KAJI AIKIN HANKALI


Wata Rana Wani Alkali Daga Cikin Magabata Mai Suna; Abu Yusuf(Wanda Shi Ne Babba a Cikin Almajiran Imam Abu Hanifah(R) Yana Tafiya Tare Da Abokanansa Sai Suka Ji Wani Matashi a Cikin Wani Masallaci Yana Magana Akan Gudun Duniya.
;
Sai Abu Yusuf(R) Ya Cewa Abokansa: 
;
"Mu Shiga Cikin Wannan Masallacin Ina Son Na Yiwa Wannan Matashin Wasu Tambayoyi, Idan Ya Amsa Mana Sai Mu Zauna Mu Saurare Shi".
;
Lokacin Da Suka Shiga Cikin Masallacin Sai Abu Yusuf(R) Ya Tambaye Shi Cewa:"Ya Kai Saurayi! Ba Mu Labari Game Da Yadda Ake Sallah???", 
;
Sai Wannan Saurayin Mai Suna Hatim(R) Ya Ce Da Su:"Shin Kuna Tambayata Ne Dangane Da Ladubanta Ne Ko Kuwa Yadda Akeyinta a Aikace???", 
;
Sai Abu Yusuf(R) Yayi Mamaki Ya Ce:"Ka Ji Saurayi! Mun Yi Masa Tambaya 'Daya Shi Kuma Ya Mayar Da Ita Tambayoyi Biyu(2), Ba Ni Labari Dangane Da Ladubanta???".
;
Sai Hatim(R) Ya Fara Da Cewa:
;
"Ladubanta Su Ne:
;
*. Ka Tashi Bisa Ga Bin Umarnin ALLAH Ta'ala,
*. Ka Nufi Masallaci Domin Neman Lada,
*. Ka 'Daura Niyyah,
*. Ka Yi Kabbara Tare Da Girmamawa
*. Ka Yi Karatu a Nitse Tare Da Jerantawa
*. Ka Yi Ruku'u Da Kushi'i
*. Ka Yi Sujjada Da 'Kan'kan Da Kai
*. Ka Yi Tahiya Da Tsarkakakkiyar Niyyah
*. Sannan Ka Yi Sallama Cikin Rahama.
;
Sai Abu Yusuf(R) Ya Qara Cewa:"To Ka Bani Labari Dangane Da Yadda Ake Yinta".
;
Sai Hatim(R) Ya Ce:
;
*. Ka Sanya Ka'aba a Tsakanin Goshinka,
*. Ka Sanya Mizani a Tsakanin Idanuwanka
*. Ka Sanya Sirad'i a Karkashin Kafafuwanka
*. Ka Sanya Aljannah a Hannun Damarka
*. Ka Sanya Wuta a Hannun Hagunka
*. Ka Sanya Mala'ikan Mutuwa(a Bayanka Yana Nemanka), 
*. Kuma Ka Sanya a Ranka Cewa Sallarka Za'a Kar6ane Ko Kuma Za'a Mai Do Maka Da Ita.
;
Sai Abu Yusuf(R) Ya Ce:"Ya Hatim! Tun Yaushe Kake Irin Wannan Sallah???" 
;
Sai Hatim(R) Ya Ce:"Tun Shekaru Ashirin(20) Da Suka Shud'e Har Zuwa Yanzu".
;
Daga Nan Sai Abu Yusuf(R) Ya Juyo Wajen Abokansa Ya Ce Da Su:"Ku Zo Muje Mu Gyara Sallolinmu Na Shekaru Hamsin(50) Da Suka Wuce".
;
TAMBIHI;
;
'Yan'uwa Masu Hankali, Mu Tashi Mu Nemi ILMIN IBADA Da HUKUNCI, Ba Lalle Sai Mun Zamo Malamai Ba, A'a Mu Koyi Yadda Za Mu Bautawa UBANGIJINMU.
;
Mu Tuna Cewa ALLAH Ta'ala Ba Zai Ta6a Kar6an Jahilci a Matsayin Uzuri Ba. Neman Ilimin Addini Wajibi Ne Akan Kowanne Musulmi Namiji Da Mace. Kamar Yadda Muka Kasance Muna Neman Duniyarmu, Mu Zamto Masu Neman Lahirarmu Fiye Da Duniyarmu. 
;
Kada Mu Zamto Wadanda ALLAH Ta'ala Yake Zarginsu Da Cewa: 
;
"Ya'alamuna Zahiran Minal Hayatiddunya Wahum Anil Akhiratihum Gafilun".
;
Ya ALLAH! Ka Sanya Mu Cikin Masu Tsayar-Da Sallah Kwatankwacin Yadda SAYYIDUL-WUJUDI(S.A.W) Ya Koyar, Ka Sa Muna Cikin Wadanda Idan Aka Duba Sallolinsu Sun Ci 'Screening' Na Shiga Aljannah Ameeen.
Post a Comment (0)