MAGANIN YAWAN AMAI GA MASU JUNA BIYU

*MAGANIN YAWAN AMAI GA MASU JUNA BIYU*

TAMBAYA TA 2572

*******************

Assalamu alaikum malam mai zauren fiqhu da

fatan katashi lafiya da iyalan gidanka ameen.

Malam ina tambaya akan mace mai sabon ciki

menene ya kamata abata don rage wahalar ciki da

laulayi, kamar amayi, tofar nyawu da sauransu.

Nagode Allah yakara dokaka darajarka da gidanka

ya kuma jikan iyaye was salam.

AMSA

*******

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa

barakatuhu.

Ka samu danyar citta (raw ginger) ka matseta ka

samu ruwanta kamar cokali guda. Sai ka hada da

ruwan dafaffiyar Habbatus Sauda, shima cokali

guda. Ka sanya cokali guda na zuma ko Ma'u Khal

(sai abinda ta za'ba).

Ka bata tasha safe da yamma, cokali daya ko

biyu. In shaAllah zata dena yawaita aman, kuma

zata samu karfin jiki koda bata cin abinci sosai ba

zata rame ba. Saboda ita zumar tana bama gangar

jiki dukkan sinadaran da take bukata.

Bayan haka asamu ganyen Na'a-Na'a adafa

ataceshi sannan a zuba garin Kirfi tare da lemon

tsami (idan bata da Ulcer) sannan azuba zuma a

bata ta rika sha safe da rana da yamma.

Allah yasa adace ameen.

WALLAHU A'ALAM.


Post a Comment (0)