GA MATA MASU SON GYARAN FUSKA

*GA MATA MASU SON GYARAN FUSKA* 👇😚
Mata da dama na sha’awar samun fata mai haske kuma mai sheki. Gaskiyar magana ita ce, ba zai yiwu mace ta dada haske a cikin kwana daya ba. Amma akwai abubuwan da za ta yi domin samun irin wannan launin fatar da take so. Don haka ne a yau na kawo muku irin abubuwan da za a yi domin samun fata mai haske kuma mai sheki daga dakin girkin uwargida ba sai an je kasuwa ko manyan shagunan sayar da kayan kwalliya ba.

• Kurkum; yana dauke da sinadaran haskaka fata da kuma warkar da tabon fuska. Yana da kyau a kasance tare da shi. A samo zuma cokali biyu sannan a kwaba da garin kurkum sannan a rika shafawa a fuska na tsawon mintuna talatin a kullum kafin a shiga wanka. Yana dada wa fatar jiki haske.

• Timatur; yana dauke da sinadarin ‘lycopene’ wanda ke taimakawa wajen haskaka fata. Idan har ana so a dada haske a sati daya, sai a markada timatur sannan a matse ruwan lemun tsami a ciki sannan a shafa a fuska da wuya a kullum na tsawon mintuna 20 kafin a wanke.

•Ruwan ‘rose’;  idan ana son amfani da wannan hanyar don dada hasken fuska, sai a rika diga shi a cikin man shafawa, yana sanya fata laushi da kuma haske. Ko kuma a samu garin alkama sannan a kwaba da ruwan ‘rose’ sannan a shafa a fuska da wuya na tsawon mintuna 20 kafin a wanke.

•  Zuma da lemun tsami; wadannan ababen na saurin sanya fata yin haske da kuma sheki. A samu zuma da  lemun tsami sannan a kwaba su a rika shafawa a fatar fuska da jiki sannan a barshi na tsawon mintuna 30 sannan a wanke kamar sau biyu a rana safe da yamma.

• Kurkum da madara; a kwaba garin kurkum da madara sannan a shafa a fuska a kwana da shi. Washegari a wanke. Yana sanya fuska haske da kuma sheki.

• Fiya da gurji; a markada fiya da gurji sannan a rika shafawa a fuska na tsawon mintuna 30 a kullum kafin a wanke. Yana sanya haske da kuma shekin fata.

• Masu karatu su gane cewa a cikin ababen da na lissafo, guda daya yakamata mutum ya yi amfani da shi domin samun sakamako mai kyau. Amfani da su duka a lokaci daya na haifar da kurajen fuska.

Post a Comment (0)