*Mata Kala Kala suke*
Mace ta farko: mace mai iya mu'amula da mutane amma ba ta da riko da Addini.
Irin wannar matar za ka same ta ta iya mu'amula da jama'a maza da mata, cikin sauki ba girman kai.
Idan tayi aure ta iya zama da miji, da dangin miji kawayenta da danginta, duk sun mata kyakkyawan shaida a kan kyawun hali.
Babbar Matsalarta shi ne; ba ta damu da riko da addini ba, ba ta damu da Abubuwan da ya shafi Islamiyya ko abu na Shari'a ba.
Idan aka zo batun Islamiyya ba ta damu ba, ba don takurawa na iyaye ko namiji ba, da ba za ta je Islamiyya ta koyi Addini ba.
Ita dai damuwarta kallon film, da karatun novels, a nan take koyon darasinta.
Ba ta damu da lokacin Sallah ba, sai ta ga dama za ta yi akan lokaci.
Ba ta damu da ta nemi sanin abu akan addininta ko hukuncin abu cikin addini ba, ita dai damuwarta rayuwa ta duniya.
Ba ruwanta da kamun kai, ita dai kowa nata, ita ce daura hotuna a social media da sauransu. Ita ce komi na yayi in ya fito tana ciki komi na burgewa.
Irin wannar matar, idan aka ci sa'a ta samu miji mai rarrashi tare da kulawa, kuma mai son addini, kuma tana matukar kaunarsa, to zai iya daura ta a kan hanya mai kyau halayyarta ya gyaru, tun da tana da kyawawan hali, hakan ba zai sa ta kin karbar gaskiya ba.
Iyaye idan suka tsaya da addu'a aka nuna mata kyakkawan kulawa za ta iya canjawa.
Irin wa'ennan mata mafi yawansu suna da saukin kai. Kuma irin wa'ennan mata masu iya mu'amula amma addini ko oho ba su damu da shi ba suna da yawa a cikin mata.
Mu'amula idan ta yi kyau ya ke yar uwata ana yiwa mutum kyakkawan zato, amma 'yar uwata ki tabbatar ba ki wasa da Sallah.
Ki tabbatar ba ki wasa da Sallah!
Kuma ki tabbatar kina kokari wajen neman ilmi addini da neman sanin hukunci abun da ba ki sani ba.
Ki sani cewa fara'a na da kyau da iya mu'amula da mutane amma ke mace ce mai daraja, ba kowani namiji ne za ki tsaya kina mu'amula da shi ba, bakinki ya dawo kamar agogo wajen gaisuwa ko surutu ba.
In za ki yi mu'amala ki yi da mutane masu kirki da riko da addini, ki zamo mai tsoron ALLAH a duk inda kika kasance.
Duk wani wanda ba muharraminki ba, ki yi mu'amula da shi yadda Musulunci ya tsara.
Yawaita tuba ga Allah, yawaita neman gafarar Ubangiji, yawaita aikata alkhairi, riki Sallah, Azumi da Xakkah.
Riki addini ki hada da kyakkawan dabi'a taki, ki kyautata zato ga Allah, sai Allah ya miki sakayya da gidan Aljannah.
✍Rasheedah Bintu Abubakar (daughter of Islam)