NA SO KUN SANI

💡 *NA SO KUN SANI* 💡 

_✍ *Abu Khadijat Assalafeey*_
29/10/2018

💡 *Na So Kun San cewa:* Zaman Lafiya ana samun sa ne ta hanyar *Ambaton ALLAH.*

💡 *Na so kun san cewa:* Shiga wahalar Rayuwa da kunci bashi ne yake nuna cewa ALLAH baya kaunar mu ba ko kuma baya amsa addu'ar mu ba. A'a amma sai dai akwai Jarabawa da ALLAH yake ma bayinsa da suke kawar da Zunubai idan bawa ya ci nasarar cin jarabawar kuma Jarabawar itace take karawa bawa kusanci zuwa gare shi (SWA).

💡 *Na so kun san cewa:* Gwargwadon Amincewa da yadda cewa jarabawar daga ALLAH ta ke, to gwargqadon yadda Soyayyar ❤ ALLAH ta ke kuma karuwa a gare mu.

💡 *Na so Kun sani cewa:* Waka 🎶 cutar da Zuciya ta ke! Lalata ta ta ke yi, da kuma yadda hatsarinta ya ke a acikin Ruhi.

💡 *Na so kun san cewa:* Yawan Rantsuwa ba ta samarwa da mutum nutsuwa, sai dai Zunubi da ta ke sa ya dauka.

💡 *Na so kun san cewa:* Mallakar Sabuwar mota 🚘, ko gina katon gida 🏘 ba shi ne ya ke nuna cewa ka yi Nasara a rayuwa ba.

💡 *Na so kun san cewa:* Mutumin da bashi da Kishi akan 'yan uwansa Mata, 🧕 kuma yake kyalesu suke fita cikin Shiga ta tsiraici da Fitsara, suna nuna kyawunsu *to ba zai taba Shiga ALJANNAH ba!*

💡 *Na so kun san cewa:* *_KUDI 💰 BA ZA SU TABA SIYA MA MUTUM ALJANNAH BA!_*

         *💡NA SO KUN SANI 💡*

_*💡 wannan Tunatarwa 📝 ce xuwa gare mu baki daya, ALLAH ya tsare mu zuwa kan tafarkin Dai Dai, ya sa mu zama.cikin bayinsa nagartattu.*_

+2348060027244
Post a Comment (0)