Eznah 24

*_EZNAH_*🌹
        _wattpad@mamuhgee_




*24*
Tana ganin ya shige ta kalli zayyan tace,

Nagode Zan shiga ciki.

Siyayyar dayayo Mata ya fitar tareda miqa Mata manyan ledojin takallesa zatai magana yace,

Apologies and thank you......

Girgixa Masa Kai tayi zatai magana yarigata da cewa,

For Allah's sake karkiyi magana ki karba..

Kar6a tayi tareda godiya ta juya tabar gurin yabita da kallo zuciyarsa na kar6ar abinda ke shigarsa akanta duk da dai yanason magana da ita sosai akan abubuwan dasuka faru Amma yabari saita warware duk da dai zuciyarsa na hararo Masa wani alamari acikin zuciyarta gameda saheeb.


Washe gari Inna da ciwon Kai Mai tsanani ta tashi tun Daren jiyanma take fama dashi..
Tana tashi ta Mike ta nufi hanyar fita Anano dake gyarawa abdul lullu6i takalleta tace,

Gwaggo Ina Kuma zakije?

Karin safiya Zan dorawa saheeb Kinga shima ba lafiyarne dashiba.

Keda bakida lafiya gwaggo kiyi zamanki zanyi Miki aikin.

Idanuwanta dabasu gama hucewaba gwaggo takalla zatayi magana takatseta....

Zan iya gwaggo zoki huta.

Miqewa tayi ta nufi kicin din gabanta na fa'duwa...
Cikin qanqanin lokaci ta ha'da Masa breakfast lafiyayye tarasa yazatayii tashiga palonsa takai masa.

Rintse idanuwa tayi tareda sauke numfashi ta dauka ta bu'de qofar palon ahankali tashigo.

Tsaye yake bakin fridge na dining area din ya Ciro Power horse zaisha kayan baccine black ajikinsa Sai suka qara fito da hasken fatarsa sosai....

Cak ta tsaya jikinta na'dan rawa sbd Sam batayi tsammanin ganinsaba kallo daya tamasa tayi saurin 'dauke idanuwanta cikin nasa tareda saurin qarasowa ta aje zata juya suka qara hada ido ya dauke Kai tareda tsuke fuska

Komawa tayi ta 'dauko sauran abincin tadawo wannan karon yabar gurin Yakoma tsakiyar palon ya zauna Kan kujera.

Sake hada idanu sukayi murya na rawa tace,

Ina kwana?

'daga power horse din hannunsa yayi yakai baki baiko kalli inda takeba bare ya amsa.

Harara ta watsa Masa tareda turo baki Aiko Sai Akan idonsa
Wani kallo yasako Mata zai dako Mata tsawa tun kafin maganar ta fito ta fice da sauri tana cewa,

Ni kullum da masifaffi Allah ke hadani hunnn.
Tun safen kamalu keson ganinta ta lafe cikin daki raqi fitowa yayita Aiko asabe tayi biris taqi zuwa

Sai Da yamma zayyan yazo ya Aiko kiranta tafito cikin doguwar Rigar blue atampa da qaramin hijab.

Kallonta yayi cikin kulawa suka gaisa tareda Yar fira sama sama ya wuce part 'din saheeb.

Part din mum asee ta wuce Dan dubo asabe dataita zaryar dubata kwana biyun.

Tana shiga taji an fixgota da qarfi tareda jefota tsakiyar palon saidata bugi centr table gefen bakinta ya fashe ta 'dago da sauri taga Kamal yana wani irin huci kamar zai buga ya sake damqo gashinta dake cikin hijab da qarfi cikin 6acin Rai yace,

You ingreat bitch so nawa Zan fa'da Miki Babu shegen dazaki kula bayan ni Amma kinqi ji 
Bakisan rufa Miki asiri ne zanyiba na taimaka muku keda that bastard thing you called son 
Ke bandama qaddara mezanyi dake da bastard son dinki.....

Cikin baqin ciki da hasala ta katsesa tareda miqewa tsaye tace,

Karka qara Kiran yarona da shege sbd ba shege bane Dan haka ka janye tausayi da taimakonmu dazakayi ka rufa Mana asiri sbd har abada bana buqatar taimako ko tausayawa daga gareka afterall Mena sama yaci bare yaba na qasa,,,
Karka Kuma Kiran sunansa sbd inason abuna ahaka duk da Yana shege Zan iyayin komai akansa Dan kuwa dakasan yanda nasamesa naci wuya akansa na yafe gatana sunana mutumcina da iyayena akansa nazo Nan nasan zaka tabbatarda idan nace maka Zan iya komai akansa zaka yarda Dan haka karka Kuma shiga rayuwata da yarona bakasan wacece Anano ba
Yaron dakake Kira bastard yafika Dan kuwa Bai dauko halayen shegunba ko 'daya saima Kaine kakeda kaf halayensu harma.......

Hannu ya 'daga a zafafe zai wanketa da Mari mum asee ta riqe hannunsa tanabin Anano da wani irin kallo Dan dama tana palon zaune itada Kamal kafin ananon tashigo....

Lallai dama ance 'dan iska na qauye...ta fa'da cikin zuciyarta 
Taji zafin maganganun ananon sosai Amma qarfin zuciyarta da iya fitsararta tareda son datace tanayiwa shegen 'danta zatai komai dominsa su zatayi amfani dasu tayi amfani da ananon ta jefi tsuntsu biyu da dutsi daya,,,ta cimma burinta,,ta wargaza ananon bayan ta sheqa shegen danta lahira..

Murmushi tasakarwa ananon bayan ta sauke hannun Kamal tareda cewa,

Bakada hankaline zaka daki mace 
Kai kullum cikin zafin Rai da rashin hakuri..fice kaban guri mutumin banxa kawai.

Kallon mamaki yabi mum din dashi tamasa alamar ya wuce
Ya wuce Yana qwafa kamar zai tashi sama.

Kamo hannun ananon tayi suka zauna a kujera ta kalleta tace,

Karki saka alamarin Kamal arai haka yake kamar Mai shaqar cocaine.

Mamakine yakama Anano ganin yanda mum asee ta sakar Mata tasan akwai abunda zata qulla 
koma meyene zatabita yanda takeso.

Murmushim yaqe tayi tana goge gefen bakinta da tissue dinta mum asee din ta miqo Mata tace,

Bakomai aina Saba da halinshi zuwa yanxu.

Mamakin Anano mum asee tasakeyi ganin yanda take Kai tsaye tayi murmushin mugunta tace shege baqauye...kafin ta fuskanci ananon dakyau tace,

Kince kinason 'danki,,,bakyayi Masa sha'awar kyakkyawar rayuwar hutu da ingantaccen ilmi da Jin da'din rayuwa..

Kallon mamaki Anano tayiwa mum asee

Mum asee tace,
Eh sbd naji kince zakiyi komai akansa..

Ina Masa addua da fatar hakan...

To idan nace Miki ga damafa Wadda zakiyi arziki 'danki yayi sunan Mai arziki hakama akiraki da uwar 'dan Mai arziki
'danki yayi kyakkyawar rayuwa yasamu ingantaccen ilmi...

Zaro idanuwa Anano tayi
mum asee tasaki wani shi'umin murmushi tana cewa,

Yes idan har Zaki iya tsayawa kice saheeb shine uban 'dan shegenki,
Ki tsaya kice shine yamiki cikinsa Kika haifesa.....

Miqewa tsaye tayi da sauri tsoronta na fitowa qarara Dan Bata ta6a kawo wannan shine abinda mum asee zata fa'daba..

Zaunar da ita mum asee tayi tace,

Kar kiji tsoron kowa idanhar Zaki iya nizan tsaya Miki akomai.

Tana kallon tsakiyar idanuwan mum asee 'din cikin tsananin mamaki tace,

Meyasa zance 'dana 'dansa ne...?

Sbd samun cikakken iko akan dukiyarsa...

To ai a musulunce 'dan shege baida gadon ubansa...

Ba wannan Zaki dubaba yanxu cigaban 'danki da naki Zaki Duba.

'dana bazai ta6a samun iko daga dukiyarsa ba Dan ance 'dansane tunda ba aurene atsakaninmu ba..

Aurenki zaiyi.....

Miqewa tasake yi cikin tsananin mamaki da fa'duwar gaba da zancen yasata.

Muryarta na rawa tace,

Ta Yaya?

Ta nice Zan saka ubansa yasashi aurenki Dole sbd yayi Miki ciki kin haihu...

Cikin 'daga murya takatseta da cewa,

Duk menene dalilin dazaisa ayi hakan.

Murmushi tasaki tareda miqewa tana kallon ananon da tuni zufa yafara jiqata sbd tashin hankali tace,

Dalilin hakan shine Ina buqatar takardu ahannunsa Kuma bazan ta6a samunsuba Dole saita hanyar matarsa.....

Girgixa Kai Anano tayi idanuwanta na cikowa da hawaye murya na rawa tace,

Bazan iya ba..

Zaki iya.

Bazan iyaba ki aura Masa yakurah.

Dole Sai kece zakiyi sbd 'dankine zai Zama dalilin auren.

Bazan iyaba"""ta fa'da hawayen idanuwanta na gangarowa sbd mum asee tafara wuce tunaninta.

Janyota tayi da qarfi tareda cewa,

Dolene kiyi idanba hakaba Zaki 'dauki gawar shegen 'danki da gwaggonki a hannunki Dan bazakiji sirrina abanza ba.....ta bu'de qofa ta hankadata waje da qarfi ta kife a qasa.

Qafafun mutum tagani agabanta ta 'dago da sauri gabanta na fa'duwa tayi Ido biyu da zayyan fuskarsa ta ka'da tayi jajir..
Miqewa tayi jiki asanyaye tareda sunkuyar dakai zata wuce ya sha gabanta tareda nuna Mata hanyar gym room 'din saheeb da hannu fuska.

Ganin yanayinsa ba sauqi yasa ta nufi inda yake nuna Mata Dan tsoron karta Kuma Shan azabar dazata sakata rasa idanuwanta.

Suna shiga ya rufe qofar tareda zaunawa Kan wani machine ya dafe kansa idanuwansa na qara canzawa...

Rakubewa tayi cikin tsoro duk da itama tana cikin tashin hankalin.

'dagowa yayi ya kalleta ciki wani irin yanayi yace,

Me saheeb yayi muku arayuwa dakuka za6i Zama masu farautar dukiyarsa da rayuwarsa....

Girgixa Masa kai tayi cikin sanyin murya tace,

Qaddaratace takawoni Nan Kuma nasan qaddara zata daukeni daga Nan din sbd na fado cikin mutanen daban ta6a ganiba arayuwa,,,,,

Qaddarar taimako ita tarabani da komai nawa harna kasance cikin wannan mummunan halin...

Kuka tasaki ahankali tana cewa,

Tabbas zasu kashe gwaggo da abdul matuqar banyi abinda sukaceba sbd nasan zasu iya fiyeda hakan Dan sunsha yi.

Kallonta yayi tereda matsowa ya fuskanceta yace,

Tabbas tun farko nayi zargin cikin gidannan basa qaunar saheeb sbd abubuwa da dama Amma bantaba tunanin hakanba...

Cikin qureta da Ido yace,

Waye yasa abisu Abba last time?

Kallonsa tayi da jajayen idanuwanta Dan batason shiga wata masifar bayan Wadda take ciki yanxu
Yanda ya tsareta da jajayen idanuwansa yasa ta bu'de baki ahankali murya na rawa tafara zayyano Masa komai ta 'dora da fa'din ,

Sun kashe matar saheeb da Mai aikinsu hakama Abba na cikin layi nasan zasu iya kashe gwaggo da abdul bazan iya zamaba tafiya zamuyi..

Dafe kansa yayi Yana karanto innalillahi sbd zancen ya girgixasa matuqa musamman mutuwar nafeesa.

Cikin rawar murya yace,

Idan tabbas nafeesa kasheta akayi da ciki ajikinta shima sun cire..

Dagowa tayi takallesa gabanta na tsananta fa'duwa.

Bazaki je ko'ina sbd duk inda kikaje zasu biki.

A tsorace ta 'dago hawayenta na qara gudu tana girgixa Kai tareda ficewa da sauri tana sakin sabon kuka.




Vote
Comment
Share

Post a Comment (0)