MATA SAI FA MUN GYARA


http://sirinrikemiji.blogspot.com/2018/08/mata-sai-fa-mun-gyara.html

👹 Wasu daga cikin dalilan da ke sanya *jinnu* shiga jikin mu fiye da maza. Duk wanda ya san matarsa ko 'yarsa na yi ku gyara musu:

👹 *1.* Zama a bakin qofa, ko bakin windo da sauran hanyoyin wucewa.

👹 *2.* Fesa turare mai qarfi yayin fita, ko kuma fesa turare lokacin kwanciya bacci mai qarfi kuma ba addu'a.

👹 *3.* Yawan yin zanen lalle mai fulawa a madadin asalin na gargajiya. Wanda aljani da kanshi ya fad'i cewa kwalliyar su ne a jikin wata.

👹 *4.* Zama babu ďankwali a cikin gida, da kwanciya babu shi. Ko bayyana gashin a fita waje.

👹 *5.* Yawan zama ba tsarki, kamar in an yi an gama da dare kawai ta kwanta babu tsarki cikin qazanta. Kuma babu ko alwala har gari ya waye tangararan. 

👹 *6.* Rashin yin alwala a lokacin jinin al'ada da barin yin dukkan addu'o'i. Mafiya yawa in tana jini sai ta yanke dukka komai har sai ta yi tsarki. Wanda hatsari ne sosai.

👹 *7.* Yawaita fushi da sanya damuwa a rai koda yaushe. Domin wata da aljanar ta shige ta cewa ta yi kullum in ta zo wuce wa zata ga tana bakin ciki da damuwa. To wai ita ma aljanar irin halin da take ciki kenan sai ta shigeta. Idan ta na magana ita kaďai na baqin ciki sai aljanar ta rinqa amsa mata tana rarrashinta. Daga karshe dai ta shigeta, in aljanar na baqin ciki sai ta rinqa yanka jikinta da wuka. Wanda matar ma haka ta koma yi.

👹 *8.* Caba ado na gani na fada a fita musamman ga wacce bata yin azkar. Da gyara adon in an samu wuri a waje ko a cikin mota. Domin ita ma wata a nan jinnun ya shige ta. Yace ta tsaya a titi ta fito da powder ta qara shafawa ta gyaggyara. Shi ya zo wucewa sai ya ga gaskiya yana sonta.

👹*9.* Zama a wuraren da aka san suna zama. Kamar wuri da koda yaushe ke da danshi, zama tsakanin inuwa da rana (rabinki a rana rabi a inuwa). Qin shiga bandaki da addu'a ko dankwali. Ko yin waqe waqe a banďaki.

👹 *10.* Shagala da duniya da yawa. Bana manta wani Ruqya da na kalla na wani bature ďan America. Aljanu ne a jikinsa sun kai 10 wanda a dalilin badala ya samo su. Sai suka sa ya zama mutumin banza sosai. Wani daga cikin aljanin da ya shigo jikinsa aka ce shi kuma me yake sanya shi? Ya ce party. Duk in da aka ce za a yi party to aljanin zai takura sa har sai ya je wurin sun gwangwaje. To kana iya gamuwa da jinnu mai irin zunubinka ko dabi'unka na sa'bo sai ya shiga, ya sanya ka yin fiye da abun da ya same ka a kai. 

👹 *11.* Shiga kasuwa babu addu'a. Ko shiga daji ko wani wuri da babu mutane sosai ba tare da addu'a ba. Akwai wani jinnun da ake magana da shi a jikin wata yarinya akan irin halittun da yake zama. Sai yace har da kare, kadangare, maciji, da jemage. Ya ce ya taba zama kare ne ya ci ji wani mutumi bayan ya shiga daji ya taka shi. Shi kuma in an ta'ba shi baya yafiya. Aka ce ina mutumin yanzu, ya ce yana can yana wahala da ciwonsa na sa masa ciwo. Kenan in zaki shiga irin wadannan wurin sai a yi addu'a a nemi tsari daga su.

👹 *12.* Yawon dare, fitan magriba, sharan magriba, wankan magrib. Dauko ayyuka a magriba. Domin Annabi (SAW) ya fada mana a lokacin suke barbazuwa. To in so samu ne a dan bari magriban ya gitta sai a yi. Kuma ki rinqa qoqarin kammala ayyukan ki kafin nan. Da nutsa yara.

👹 *13.* Zubar da ruwa mai zafin gaske. In kin wanke shinkafa ko kin yi per boiling ki yi banza da shi har ya huce sai ki nemi tsari (Auzu billaahi minash shaydanir rajim) ki zubar. Saboda wurin kwata da wanke-wanke suna da danshi da qazanta. Haka nan da zubar da bola da tsakar rana musamman in akwai wani abu na glass da ya fashe a ciki. Wanda in kin watsa in akwai wani abu zai iya jin masu ciwo. Haka nan zubarwa da Magriba.


Post a Comment (0)