KULLUM SAI AURE YA MUTU

🌹 *_KULLUM SAI AURE YA MUTU_*🌹

🌹Jiya wani ďan'uwa da yake aiki a wani Shari'ah Court yake ce mun: "Kullun zan iya miki rantsuwa da cewa babu garin Allah da zai waye face sai an raba *AURE*, kuma sabbin aure sun fi yawa. Wata uku, hudu ko 1 year. In fact, yau dinnan sai da aka yi wani case na mutuwan aure kuma kullun kenan aikin."

🌹Sai nake tambayarsa akan duka raba auren da ake yi menene babban matsalar da ya fi fahimta kuma ya fi yawa (aka fi kashe aure dominsa). Sai yace: "Gaskiya ni abunda na fahimta shine kamar haka, 1. Wasu daga iyayen matan ne, wato iyayen yara basa bincike sosai kafin su bada auren 'yarsu. Ba sa binciken mijin da zasu ba ma auren. Sai daga baya wasu hallayensa marasa kyau su bayyana musu bayan an yi aure. Wanda da sun bincika da sun gane hakan at the beginning da ba a bashi aure ba." 

🌹Kun gani babba abun da ya fi kawo mutuwar aure shi ne *KWADAYI DA SON ABUN DUNIYA.*

🌹Idan har 'yan mata basu cire kwadayi ba da son kuďi daga cikin agendan su ba to kawo qarshen mutuwar aure a qasar hausa ba abu ne mai sauki ba. Idan mata suka cire kwaďayi to tabbas kashi casa'in na maza zasu daina qarya don mace ta so su.

🌹Na san mata zasu ce ina supporting maza but ku auna shi da common sense, a cikin mata kashi goma ne kaďai basa kallon kuďi da kyale-kyalen duniya kafin su yi aure. Ta fi so yayi qarya domin ta yi Alfahari a cikin mutanenta. 

🌹Waďanda ba su nuna son abun duniya ba a mata mazan suka zo suka musu qarya suka yaudare su basu wuce 2% ba a cikin ďari. Abu mai wuya ka ga mace tana wa saurayinta mai kudi soyayyan gaskiya. Zata yi ta masa rawar kafa kamar tana son shi, tana shiga ta ga babu kuďin ko ya daina bata sai ta daina son shi ta daina masa biyayya. Naga irin wannan da yawa wallahi.

🌹Yanzu in dai namiji yaje da kuđi gidansu yarinya abu mai wuya su bincike sa, in ma sun bincikesa sun gano laifinsa still za a bashi aure koda duk yan unguwarsu sun masa shaidan banza. Sai ace in ta aure shi zai canza. Shiyasa kuwa aure ba zai shekara ba ya mutu. 

🌹Yaa Allah Ka tsarkake mana zukatan mu, mu rinka yin abu dominKa, shine yake yin kyau kuma yake qarqo.

Rubutawa:- Sadiya Lawal Abubakar
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

 ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.


Post a Comment (0)