««« TARWATSA MAZA-2 »»»
Littafe na Biyu.
Na abdul Aziz sani madakin Gini
Type Suleiman zidane kd
Whatsapp 09064179602...
................................................................
Wa dansu sandunan karafa da ke zube a
kasa gudu uku a cikin kejin. Da ganin
wadannan karafa a salinsu makamai ne na
irin fursunonin dodo gurmazu. Nan take na
dau biyu daga cikin karafan na dunga
bugasu a kan guda, wato na maishesu
gangar kida. Bisa mamaki sai naji dajin gaba
daya ya kaure da kidan nawa har karfin
kidan ya danne munsharin dodo gurmazu
cikin tsananin fushi sauran aljanun nan su
dubu biyu suka yunkura suka taso mini
kamar zasu cinyeni danye ni kuwa sai nayi
wuf na zare takobina nace, "Na rantse da
karfin sihirina duk wanda ya iso kaina sai
dai uwarsa ta haifi wani. "
Da farko sun yi tsammanin cewa kuri nake
bazan iya hallaka daya daga ciknsu ba, don
haka sai biyu suka afko mini ai kuwa sai
nasa takobina na saresu. Take jikinsu ya
zagwanye suka zama kwarangwal. Koda
ganin abin da yafaru sai sauran gaba daya
suka ja da baya a tsorace suka yi cirko-cirko
kamar bera ya ga kyanwa suka kama
karkarwa. Duk wannan abu dake faruwa
aljani barzila na zaune a gefe daya yana
din lonmu kawai bai ce uffanba ya zuba ido
kawai yaga iyakar gudun ruwana. Daya daga
cikin aljanun ya dube ni cikin alamun tsoro
da damuwa kamar zai fashe da kuka yace,
"Ya kai wannan hatsabibin bil'adama kayi
sani cewa wannan kidan daka kama yi ba
karamin tashin hankali bane a garemu gaba
daya domin zai iya sawa ka farkar da dodo
gurmazu daga barci. Idan kuwa ya farka a
fusace zai fito ya bude kejin nan ya cinye
wasu daga cikinmu a wannan dare ba tare
da ya bari ya wayeba. "
Koda naji wannan batu sai na bushe da
dariya nace, "Amma dai kun cika gaulaye,
shashashu. In ban da abinku menene
banbancin mutuwar dare da ta safiya? Ai ni
yanzu nafi soma dodo gurmazu ya cinyeni da
wuri, domin na huta da fargaba. Don haka
ba zan fasa yin wannan kida ba, burina shi
ne ya tashi yaji na hanashi barcin domin ya
kawar dani da wuri. "
Koda gama fadin hakan, sai naci gaba da
buga wadannan karafuna. Ai kuwa sai dajin
ya sake kaurewa da karar karafan tamkar
ana aiki a makera
Dodo gumurzu na cikin barcinsa sai yaji
kunnensa ya dameshi, a sakamakon kidan da
nake yi bai san sa'adda ya mike zaune
zumbur a fusace. Koda ya gane cewa daga
cikin kejin fursunoninsa wannan kida ke tashi
sai ya harzuka ya mike tsaye zumbur ya fito
daga cikin bukkarsa a matukar fusace ruke
da fitilar ice ya nufo inda kejin yake, ni kuwa
na cigaba da kidana ban fasa ba, harya iso
gaban kejin ya sunkuyo da kansa yayi arba
da ni ina ta faman kida tamkar a cikin
gidana nake al'amarin daya matukar ba shi
mamaki kenan musamman daya ga nayi ido
biyu dashi, amma ban fasa yin kidan ba.
Nan take gurmazu ya daka mini tsawa wacce
tasa na firgita ainun na ji kamar hantar
cikina zata fado kasa daga cikin bakina. Su
kuwa su aljani barzila sai duk suka koma
gefe daya suka cakude suka mammanne da
juna suna kyarma. Ni kam a zuci ne na
firgita amma a zahiri babu alamar tsoron
komai a tare da ni face murmushi a fuskata,
sai dai na tsaya cak ga barin kidan na
kurawa gurmazu idanu. Gurmazu ya dubeni
da kyau sama da kasa, sannan yace,

sani cewa fiye da shekaru hamsin baya ban
taba kama fursunan daya tasheni daga barci
ba sai kai lallai ka tsokanowa kanka masifa
da bala'I mara misaltuwa idan gari ya waye
sai nayi maka mummunan kisan da ban taba
yiwa wani ba".
Sa'adda dodo gurmazu yazo nan a zancensa
sai na kyalkyale da dariya al'amarin da ya
matukar bashi mamaki kenan, kuma ya
baiwa sauran aljanun mamaki. Lokaci guda
kuma na murtuke fuska nace da shi, "Ai idan
ka bari sai da safe zaka dau mataki a kaina
baka burge niba yanzu a daren nan nake son
ka hallakani idan za ka iya ka sani cewa ko
kadan bana shakkar ka kuma ina tabbatar
maka da cewa lokacin daka kama ni
shammata ta kayi, In ba don hakaba tuni na
hallaka ka".
Koda jin wannan batu sai dodo gurmazu ya
cika da tsananin mamaki ya kura mini idanu
sosai ya kasa cewa komai. Daga can sai ya
bushe da dariya tamkar ana ruwan
kwarankwatsa daga sama ya dubeni yace,
"Tabbas barewa bata yin gudu danta yayi
rarrafe. Ya kai wannan bil'adama ka yi sani
cewa, kai tsatson wani hatsabibin bil'adama
ne da na taba kashewa a wasu shekaru da
dama da suka wuce, domin na ga kuna kama
matuka kai da shi, tamkar an tsaga kara.
Bari na nuna ma wani abu."
Gama fadin hakan ke da wuya sai dodo
gurmazu ya juya ya koma cikin bukkarsa jim
kadan sai gashi ya fito ruke da sandar nan
ta mulki ta masarautata.
Ita dai wannan sanda anyi tane da zallar
farin karfe na lu'u'lu'u. Nan da nan hasken
sandar ya gauraye dajin gaba daya tamkar
safiya ce ta yi badare ba. Sandar ita kadai
kyalkyali take da sauya launi, kai dagani
kasan sandar sihirice. Daga saman sandar
kotace, kasanta kuwa tsinine, tamkar mashi.
Dodo gurmazu ya karaso daf da kejin da
muke ciki ya tsuguna yana mai nuna mini
sandar yace, "ka san wannan?"
Koda jin wannan tambaya sai na kyada kai
cikin alamun takaici da bakin ciki a lokacin
da idanuna suka ciko da kwalla nace,
"Kwarai kuwa na san wannan sanda mallakin
mahaifina ce, kuma kai ne ka kashe shi kara
bashi da wannan sanda ka sani cewa nazo
wannan daji ne domin na dauki fansar ran
mahaifina kuma na karbi wannan sanda a
hannunka na mai da ita masarautarmu. "
Koda jin haka sai dodo gurmazu ya
takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya
wadda ta haddasa karamar girgizar kasa a
dajin gaba daya har sai da ya tsuke bakinsa
sannan dajin ya tsaya cak. Gurmazu ya dube
ni yace, "Hakika kayi wauta har da kake
tunanin daukar fansa a kanmu domin nine
karo da dubu ko dubu ta taru sai hakuri
hakika ka fusatani irin fusatar da ban taba yi
ba a rayuwata amma sai gari ya waye
sannan zan nuna maka irin fushina ba ma
kai ba hatta wadannan fursunoni 'yan
uwanka ka shafa musu kashin kaji. "
Gama fadin hakan keda wuya sai gurmazu
ya lura da gawar aljanun nan biyu da na
kashe a cikin kejin cikin tsananin fushi ya
dubemu gaba daya yace wane ne ya bata
mini abincina haka daga cikin ku?"
Kawai saina yi farat nace nine kuma ina
tabbatar maka da cewa yadda na bata maka
wannan abinci haka kai ma zan zare maka
rushin numfashinka. Idan har ka isa kai
jarumine ka fito dani yanzu daga cikin kejin
nan mu yi yaki gaba da gaba. "
Sa'adda dodo gurmazu yaji wannan batu
daga bakinsa. Sai idanunsa suka matso
kwallar takaici. Domin tun da ya wanzu a
duniya ba a taba yi masa irin wannan rashin
kunya ba. Cikin tsananin fushi ya dube ni
bakinsa na karkarwa yace, "Kaicon ka yaro
hakika kayi babbar sa'a domin dokar tsafina
ta hana ni yin komai da daddare. Amma ka
kiyayi wayewar gari, domin sai na maisheka
misali a kan dukkan sauran bil'adama masu
girman kai a duniya. "
Koda gama fadin haka sai dodo gurmazu ya
juya ya nufi bukkarsa ruke da wannan
sandar mulkin ta mahaifina. Koda na ga
haka sai na cigaba da kidana har gurmazu
ya shiga cikin bukkarsa ban fasa ba. Kai a
takaice dai sai da na kwana ina wannan
kida, ban runtsaba su kansu su aljani barzila
na addabesu. Dalilin da yasa nayi haka
kuwa, shine ko ba komai na san cewa na
hana dodo gurmazu barci a wannan dare don
haka ya kwana da mugun bakin ciki bazan
mutu a banza ba, naci ribar hanashi barci.
Kashe gari kuwa, da sassafe dodo gurmazu
ya zo ya fito daga cikin bukkarsa. Ina
kallonsa na ga idanunsa sun yi jajur kai da
gani kasan cewa bai samu barci ba, kawai
sai na bushe da dariyar mugunta dodo
gurmazu ya nufo kejin da muke ciki a fusace
yayin dasu aljani barzila suka tsinke da
gudawa gaba dayansu, saboda tsananin
razana, nikuwA sai na mike tsaye na rike
kuguna da hannu biyu cikin takama da jinkai
"al'amarin da ya bawa dodo gurmazu
mamaki kenan, yace aransa to waishi
wannan yaro menene madogararsa ? Ni
kuwa zan bashi dama mu fafata yaki domin
naga iyakar abin da yake dogaro da shi.
Yayin da dodo gurmazu ya iso daf da kejin
yaga har a sannan ban ji tsoron komai ba
ina tsaye cak ina kallonsa kawai sai yasa
hannunsa guda ya bude kejin a lokacin da
daya hannun nasa. Ke ruke. Da katon
sunguminsa na yaki ya ce dani.
"Kai yaro fito naga iya takamarka, ga shi
dare ya shude gari ya waye. "
Ba tare da fargabar komai ba na fito daga
cikin kejin na tsaya a gaban gurmazu tamkar
kare ya tsaya a gaban giwa saboda
banbancin girma jikinmu. Gurmazu ya dubeni
sama da kasa sai ya kyalkyale da dariya,
sannan ya turbune fuska ya ce, "Na baka
dama idan bazaka iya yakata baka falfala da
gudu a cikin wannan daji har izuwa tsawon
sa'a guda sannan zan biyo ka na kama ka
nayi. Maka irin kisan da nakeso. Idan kuma
kana ganin cewa zaka iya yaka ta to mu fara
wanne ka zaba?"
Koda jin wannan zabi sai na yi shiru ina
tunani domin na san cewa wannan fa ita ce
dama tata karshe. Abu na farko ni kam na
tabbatar da cewa karfin damtsena dana
sihirina baza su taba kubutar dani ba a
wajen dodo gurmazu domin ya ninka ni sau
dari a wannan bangare. Yanzu menene
mafita? Kwazam sai wata dabara ta fado
mini wacce bani da tabbacin zata yi tasiri,
amma da na tuna cewa sai an gwada akan
san na kwarai sai. Kawai na duba dodo
gurmazu nace, "Na zabi ka bani damar na
falfala da gudu in yaso ka kure mini gudun
ka kasheni. "
Koda jin haka sai dodo gurmazu ya bushe da
dariyar mugunta yayi ta kyalkyalawa kamar
bazai daina ba, har sai da hawaye ya zubo
masa, sannan ya turbune fuska ya maida
kofar kejin ya rufe su aljani barzila suka
dada firgicewa suka cigaba da tsula gudawa.
Gurmazu ya dubeni yace, "Haba yaro yaya
zaka yi saurin sallamawa haka. Lallai baka
gaji ubanka ba, domin shi ya jarraba yin yaki
dani har yasamu nasarar shafe dakika dari
uku muna fafatawa. Tabbas na jinjina masa
sHi na mijine amma hargobe idan na tuna
irin kisan dana yi masa yana bani tausayi. "
Koda jin wannan batu sai na ji zuciyata ta
harzuko cikin fushi na tambayi gurmazu
nace, "Wanne irin kisa kayi masa?
Gurmazu yace, "da na soka masa farcen dan
yatsana a cikin bakinsa sai da ya fito ta
cikin duburarsa a haka ya sankame jikin
hannuna ya zama gawa, kuma a hhakan na
gasa shi a wuta na rinka gutsurarsa da
kadan-kadan ina ci har sai da ya kare tas. "
Koda jin wannan batu sai na kwarma uban
ihu, kuma na fashe da kukan bakin ciki.
Dajin kukana sai dodo gurmazu ya cigaba da
kyalkyala dariya, sannan ya zauna dirshan
kasa ya runtse idanunsa yace, "Na baka
dama yaro ka ruga da gudu kayi ta gudun
har tsawon sa'a guda, lallai zaka riskeni a
gabanka. "
Koda jin haka kuwa sai na falfala da gudu
maimakon na nausa cikin daji saina nufi
cikin bukkar dodo gurmazu, shikuwa
gurmazu bai lura da hakan ba, domin
idanunsa a rufe suke yana ta kirga dakikoki,
jira yake kawai sa'a guda tacika.
Kuyi hakuri bisa tsallaken da kuka gani
wannan ya farune sakamakon matsalar fage Lokacin dana shiga cikin bukkar dodo
gurmazu sai nayi arba da kwarangwal na
kawunan bil'adama dana aljanu birjik
barkatai ba adadi, kuma a jere layi-layi koda
na dubi wadannan kawuna sau na fahimci
cewa a dadinsu shine adadin mutanen da
aljanun da ya cinye a zamansa cikin wannan
daji na shjaril maurud nan fa naci gaba da
bincike a cikin bukkar ina neman wannan
sandar sarauta ta ubana, amma ko alamarta
ban gani ba. Al'amarin da ya dugunzuma
hankalina kenan.
Kwazam sai naga wadannansu hakora na
dodo gurmazu guda hudu a ajiye a gefe
daya. Ko wanne guda daya ya kasance mai
tsawo tsini da kaifin tsiya. Na dubi hakoran
da kyau nayi nazarinsa sai na gane cewa
duk abin da aka karta ko aka sara sai ya
rabe biyu ko ya huje komai karfinsa. Kawai
sai na wuce hakoran na cigaba da neman
wannan sanda. Kwazam sai naga wata
akwatun sihiri wacce aka rufe ta bam da
katon kwado mai kauri da girma, wanda inda
karti arba'in zasu taru majiya karfi bazasu
iya daga shi sama ba. Nan fa na shiga
lalube ko zan ga kubar da aka rufe kwadon
da ita, amma ko alamarta ban gani ba.
Alqkamarin daya dugun zuma hankalina
kenan domin a wannan lokaci na tabbatar da
cewa baifi saura dakika dari biyu ba dodo
gurmazu ya bude idanunsa,ya nemeni a inda
nake, nan take nayi amfani da karfin sihirina
, domin na bude wannan kwado, amma sai
abu ya faskara. Koda na juyo baya na dubi
wadannan hakora guda na dodo gurmazu sai
dabara ta fadomini. Da gudu na ruga na
dauko hakori guda na sari wannan kwado.
Take kwadon ya karye ya fadi kasa. Karar
sarar kwadon kuwa ta cika dajin gaba daya.
Al'amarin da yasa dodo gurmazu ya bude
idanunsa kenan ya kallo cikin bukkarsa.
Cikin tsananin zafin nama na daga murfin
akwatin nayi arba da wannan sandar
sarauta. Ai kuwa sai nayi wuf na dauko ta.
Kafin na juyo sai naji an yi bal dani nayi
sama na fasa sai dana yi sama sosai,
sannan na rikito kasa baje wanwar, idanuna
na gani dishi-dishi, gaba daya jikina yayi
tsami tamkar a cikin turmi aka daka ni.
Amma saboda naci ina ruke da wannan
sandar sarauta.
Kawai sai ganin dodo gurmazu nayi tsaye
akaina. Kafin nayi wani yunkuri ya kawo mini
suka da farcen hannunsa izuwa cikin bakina.
Cikin tsananin zafin nama na goce ya soki
kasa yatsan nasa ya nutse gaba daya azuwa
cikin kasa. Koda ya zare hannun nasa sai
wajen ya zamo rami mai zurfi tamkar an
haka rijiya mai tsawon kamu dubu nikaina
nayi mamakin yadda aka yi na samu
gawurtaccen zafin nama dana gocewa
wannan mugun hari nasa. Abinda bansaniba
shine, wannan sandar sihiri dake hannuna ita
ce ta taimaka mini nanfa muka cigaba da
mugun artabu ya zamana cewa dodo
gurmazu na kawo mini suka da sunguminsa
yayin da na goce ya soki kasa ko ya dake ta
sai ya haddasa rami, gami da girgizar kasa.
Nan da nan ya tashi hankalin dajin gaba
daya ya zamana cewa duk wata halitta mai
rai da ke cikinsa ta suma sau ba adadi,
domin su aljani barzila kuwa a wannan
lokaci suna kan suma na arba'in da hudu.
Sai da muka shafe sa'a hudu muna wannan
gumurzu, a sannan ne gurmazu ya fara
samun nasarar yankar jikina da kaifin
faratansa ya zamana cewa yayi mini
munanan raunika guda bakwai, sai jini ne ke
zuba a jikina har jiri ya fara diba ta, kuma a
sannan ne ya fara kokarin kwace wannan
sandar sihiri dake hannuna, amma saboda
naci sai naki yarda ya kwace sandar. Muna
cikin wannan gumurzu ya shammace ni ya
kwada mini mari a fuska , saboda karfin
marin sai dana yi katantanwa sau uku a
sama sannan na fado kasa na baje ko
motsin kirki ban yi ba. Cikin tsananin murna
dodo gurmazu ya bayyana a gabana ya
sunkuyo da fuskarsa, kuma ya tallafo kaina
da hannunsa guda ya ajiye sunguminsa a
gefe daya. Kawai sai ya daga danyatsansa
guda da nufin ya soka mini farcensa ta cikin
bakina, don ya yi mini irin kisan dayayi wa
mahaifina. Bazato ba tsammani, sai
gurmazu yaji na suka masa tsinin wannan
sandar sihiri dake hannuna a cikin bakinsa
har sai da ta hudo keyarsa. Gurmazu ya
kwarara uban ihu wanda ya haddasa
kakkaryewar bishiyoyin dajin. Gurmazu ya
dunga tsalle yana tumuwa da kasa ya sake
haddasa girgizar kasa.
A lokacin ne nayi zumbur na mike tsaye na
koma gefe daya ina kallon yadda yake ta
matagungun. Sai da gumurzu ya shafe rabin
sa'a yana birgima a kasa gami da daka
tsalle sama yana fadowa sannan ya baje
akasa yayin da jini ke ta malala daga cikin
kokon kansa, amma saboda taurin rai yaki
mutuwa yana ta shure shure a hakan ya juyo
da kansa ya dubi inda nake. Sannan ya dude
baki yace,
"Ya kai magajin ubansa kayi sani cewa ba
zan taba mutuwa ba face kazo ka cire
wannan tsafin daga cikin bakina idan kuwa
ka bar ta har tsawon rabin sa'a nan gaba zan
mike tsaye. Tamkar wani abu bai same niba,
na hallaka ka. "
Koda jin wannan batu sai hankalina ya
dugunzuma na nufi inda dodo gurmazu ke
kwance da nufin na zare wannan sandar
sihiri. Da zuwana daf da shi sai na kai
hannu zan zare sandar, amma sai sai na
fasa, domin ji nayi zuciyata ta daka mini
tsawa tace dani "A kul! Kayi amfani da
zancen wannan azzalumin dodo, domin babu
mamaki idan ka zare sandar daga cikin
bakinsa ya rayu. "
Kawai sai naja da baya na dubi dodo
gurmazu nayi masa murmushin mugunta
nace "Zan jira har rabin sa'ar ta cika sannan
na ga yadda zaka iya hallaka ni. " Lokacin
da dodo gurmazu yaji wannan batu, sai
hawaye ya zubo a idanunsa yace, "Yaro
tabbas yau kaga karshena, domin ka karya
tasirin sihirina. Inda kayi kuskuren zare
wannan sanda daga cikin bakina da tuni duk
digon jinina daya zuba akasa ya zamo irina
guda tabbas kacika gwarzo abin jinjinawa a
wannan zamani. Duk bukatar da kasa a
gabanka sai ta biya kasani cewa nan da
cikar rabin sa'a zan mutu kuma irin mutuwar
da mahaifinka yayi ita zan dandana. Alfarma
daya zan roka a wajenka ina son idan na
mutu ka kone gawata, kuma koda kasusuwan
jikina sun yi saura ka binne su a cikin kasa
yadda zasu rube da sauri. "
Koda naji wannan batu sai na bushe da
dariyar farin ciki nace, "Ya kai wannan
azzalumin dodo, wanda ya shafe shekara da
shekaru yana kashe mutane da aljanu kayi
sani cewa tsakanina da kai har abada babu
alfarma, don haka a inda ka mutu din nan a
nan zanbar gawarka har ka rube. Ka zama
kwarangwal, domin mutane da aljanu su yita
ganinka ka zamo abin tunawa. "
Gama fadin haka keda wuya sai jiri ya
kwasheni na bingire kasa sumamme. Ban
farfado ba sai bayan sa'a guda. Ina bude ido
naga dodo gurmazu ya zama gawa, bakinsa
a wangame har tsuntsaye sun fara
tsatstsagar jikinsa. Ni kaina tsuntsayen sun
fara kawo mini hari, domin suna zaton na
mutu sai da suka ga na yunkura sannan
suka tashi fir. Da jan ciki na isa inda gawar
dodo gurmazu take na zare wannan sandar
sihiri daga cikin bakinsa sannan na sake jan
ciki na isa kejin dasu aljani barzila suke ciki.
Da kyar da sidin goshi na mike tsaye na
sare kofar kejin da sndar ta bude. Cikin
tsananin farin ciki su aljani barzila suka fito
daga cikin kejin suka kama tsalle da murna
tsira da rayuwarsu. A sannan ne na sake
faduwa kasa sumamme.
Sai da su aljani barzila sukayi jinyata tsawon
kwana bakwai a cikin dajin shajaril murud
sannan na sami lafiya na dawo cikin
hayyacina. A ranar da nasami lafiya ne
wadannan aljanu guda dubu biyu fursunonin
dodo gurmazu suka yi alkawarin cewa daga
yau sun zama bayina kuma duk ranar da
nake bukatar su suyi mini wani aiki na
nemesu. Bayan aljanun sun tafi sai na
bukaci aljani barzila. Daya shiga cikin bukkar
dodo gurmazu zai ga wannan giwa da yake
kiwo a ciki ya kashe giwar ya yanko
harshenta ya kawo mini. Nan take kuwa
aljani barzila yaje ya cika wannan umarni a
cikin abin da bai wuce dakika dari da
ashirinba. Ba tare da bata lokaci ba aljani
barzila ya goya ni a bayansa ya bude fuka-
fukansa ya tashi sama muka nufi birnin
sharas.
Tun kafin mu isa gida boka surub ya ga duk
irin nasarar dana samu a cikin madubin
tsafinsa don haka shine mutum na farko
daya tare mu a cikin fada ta. Muna sauka a
kasa ya rugo izuwa gare ni ya rungumeni
yana mai yi mini barka bisa samun nasara.
Ba tare da bata lokaciba, boka surub ya
karbi wadannan abubuwa uku dana samo ya
zuba su a cikin tukunyar tsafi yayi ta dafa su
har tsawon kwana tara. A daren kwana na
tarane nayi tsirara na shafe jikina kaf da
dafaffen maganin, sannan ya umarceni da
tafiya makabarta. Nan take kuwa na tafi
makabartar a cikin wannan tsohon dare na
nemi kabari wanda ya shekara tamanin bai
bajeba, kuma ba a taba haka shiba. Kawai
sai na zauna a gaban kabarin na soka
hannayena ba.
Tsawon kwana ukun babu mahalukin da ya
rabi kusa da makabartar walau mutum ko
aljan saboda karfin mulkina da karfin
sihirina bayan na kammala wannan aiki ne
na ji wani irin gagarumin karfi ya shiga
jikina, irin wanda ban taba jin karfi ya shiga
jikina, irin wanda bantaba jin kamarsaba a
rayuwata domin na gwada karfin nawa ne na
kirkiri yakuna bakwai da kasashenda ke
makwabtaka da kasata. Duk sai da naci
yakokin ko sau daya ba a kaini kasaba kuma
ba a yi mini rauni daya ba, Bayan an gama
yakokin ne na shirya walimar farin ciki ta
musamman, saboda murnar abu uku. A bu
na farko shine, na zama gawur taccen
jarumin da babu kamarsa a duniya. Abu na
biyu na sami nasarar dawo da sandar
masarautar kasata, wacce dodo gurmazu ya
kwace a wajen mahaifina, wanda a dalilin
dawowar sandar arzikin kasata ya bunkasa
ainun, a bu na uku shine, na dawo na iske
'yata wadda matata ta mutu ta bari a
wannan shine a salin samun jarumtaka ta ta
ban al'ajabi, sirrin da babu wanda ya sanda
shi face boka surub sai kuma ke da na baki
labari a yanzu, sa'adda sarki hasanul
mauzur yazo nan a labarinsa sai gimbiya
shulaira ta cika da tsananin mamaki kuma ta
rungume shi tana mai fashe da kuka tace,
"ya kai abbana hakika kasha bakar wahala a
rayuwarka kuma ka ruke alkawarin ga
mahaifiyata, har abada ba zan taba
mancewa da irin wannan gwagwarmaya
dakayi ba"
Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube
sarki hasanul mauzur ya janye jikinsa daga
jikin shulaira suka fuskanci juna sannan ya
ce, "Ya ke 'yata kiyi sani cewa ni yanzu bani
da wani sauran buri a duniya face naga kin
auri miji wanda ya fini gwagwarmaya da
daukaka a duniya, domin na mutu da farin
ciki alkawarin dana daukarwa mahaifiyarki
cewar bazan taba bari kisha wahala ba a
rayuwarki. Bisa wannan daliline gobe zan sa
a yi shela har izuwa dukkan sauran kasashe
dake wannan nashiya tamu cewar duk wanda
yake son ki da auren naki, bisa wadannan
matakai guda uku da kika gindaya, amma
sharadai biyu na cewar ba zai yi miki
kishiya ba, kuma ba zai kara aure ba, koda
kin mutu kamar yadda nayi wa mahaifiyarki
alkawari, sai bayan an gama gasar zamu
bayyana su. "
Cikin farin ciki shulaira tace, "Na yarda da
hakan ya kai abbana. "
Koda wanda zai shiga wannan gasar Nidai
na dau damara na dau hanya waye zai take
mini baya kodai matsoratane ???
Suleiman zidane kd kenan......
Kashegari da sassafe aka fara shela a cikin birnin sharas ana gayyatar jama'a I zuwa gasar samun auren gimbiya shulaira, sannan aka tashi manzanni a shirin da bakwai suka tafi izuwa sauran kasashen dake nahiyar suna kai wasiku izuwa ga sarakuna na gayyatar su izuwa wannan kasa. Sai da aka kwana talatin ana ta watsa wannan shela, nan da nan kuwa labari ya bazu ko'ina a nashiyar gaba daya har dama sauran kasahen dake wadansu na shiyoyin daban.
A cikin nashiyar da kasar sharas take a kwai wata karamar kasa mai suna DUMAR. Sarkin dake mulkin birnin ya kasance a dali mai tausayi da jinkan talakawansa kuma gwarzon jarumi ne na gaske, ana kiransa da suna mushlik.
Gaba daya fadawan mushlik azzalumaine, kuma basa son halayen mushlik, babu yadda basuyiba akan su tumbuke shi daga kan mulki ta hanyar amfani da karfin sihiri da makirci, amma abu ya gagara, saboda yafisu karfin sihiri. Komai na duniya allah ya baiwa sarki mushlik, ga arziki kuma ga iyali, amma 'ya'yansa goma sha bakwai ne dukkaninsu matane, namiji guda daya ne ana kiransa da suna yarima zamir.
Shekarun yarima zamir basu haura ashirin da biyar ba, kuma ya kasance kyakykyawan saurayi kuma ya gaji mahaifinsa a bangaren kyawawan halayeensa sai dai ko kadan bai kasance jarumi ba tunda yarima zamir yazo duniya ko kiyashi bai taba kashewaba saboda tsananin tausayinsa kuma bai taba ruke takobiba a rayuwarsa a kullum yarima zamir babu abinda yake so sama da zama a cikin yara yana wasa da su suna debe masa kewa ko kadan yarima zamir bai damu da jin dadin duniyaba kuma bai taba ganin wata budurwa ba ya nuna yana sonta komai tsananin kyanta. Dare da rana yarima zamir na tare da kannansa yara maza da mata yana wasa da su.
Wannan halaiya ta yarima zamir ba karamin bakin ciki ta jefa sarki mushlik a ciki ba, domin babu yadda baiyi a kan ya sauya yanayin rayuwarsa amma ya kasa. Burin sarki mushlik shi ne yarima zamir ya gajeshi a karagarsa, kuma yayi gagarumin abin bajinta, wanda zai shahara a duniya gaba daya. Dalilin da yasa yake da wannan buri shine yasan cewa duk ranar daya fadi ya mutu, shi kenan mulkinsa da dukiyarsa sun zama na daya daga cikin fadawansa, kuma a dalcin da ake yi wa talakawa an daina. Haka kuma a gaba daya nahiyar ana zunden yarima zamir ana cewa ba a taba yin malalacin yarima ba kamarsa har dariya ake yi masa ana goranta masa ana cewa sarki mushlik yayi a sarar haihuwa. Duk sa'adda sarki mushlik ya tuno da wannan al'amarin sai ya shiga cikin turakarsa ya kulle kansa yayi ta kuka saboda bakin ciki.
A ranar da wasikar gayyata ta gasar neman auren gimbiya shulaira ta riski sarki mushlik saihankalinsa ya dugunzuma ainun kuma ya kamu da tsananin bakin ciki fiye da koyaushe, domin ga bikin zuwa babu zanin daurawa. Abin da yafara fado masa a rai shine yarima zamir ya shiga wannan gasa, domin yayi gagarumar bajintar da ba a taba yin irintaba kuma ya auri gimbiya shulaira wato dai ya jefi tsuntsu biyu da hoge daya. Sarki mushlik ya tuna cewa ko kadan yarima zamir bai iya aikin sihiri ba. Babbar matsalar itace a dokar gasar ba a yarda sarakuna su shiga ba sai dai 'ya'yansu.
Bayan sarki mushlik ya gama jin sakon da ke cikin wasikar gasar. Sai ya kasa zaune ko tsaye ya shiga kai-kawo yana ta tunani bisa yadda zai amfani da wannan dama a kan dansa yarima zamir, amma sai ya ga sam-sam babu mafita. Bisa wannan da muwace sarki mushlik yayi shiri ya fita rangadi izuwa bayan gari shi kadai, domin ya sami kadaici kuma ya sami saukin tunani da damuwa. Lokacin da sarki mushlik yayi nisa ga barin gari sai ya yada zango a bakin wata korama ya sha ruwa, dokinsa ma ya sha ya zauna yana kallon ruwan koramar, wanda cibiyace ta wani babban kogi sai ruwa ne ke ta gudu ba tsayawa.
Kwazam sai sarki mushlik ya ghango wani allon jirgin ruwa daga can nesa igiyar ruwa na kado shi gaba. Tun daga nesa mushlik ya fashimci cewa akwai mutum a kan allon jirgin a kwance tamkar gawa, domin ko motsi baya yi. Cikin hanzari sarki mushlik ya mike tsaye ya shiga cikin koramar ya tari allon jirgin, don kada ruwa ya tafi dashi. Koda allon yazo zai gifta sai yayi wuf ya ruko shi ya janyoshi izuwa bakin gaba da yake mutumin a kwance yake cikin ruf da ciki, sai ya kama kafadunsa ya dago shi sama sai yaga a she saurayine kyakykyawan gaske. Ga kibiya ta soke shi a cikin gefen kirjinsa kuma bai mutu ba yana numfashi kadan-kadan. Cikin sauri sarki mushlik ya dauki saurayin yaje ya dora shi a kan dokinsa, sannan shima ya hau kan dokin ya zabure shi da gudu izuwa cikin gari.
Sarki mushlik na isa gida ya tura aka kira likitansa ya kama aikinsa a kan bakon saurayin, wanda rayuwarsa na tsakanin rai da mutuwa. A wannan lokaci hankalin sarki mushlik ya dugunzuma ainun, tamkar yarima zamir ne a cikin wannan hali. Sai da likitan ya shafe sama da sa'a guda yana aikin a kan bakon saurayin, sannan ya fito daga cikin dakin da aka kwantar da bakon koda fitowar likitan sai sarki mushlik ya tare shi cikin matsananciyar damuwa yace, "me a ke ciki? Shin wannan matashi zai rayu ko mutuwa zai yi?
Likitan yayi ajiyar zuciya, sannan yace, "Ya shugabana bakon ka zai rayu amma ba zai iya yin komai ba sai nan da kamar kwana bakwai. Lallai a kula da shi sosai a dunga dura masa abinci ko da ba zai iya ci da kansa ba, kuma akwai magunguna da zan bayar a dunga bashi yana sha kullum sau uku. Idan aka yi fashin ba shi wannan magani ko da na rana daya ne zai iya rasa rayuwarsa, saboda tuni dafin kibiyar ya shiga jikinsa, dole ne ya sha iya a dadin maganin da jinin jikinsa ke bukata, wanda zai lalata dafin. "
Koda gama fadin haka sai likita yayi sallama ya tafi a kan cewa yana zuwa gida zai turo 'yarsa ta kawo maganin da za a dinga bawa mara lafiyar.
Tafiyar likita ke da wuya sai sarki mushlik ya tura aka kirawo 'yarsa mai suna lasmin.
Lasmin budurwa ce kyakykyawa ta kwatance kuma kanwar yarima zamir ce wato daki daya suke kuma ita ce bin yarima zamir. A shekara biyu ce tazarar dake tsakaninsu ma'na gimbiya lasmin tana da shekaru a shirin da uku ne.
Sarki mushlik yana matukar kaunar gimbiya lasmin kamar yadda yake kaunar yazima zamir, banbancin kawai shine ita mace ce bata da ikon gadon karagar mulki. Sarki mushlik ya yarda da gimbiya lasmin ainun domin koda wani aikin na sirri yake son a yi masa ita yake sawa tayi.
Lokacin da gimbiya lasmin taji kiran mahaifin ta sai ta tashi da sauri ta ruga izuwa gareshi inda ta iske shi tsaye a kofar dakin da aka kwantar da mara lafiya. Da zuwanta sai sarki mushlik ya kama hannunta ya ja ta izuwa cikin dakin inda suka iske mara lafiyan kwance bisa gado, kamar gawa, amma yana numfashi kuma idadunsa a rufe suke da zuwansu bakin gadon lasmin tayi arba da fuskar mara lafiyan sai taji nan take ta kamu da kaunarsa, al'amarin daya matukar bata mamaki kenan, domin a rayuwar gimbiya lasmin bata taba yin soyayyaba, kuma ba ta taba ganin saurayin da taji tana soba face wannan mara lafiyar dake kwance. 'Ya'yan sarakai da attajirai da yawa sun nemi auren gimbiya lasmin, amma taki saboda ta kudurce a ranta cewa bazata taba yin aureba face ta ga cikar burin mahaifinta a kan yayanta yarima zamir, sai dai a zuciyarta ta bar wannan buri ko shi kansa sarki ba ta furta masa ba. Lokacin da sarki mushlik yaga gimbiya lasmin taki ta fitar da gwani daga cikin masoyanta sai hankalinsa ya dugun zuma ya kira ta suka kadaita yace, "yake 'yata kiyi sani cewa ina cikin tsananin bakin ciki da damuwa a kan yadda dan'uwanki yarima zamir ya kasance. Kece kadai nake da sauran Buri a kanki, wanda zai share mini hawaye. Hanyar daza ki share mini hawayen shine kiyi aure za ki haifi dan da zai gaji karagata bokayena sun tabbatar mini da cewa yarima zamir ba zai taba gado naba amma ke idan kika yi aure zaki haifi dan da zai gajeni saboda me baza ki gaggauta yin aure ba, domin naga jikana tun gabannin ajalina?
Sa'adda sarki mushliik yazo nan a zancensa, sai hawaye ya zubowa gImbiya lasmin ta rungume shi tace, "Ya kai abbana ka tsaya kayi tunani. A halin yanzu shekarunka sun kai saba'in da doriya tsufa ya fara riskarka, yanzu yaushe zan yi aure har na haifi dan da zai girma har ya zama sarki? Tabbas kafin zuwan wannan lokaci a jali ya riske ka. Burinka shine kaga magajinka a kan karagar mulkinka, idan baka mantaba ka taba gayamin cewa idan har yarima zamir yayi gagarumin a bin al'ajabi a duniya zai iya gadon karagarka. Mai zai hana ka cigaba da kokarin ganin faruwar hakan tunda tsafi ya tabbatar da cewa babu wani abu da zai gagara afkuwa a cikin wannan duniya. "
Sa'adda gimbiya lasmin tazo nan a zancenta sai jikin sarki mushlik yayi sanyi, ya yi shiru bai ce komai ba daga wannan rana bai kara yi mata maganar aure ba.
Suleiman zidane kd. Ke magana...
Bayan sarki mushlik ya nunawa gumbiya
lasmin bakonsa mara lafiya dake kwance, sai
ya dube ta ya ce, "Yake amintacciyar 'yata
daga yau ina son ki cigaba da kula da
wannan bakon mara lafiya, har izuwa lokacin
da zai samu lafiya muji labarinsa, domin a
can bayan gari na tsinto shi a cikin korama
bisa allon jirgi an harbe shi da kibiya in ba
dan yana da nisan kwana ba da tuni ya
hallaka. "
Koda jin wannan batu sai gimbiya lasmin ta
cika da tsananin mamaki, sannan ta dubi
sarki mushlik tace, "Lallai zan kasance mai
biyayya ga wannan umarni haka. "
Sarki mushlik yayi murmushi, gami da dafa
kafadar lasmin yace, "Na san da haka, domin
baki taba bani kunya ba. "
Koda gama fadin hakan sai sarki mushlik ya
juya ya fice daga cikin dakin, fitarsa ke da
wuya sai lasmin ta zauna akan gefen gadon
ta kurawa. Mara lafiyar idanu a lokacin data
ji ta kamu da tsananin tausayinsa.
Fitar sarki mushlik ke da wuya, sai ya wuce
izuwa lambunsa, domin ya zauna a ciki ya
huta. Tun daga nesa ya hango yarima zamir
a cikin lambun tare da kannansa suna wasan
'yar buya. Yarima zamir yarufe idanunsa da
tsumma yana ta laluben yaran har suna
dungurinsa yana faduwa kasa suna ta
yimasa dariya. Koda ganin wannan al'amari
sai takaici ya kama sarki mushlik har kwalla
ta zubo masa. Kawai sai ya fasa karasawa
cikin lambun ya juya da baya ya nufi
fadarsa.
Da isar sarki fadarsa sai ya iske gaba dayan
fadawansa a zaune basu watse ba, alhalin
tuntuni lokacin tashi daga fadanci yayi.
Al'amarin da yayi matukar bashi mamaki
kenan, ya dube su yace, "ina dalilin zamanku
a fada har yanzu?"
Koda jin wannan tambaya sai waziri ya mike
tsaye yace, "Ya shugabana mun tsaya ne
domin muji hukuncin daka yanke bisa
wasikar da sarki hasanul mauzur ya aiko. "
Da jin haka sai sarki mushlik yayi shiru yana
tunani tsawon 'yan dakiku. Daga can sai ya
dago kai ya dubi gaba dayan 'yan majalisar
yace aje a yi shela duk wanda yake da
bukatar shiga wannan gasa ya je yayi shiri
na kwana bakwai sai su taru a nan fada ta
sannan su dunguma gaba daya su tafi koda
gama fadin haka sai sarki mushlik ya juya
da nufin ya fita daga cikin fadar, amma sai
waziri yayi gyaran murya yace, "Ya
shugabana shin babu wanda zai wakilce ka
ne a cikin wannan gasa? Ka sani cewa duk
mutumin da y sami nasarar lashe wannan
gasa sai yayi daukakar da babu wani
mahaluki da zai yi kamar ta a wannan
zamani. Ina ganin cewa bai kamata a ce
kabar wannan dama ta wuce kaba. "
Yayin da sarki mushlik yaji wannan batu sai
ya juyo ya dubi waziri yayi murmushi, yace,
"Zan yi matukar farin ciki idan danka jarumi
haslim ya lashe wannan gasa. "
Kafin waziri ya bude baki ya kar cewa komai,
tuni sarki mushlik ya dufi kofar fita daga ya
fice gaba daya. Al'amarin da yasa jikin
waziri ya yi sanyi kenan, ya dubi sauran 'yan
majalisar suma sai suka sunkui da
kawunansu kas ba su ce uffan ba.
Jarumi haslim sadauki ne na gaske wanda
ake takama da shi a birnin dumur, sarki
mushlik ne ka dai aka tabbatar da cewa yafi
shi sadaukantaka da karfin sihiri. A duniya
babu abin da jarumi haslim ke so sama da
gimbiya lasmin, amma duk sa'adda yayi
mata maganar SO, babu abin da ke biyo
baya face bakar magana ko zagi a
tsakaninsu. Har sai da ta kai cewa sarki
mushlik ya kira jarumi haslim ya yi masa
kashedin karshe a kan cewa ko kallon
gimbiya lasmin ya kara yi yayi mat
murmushi zai fuskanci hukunci. Bisa dole
jarumi haslim ya daina bin hanyar da lasmin
kebi, kuma ko wani taro za a yi idan har zata
je wajen tofa shi baya zuwa kullum dare
darana da wannan bakin ciki yake kwana.
Shi kuwa mahaifinsa wato waziri sai ya
shiga rarrashinsa yana mai kwantar masa da
hankali, kuma ya tabbatar masa da cewa in
dai yana raye sai ya aura masa 'yar sarki
wacce tafi gimbiya lasmin kyau da matsayi.
Lokacin da waziri sharabul yaji bayanin da
sarki yayi sai ya cika da tsananin farin ciki,
saboda ganin cewa lokaci yayi da zai cikawa
dansa alkawarin da ya daukar masa. Ma'ana
zai tura jarumi haslim izuwa wannan gasa
kuma zai nema masa sa'a a wajen bokaye. A
gaba daya birnin dumur babu attajiri kamar
waziri sharbul, saboda haka a tunaninsa zai
iya siyawa dansa haslim sa'a a wajen
bokaye bisa wannan gasa da za a tafi.
Bayan fada ta watse waziri sharbul ya isa
gida sai ya kirawo dansa jarumi haslim ya
sanar da shi duk abinda ya faru tsakaninsu
da sarki a fada don haka sai ya umarci
jarumi haslim daya yi shirin tafiya ta kwana
biyu domin ziyartar manyan bokayen kasar
su hudu cikin tsananin farin ciki jarumi
haslim yaje yayi shiri cikin gaggawa bayan
ya gama kimtsawa, sai waziri sharbul ya
kawo dinare mai yawan gaske jaka hudu ya
bashi sannan ya kama hanya ya tafi izuwa
garurun hudun da manyan bokayen kasar
suke.
Al' amarin gimbiya lasmin kuwa, bayan sarki
mushlik ya fita ya bar ta a dakin mara lafiya
ta zauna a gefen gadon ta kura masa ido har
tsawon 'yan dakiku sai taji an kwankwasa
kofar dakin cikin sauri lasmin ta waigo, koda
tayi arba da wanda ke shigowa sai ta juyar
da kanta ga barin kallon mai shigowar. Ba
wani bane ya shigo face hizra 'yar likitan
sarki tana dauke da wata tukunyar kasa cike
da rwan magani. Hizra ta tako a hankali ta
iso har gaban gimbiya lasmin, sannan ta
risina ta kwashi gaisuwa. Cikin jin kai da
dagawa lasmin ta amsa gaisuwar batare da
ta dubi fuskar hizra ba ita kuwa hizara sai ta
tsaya a tsaye cak batace uffanba kuma bata
yi komai ba. Cikin fushi lasmin ta dago kai
ta dubi Hizara cikin fushi tace, "Ki a jiye
abinda aka aiko ki ki kawo ki tafi, me kika
tsaya jira?"
Koda jin wannan tambaya sai hizara ta sake
risinawa cikin biyayya tace , "ya shugabata
akwai. Bukatar nayi bayanin yadda za a bai
wa mara lafiyar kamar yadda mahaifina yayi
mini bayani. "
Koda jin haka sai lasmin ta saki fuskarta ta
ce, "Maza kiyi bayanin ina sauraronki. "
Hizara tace, 'Bayani kadai ba zai gamsar ba
sai a aika ce. Da farko dole ne a dafa
wannan magani sau uku a rana a ba shi ckin
kofi ya shanye, kuma lallai da duminsa za a
bashi ya sha. A duk sa'adda aka bashi
maganin ya sha sai kuma a mulke kirjinsa
da bayansa da ruwan maganin. Yana yin
mulka maganin dole ne a dunga danna fatar
mara lafiyar ana lailayata sai tayi taushi
sosai, domin maganin ya ratsa ta cikin
dukkanin kofofin gashin jikiNsa. "
Sa'adda gimbiya lasmin taji haka sai ta tari
numfashin hizara tace, "Duk da haka ina son
ki yi wannan aiki a aikace, domin ban
fashimci yaza a yi shi ba"
Nan take hizar ta dauko kaskon wuta ta dora
tukunyar maganin akai. Dama akwai
garwashi a cikin kaskon wanda ake dumama
dakin da shi. Sai da tukunyar ta sami
tsawon dakiku a kan kaskon, sannan ruwan
maganin dake ciki ya tafasa. Nan take,
hizara ta dauko kofin zinare ta zuba ruwan
maganin a ciki, sannan ta balle maballin
rigarsa ta sake debo ruwan maganin cikin
kofin da zafinsa ta rinka zubawa a kan kirjin
mara lafiyar da kadan-kadan tana mulkawa,
tana danna fatarsa. Nan da nan kuwa ruwan
maganin ya dinga shigewa ta cikin kofofin
gashin jikinsa. Bayan ta gama mulke kirjin
sai ta juya mara lafiyar yayi ruf da ciki ta
kwaye rigarsa nan ma ta mulke bayan da
ruwan maganin bayan ta gama tsaf, sai ta
ajiye kofin a kusa da tukunyar maganin,
kuma ta rufe tukunyar da murfinta. Sannan
ta dubi gimbiya lasmin tace,
"Na kammala ya shugabata. Wannan shine
yadda za a ringa yiwa wannan mara lafiya,
har tsawon kwana bakwai. "
Koda jin haka sai lasmin tayi ajiyar zuciya,
sannan ta dubi hizara tace, "daga yau na
umarce ki da kullum ki zo sau uku a rana
kiyi wa wannan mara lafiya abin da kika yi
masa yanzu, har tsawon kwana bakwai. "
Cikin alamun damuwa hizara tace, "Amma
mahaifina ya gaya mini cewa kece zaki kula
da mara lafiyan."
Lasmin tace, "Wannan gaskiya ne ba karya
ya gaya miki ba, amma yanzu nima na
umarce ki da wakilci na. A matsayina na 'yar
sarki bai kamata na yi wa bako irin wannan
aiki ba. Lallai ki kiyaye wannan doka, kada
ki kuskura kiyi fushi ko da sau daya ne a
rana."
Gama fadin hakan keda wuya sai gimbiya
lasmin ta mike tsaye ta fice daga cikin
turakar kafin ta fice sai da ta juyo ta dubi
mara lafiyar ta yi masa wani irin kallo mai
dauke da alamar tambaya, wanda yasa ita
kanta Hizara ta tsargu kuma tayi zargin cewa
ruwa baya tsami banza, amma kuma bata da
tabbacin abin da take zargi.
Daga wannan rana kullum gimbiya lasmin sai ta shiga dakin bako sau uku, kuma a gaban idanunta hizara ke kula da bakon tana yi masa magani. Sai da aka kwana hudu a cikin wannan hali, amma bakon ko bude idanunsa bai yi ba, bare ya motsa hannunsa ko kafafunsa. Ta hanyar da hizara ke ganewa cewa yana da rai sai ta kara hancinta a dai-dai nasa sannan take jin alamun numfashinsa.
A daren kwana na hudu ne da magariba bayan hizara ta gama yi wa mara lafiyar magani sai gimbiya lasmin tariga ta fita daga cikin dakin a ka'ida kullum da magariba kafin hizara ta fice daga dakin sai ta lullube bakon da mayafi iya kirjinsa, amma a wannan rana sai ta manta ba ta lullube shiba. Har ta kai bakin kofa tasa kafarta guda waje sai kawai taji kamar anyi motsi a cikin dakin. Cikin mamaki hizara ta waigo ta dubi mara lafiyan ta ga babu alamar shi ne yayi motsin, yana kwance kamar gawa. Ta karewa dakin kallo tsaf gabas da yamma kudu da arewa bata ga wani abu mai rai ba kawai sai ta sake juyawa da nufin ta fice ta janyo kofar dakin ta rufe. Ba zato ba tsammani sai ta ji mara lafiyan yayi tari. Cikin tsananin farin ciki ta ruga da baya gare shi taje kansa ta tsaya, nan take mara lafiyan ya bude idanunsa suka dubi juna har yayi mata wani irin kallo mai kama da na tsoro, sannan ya dubi kowacce kusurwa ta dakin sai ya rufe idanunsa bai sake motsawa ba, bare ya sake bude idanun nasa.
Koda ganin haka sai hizara tayi murmushi, domin ta fahimci cewa lafiya ta fara samuwa. A sannan ne ta lura da cewa ta manta bata lullube shiba. Nan take ta janyo mayafin ta lullube shi iya kirji, kamar yadda ta saba, sannan ta sunbaci goshinsa ta fice daga cikin dakin, zuciyarta cike da mamaki bisa dalilin da yasa take matukar farin ciki bisa ganin mara lafiya ya fara samun sauki. Hizara ta bai kanta amsa a cikin zuciyarta tace hakika na fuskanci cewa na shakuda wannan bako a cikin kwana hudun nan rak da nake jinyarsa. Watakila ko dan ya kasance kyakykyawa ne, domin ko yarima zamir bai fishi kyau ba. Haka dai hizara ta fice daga cikin gidan sarautar tana ta wannan zancen zuci.
Daga wannan rana kullum sai mara lafiyan ya bude idanunsa sau daya da magariba yayi arba da mai jinyarsa, wato hizara, kuma wani ikon allah bai taba bude idanunsa ba a gaban gimbiya lasmin, sai bayan ta fita. Haka kuma yakan motsa kafarsa da hannunsa sau dai-dai a kullum sarki mushlik yana shigowa dakin mara lafiyar ya duba shi kuma ya tambayi gimbiya lasmin ko ana samun cigaba sai tace dashi sauki take gani. Raunin dake jikinsa sakamakon kibiyar data soke shi ramin na cikewa.
A ranar kwana bakwai ne fadar sarki mushlik ta cika da jarumai na kasar, zaratan samari masu takama da sadaukanta ka. Arziki da tsafi amma a ga ba dayansu babu kamar haslim dan waziri sharbul, domin duk ya fisu sadaukan taka kuma babu mai arzikin mahaifinsa. Wato a wannan rana mutane sun zo daga dukkanin birane kasar don ganin samarin da zasu yi wannan gagarumar tafiya izuwa birnin sharzas don shiga gasar neman auren gimbiya shulaira, don haka duk inda mutum ya duba ba abinda zai gani face kawunan bil'adama rututu babu masakar tsinke. Ga shidai jama'a sun gama taruwa, amma har tsawon dan lokaci sarki bai fitoba, bare ya gabatar da jawabin taron. Al'amari daya janyo mutane suka kagu da jiran sarki kenan.
A she sarki mushlik tsananin ta kaici ne ya hana shi fitowa, saboda ga dama ta samu wacce yake son ya dora yarima zamir a kai, amma babu ikon amfani da damar. Bisa wannan dalili ne sarki mushlik ya zauna a cikin turakarsa yayi tagumi yana zubar da hawayen bakin ciki. Yana cikin wannan hali ne kawai yaji motsin tafiya an shigo cikin turakar tasa. Cikin mamaki sarki mushlik ya dago kai don ganin wanda ke shigowa. Ba wani bane face yarima zamir. Koda ganinsa sai sarki yayi sauri ya goge hawayensa ya mike tsaye ya tare shi ya ruke kafadunsa yace,
"Ya kai dana menene ya kawoka har nan cikin turaka ta? A iya sanina baka taba shigowa cikin turakata ba, sai yau."
Koda jin wannan tambaya sai yarima zamir yayi ajiyar zuciya yace, "Ya kai abbana nazo ne naji dalilin da yasa kaki fita fada, alhalin jama'a na can suna jiranka?"
Yayin da sarki yaji wannan tambaya sai idanunsa suka ciko da kwalla, har hawaye ya zubo masa sannan yace, "Ya kai dana kayi sani cewa ba komai ne yasa na kasa fita ba face takaicin babu kai a cikin wannan tafiyar da za a yi. Ka tuna cewa kai ne dana wanda ya kamata ya gaje ni, amma saboda rauninka na jarumtaka da rashin kulawarka a kan harkokin mulki ka rasa wannan dama, har ma mutane suna zunden ka a ko'ina,
Koda gama rufe bakin sarki mushlik sai suka ji ance tabbas yarima zamir zai shiga wannan gasa, koda jin haka cikin sauri suka waiga bakin kofa bakowane me wannan magana ba face wannan mara lafiyar.
Mu hadu a TARWATSA MAZA littafi na uku don jin ci gaban wannan labari daga ni mai debe muku kewa kuma masoyinku dan uwanku. Suleiman zidane kd..
Whatsapp 09064179602
*_Haiman Raees_*
_*Phone:*_
08185819176
_*Web:*_ www.haiman.com.ng
_*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees
_*Twitter:*_ @HaimanRaees
_*Instagram:*_ Haimanraees
_*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com