TSARABA GAMASU JUNA BIYU

TSARABA GAMASU JUNA BIYU 


http://dandalinaminuyahuz a.blogspot.com/2018/08/tsaraba-gamasu-juna-biyu.html
MAGANIN YAWAN AMAI GA MAI DAUKE DA JUNA BIYU
🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻
1. A samo kanamfari da HAbbatus sauda {bakin al~garur} a hade su guri guda ana dafawa ana sha
2. Citta citta na taimakawa sosai ga mai amai domin yana kare ciki wajen toshe hanyoyin dake haddasa amai ga iyayenmu mata da suke fama da wannan lalura na amai sai su bi daya daga cikin wannan
~ta rika yin shayi mai citta tana sha
~ta hada citta da lemun kowanne cokali daya tana juice nashi tana sha
~ta rinka tauna citta tare da zuma tana sha
3. Ta samu ganyen Na'ana'a tana yin shayin shi tana sha ko kuma ta rinka tauna ganyen
4. Ta samu man kanamfari ta sanya a cikin ruwan dumi tana sha kadan kadan ko kuma ta samu garin kanamfari ta hada zuma ta gauraya tana sha
5. Ta hada juice na albasa ta sha bayan ta gama sha sai tasha shayin Na'ana'a mai sanyi
Baya ga damuwar amai da iyayenmu mata akwai kuma saurin gajiya wanda kan faru imma ta dalilin yawan aiki mai wahala ko makamancin wannan shi yasa anso in mutum na da dama in matarsa ta samu juna biyu ya neman mata wadda zata rika taya ta aiki don samun cikakkiyar kula ga abin dake cikin , haka nan ana son mai juna biyu ta rika kokarin kwantawa da wuri kuma in zata kwanta ta kwanta a rigingine don jini ya samu ya rika zaga jikin jaririn da take dauke da shi
Haka nan kuma ana so ga iyayenmu da suke dauke da juna biyu su rika yawan motsa jikinsu da cin abinci mai kyau wadda zai taimakamata ya kuma taimakwa jaririn dake cikinta sannan su guji cin abinci mara kyau don gudun fadawa wani hali irin abincin da ake bukata mace ta rinka ci sun hada da
~ wake
~jan nama
~kayan marmari tsaftatacce kamar mangoro,ayaba,gwanda,karas,gwaiba,fiya abarba da sauran.
DAGA DANDALIN AMINU YAHUZA 08080678100
 
Post a Comment (0)