Amma tuni jabirun ya wuce ta ha'diye yawu daqyar cikin tsoro tace,

Allah ka kawomin qarshen zamana Nan gidan konayi sauqaqaqiyar rayuwa kamar kowa.

Miqewa tayi tareda 'daukar abdulshakur jiki a sanyaye taje kicin takaiwa gwaggo shi ta Goya sbd Sam Bata cika son fita dashiba sbd zagi da aibantashi da'ake.

Tunda ta hangosa jikinta yafara rawa ta daure ta qarasa tareda sunkuyar dakai tace,

Ina wuni?

Cikin kulawa ya amsa tareda tambayarta ya jiki.

Da sauki tace a sanyaye..
Shiru tayi tanason tambayarsa ya saheeb tana tsoro
kamar yasan metake tunani yace,

Saheeb na ciki Yana hutawa sbd yayi weak sosai sbd sanyin daya shiga qashinsa sosai
Amma insha Allah he'll be fine idan yatashi.

Hmmnn nikam ai yanzu na tabbatarda bawanda yakai sojoji mugunta tunda Naga zahiran a idanuwana.

Katse mata tunani yayi ta hanyar cewa,

Idan bakya komai Zan kaiki gurin wani Dr ne yaduba idanuwan.

Girgixa Kai tayi tace,

Aa naji sauki tunda gashi Ina gani.

Murmushi yayi sbd ya hango tsoro qarara a idanuwanta Amma ai baiga laifintaba Danma tayi qoqari Sosai Dan tamatuqar burgesa.

Lalla6a yayi daqyar tabisa bayan taje tasanarda gwaggo.

Wani private asibiti yakaita aka dubata tareda Bata magani kafin suka baro.

Wani qaton shopping mall yabiya da ita shikadai yashiga yayo siyayya Mai yawa Suka nufo gida Yana 'dan janta da zance tana amsa Masa ahankali.

Suna shigowa harabar gidan Kamal nafitowa daga part dinsa ya tsaya kallonsu cikin uban mamaki da 6acin Rai 
Tana ganin haka tahau yaqewa zayyan baki tana amsa Masa zancensa cikin sakewar fuska.

Qwafa yayi ya wuce afusace Dan  badan sojojin dake gurinba saiyazo ya 6alla musu rashin mutunci Amma yasan Yana zuwa ubansa sojojin zasuci barema Daman idan saheeb na gida basa Bari atada hayaniya hardai yanxu da baida lafiya.

Please for godsake ku ringa sanin comment din dazakuyi karfa ku manta novel ne ba reality ba and fiction ne fa so meyesa kuke magana akan wannan is kaza,
Wannan is not kaza,,,,,gsk am not happy da yanda wasunku ke magana akan lallai Bai kamata ace anyi wannan ba,anyi wancan ba....
Please kufadi alkhairi ko kuyi shiru.

Anyways my wattpadian I love you guys so much sbd Ina ganin kulawarku sosai but please kuyi voting kuyi sharing not only comment 😍

# vote
# comment
# share

Post a Comment (0)