TUN KAFIN AURE 20

TUN KAFIN AURE💐20
Ke kada ki raina min hankali mana. Ya daga zuwana zaki  ce wani zaki shiga gida. Ya kara kankance ido irin na 'yan duniya ko kina son nayi miki irin abinda wanan matsiyacin yayi miki ne a wadannan pictures din? Gyara zama tayi tana kallonshi. Kaddai ace a hotunansu da Saif ya ganta. Tasan ance a hoto ya ganta amma bata da details din abinda ya faru. Da kyar tace wane hoton kake nufi ne. Wata babbar waya da bata taba gani ba ya dauko ya nuna mata hotunan. Gabanta ne ya fadi a tsorace ta mike wallahi ni ba yar iska bace idan ma abinda ya kawo ka kenan. It was my first and it will be my last in sha Allah. Tafi ya rinka yi tana magana eyye! eyye yarinyar ta iya turanci ashe. Kunya taji ta kamata shi kuwa ya cigaba da magana. Kar ki damu fa Juni has done worst amma tunda naga babanki yana pretending kamar ke saint ce ba komai shiyasa ma zan aure ki. Daga nan har muyi aure zanyi kokarin dena kula wasu matan sai ki dage ki koyi jan hankalina. Da wuya ake impressing din Juni. Yana gama magana ya tashi ya good night Hafsi Hafsi. Daga bakin kofa yayi blowing mata kiss. Sai da ya fita taja wani numfashi. Lallai akwai matsala ina ita ina wannan mai zubin 'yan iskan.
*********************
Fuska ba annuri ya shigar mata daki ba ko sallama. Junaidu abin ya motsa ne ka shigo min daki kai tsaye. Dafe kai yayi oh sorry Hajiyata raina ne a bace. Dan murmushi tayi tana nuna masa wurin zama. Zo nan dan Hajiya bani labarin yadda kuka yi da Hafsa. Kara zumburu baki yayi wai don rainin hankali baki ga yadda take min wani irin kallo ba. Hajiyan dangi dariya tayi ya bita da ido me kuma ya faru kike min dariya? Yo dannan banda abinka ji irin shigar da kayi kamar wani tsohon dan tasha. Duk kayan jikinka sunyi maka yawa. Lah Hajiya gayun kenan fa. Black americans hadaddu ai irin shigar nan suke irinsu ice cube, snoop dog, kanye west da....kafin ya kara magana ta daga masa hannu dakata haka. Yanzu don Allah zaka iya kawo min sunayen Annabawa ko Sahabbai goma? Ka rasa wanda zakayi koyi dashi sai makiyan musulunci? Kaji tsoron Allah Junaidu ka gyara rayuwarka. Yanzu dubi wani gashi a kanka kamar juji kuma nasan kana sane ka tara shi. Kana girma kana kara cin kasa. Bakin nan na Junaid kam yayi tsine saboda yadda yake zumburo shi..dan me zaayi masa fada. Sai dai kuma maganar ta dan shige shi. Ya mike zai fita daga dakin Hajiya kiyi hakuri da yardar Allah zaki ga na zama salihin mutum ko, yanzu ma ai kinsan Juni yayi sanyi. Filo ta jefe shi dashi ya gudu don yasan ta tsani Junin nan da ake kiransa.
*******************
To baiwar ciki ina nan ina ta nema miki mafita wurin Juni ke banda ci babu abinda kika iya. Tilly ta hadiye naman da ke bakinta da kyar kin dai sanni tun farkon haduwarmu ina da son abinci musamman idan akwai nama. Rosie ta bata fuska to naji mayya amshi ki karanta wannan. Dafe kirji Tilly tayi me zan gani haka? Aure zaiyi, ai wallahi uban kuturu yayi kadan. Ni fa banda kudinsa shima kansa ina so. Wata takardar Rosie ta mika mata tace to wanan kuma fa. Ci...ci...ci me? Mun shiga uku Rosie ya akayi kika bari ciki ya shige. Rosie ta dakatar da ita tsaya kiji ai cikin nan shine license dinki  for now. Ke dai ki saurare ni da kyau kinsan tunda muke bamu taba yin babban kamu irin haka ba dole mu rike wuta.
****************
Nafisa da Hamida sai shirye shirye suke dan uwansu zaiyi aure. Kashe kudi suke kamar babu talauci a nigeria har sai da mommy tayi magana. An hada lefe na gani na fada a cikin gidan daga baya Senator ya yi musu gine mai kyau babu abinda bai saka ba yace a nan zasu zauna har sai yaga kamun ludayin zaman nasu don bai gama yarda da dan nasa ba.
A kano ma su maman Hafsi suna nasu shirin duk da sun san Senator Rufai da iyalinsa ba tsaransu bane amma dai suna gudun gori ace sikau suka kai yarsu.
Ranar karbar lefe tazo dai dai da sati daya kafin biki Hafsi bata sake ganin Junaid ba shima bai neme ta ba don yasan ta kusa shiga hannunsa wannan yatsine yatsinen da take masa dole ta ajiye a gefe.



Post a Comment (0)