Bottom of Form
Hrit
Takaitaccen sharhin fil din raid
Raid 2018 film
Raid indiyan crime da action
Wanda ya rubuta Ritesh Shah
Directed by Raj Kumar Gupta
Waxanda suka fito a ciki
Ajay Devgan
Ileana D'Cruz
Saurabh Shukla
Wannan labarin ya faru ne a 1980s akan kudin haraji da yake shigowa, wanda ya jagoranta shine officer of the Income Tax Department qarkashin shugabancin Indian Revenue Service.
.
Film xin ya fara ne da IRS officer Amay Patnaik (Ajay Devgn) a matsayin Deputy Commissioner of Income Tax, wanda yake rayuwa tare da matarsa cikin farin ciki, matar tasa it ace Malini (IIeane D’Cruz), wata rana officer Amay Patnaik ya samu labarin wasu haramttatun dukiya wanda wani daga cikin manyan gari ya voye, wato Rameshwar Singh(Saurabh Shukla), mai kuxi ma Sitagarh. Ya kasance baya bada kuxin haraji tsawan wani lokaci.
Amay da team xinsa sun shirya sun je Sitagarh, sun sami karva mai kyau a gurin iyalan Rameshwar Singh, Amay da yaran sa suka fara bincike ko ina na cikin gidan lungu da sako na ko ina na cikin gidan domin su gano inda haramttatun kuxaden da aka voye. Bayan wasu lokuta da suka xauka suna bincike basu sami komai ba, sai Amay ya sami wasika da bayanin da inda aka boye kuxin a cikin gidan tare da map xin gidan da inda aka voye.
Amay da yaransa suka fasa celin da bango da storerooms, tare da taimakon map xin, da suka samu, anan ne suka samu tarin dukiya mai yawa tare da zinarai a tare a voye.
MP Rameshwar, bai yadda da wannan al’amari da ya faru da shi ba don haka ya umarci Amay da ya bar masa gida, MP Rameshwar ya je ya gana da Chief Minister of Uttar Pradesh, amma Chief Minister ya ki yadda da abin da ya faru, IT depertment tana aiki ne qarkashin Central government's control and the raid is legal, central finance minister ya kirawo Amay da ya bar wannana aiki.
Rameshwar ya runga zuwa waje ministoci yana ganawa dasu akan wannan al’amari, da wasu manya manyan ‘yan siyasa da duk wani mai faxa aji a qasar daga qarshe har ya je wajen Prime Minister, Indira Gandhi.
Ya samu damar ganawa ne da Prime Minister, Indira GandhI ta hanyar nuna mata muhimmanci sa akan siyasa ta hanyar cabinet xinta. Daga karshe ta yadda ta gana da shi, bayan kwana uku da yin bincike ne da daddare, PM da Rameshwar suka haxu, PM Indira GandhI ta kirawo Amay omin ya duba yayi aiki da halattaciyar hanya, Amay ya amince ya yadda kuma yana jira gobnati ta sa hannu akai.
PM ta tsaida binciken da kuma cajin da akewa Rameshwar, media da sauran yan gari suka sa gobnati a gaba, haka gobnati ta hakura ta kori Rameshwar.
Rameshwar ta takura ta mai yawa don haka ya tura a kaiwa Malini wato matar Amay hari, daga bisa ni ta samu ta yi escape.
Daga nan ne mutanen garin suka kaiwa Amay da yaransa hari, har ta kai sun kusa su kore su daga garin.
PM ta turo special police forces domin su ceci Amay, Rameshwar Ankamashi bisa yadda doka ta tanada.
Amay ya gane wacce ta taimakamasa ya samu information, ba wata bace illa surukar Rameshwar, ita kuma tayi haka ne domin xaukar fansa da tayi saboda tilas ta mata da akayi aka rabata da masoyinta aka haxata da wanda bata so wato xan Rameshwar.
Rameshwar ya gane wadda ta tona masa asiri, shi kuma Amay da matarsa Akamai transfer ya koma wani gari yaje yana rayuwarsacikin farin ciki.
KARSHE
Naku Yakubu Yabkhan