TUN KAFIN AURE 02

TUN KAFIN AURE💐 2


A tsakar gida ta tarar da mamanta tana dinki. Bayan sun gaisa Mama ta tambayetajarabawa. Alhamdulillah tayi sauki sosai. Hmmm kinji ki wai tayi sauki sosai to a bita da addua dai. In sha Allah ta bata amsa tare da shigewa daki. Tunani kawai take yi na yadda zata gabatar da plan din da suka yi da Ummati idan ba haka ba sai dai Saif yayi hakuri. Amma tasan halinsa sarai na fushi. Gado ta fada tana juyi. Idan akwai abinda ta tsana bai wuce fushin Saif dinta ba. Ina ma dai yayi hakuri har zuwa lokacin aurensu sai ayi kowanne hoto yake so ta fada a ranta.

Sauransu jarabawa  uku su gama makarantar gaba daya sai dai har yau ta kasa fadawa Mama. Hafsi ta rasa me yake mata dadi domin kuwa daren jiya da Saif yazo baram baram suka rabu. A cewarsa bai taba tambayarta komai ba sai wannan ta gagara yi masa. Da bacin ransa tayi bacci 'yar wayar daren ma da suke yi yaki kiranta da ta kira kuma yaki dauka.

Shewar Ummati ta jiyo tare da kannenta Amira da Anisa. Da sauri ta fito ta jawo hannunta suka koma daki. Ummati ta kalle ta to sarauniyar masoya yau kuma me ya faru? Tunda naji muryarki kamar zaki yi min kuka nasan an taba zuciyar. Ba kya ma tausayina wallahi naga abin har dariya yake baki. Plate din abincin da Hafsi ta zuba amma tunani yasa ta kasa ci shi Ummati ta dauka tana ci...bakinta cike da abinci tace bana tausayinki zan zo yau. Ai don nasan Baffa yana gida yau ba aiki ne ba bari zaiyi ki fito ba. Ni fada min me ya faru. Hafsi ta zauna kan dadduma tace akan zuwa daukan hoton nan ne fa. Kwarewa Ummati tayi tana kokarin yin magana. Amma dai ke anyi banza wallahi Hafsi, ina ce tun last week muka rufe zancen nan. Ajiye plate din tayi ta tashi ina zuwa...ganin zata fita Hafsi ta bita da gudu tsaya don Allah ina zaki. Ko sauraronta bata yi ba ta shige kitchen wurin mama. Mama kinga Hafsi ko...dago kanta  tayi daga tsintar waken da take yi me tayi miki kuma ku da ba kwa rabo da fada. Wai nace mata ranar da muka gama exams tunda ta safe gare mu ranar tazo muje daukan hoto shine tace wai bazata ba. Mama tun shekaranjiya nake mata magana tana kin bani amsa shine nace bari nazo kawai na fada miki. Kun fiye shirme ke da yar uwar taki meye abin fada a nan. Kinsan halin Baffanku sarai baya son fice fice ba gaira babu dalili nasan abinda take tsoro kenan. Ummati wadda ta zauna a kasa tana taya  ta tsintar waken tace Mama dama wai na tarihi nake son muyi ranar tunda kinga ni Bauchi zan....karasa mana bauchi zamu kaiki ko. Tashi tayi zata gudu Mama tace ba komai zan fada masa ranar da ku ka gama din sai kuje kuyi hoton shikenan ko. Nagode nagode nagode abinda ummati take ta fada kenan har ta fita daga kitchen din. Ita kuwa Mama dariya take sai dai bata san me yaran ke kullawa ba.

********************
Kwance yake kan makeken gadonsa yana zukar wata irin taba mai kauri da tsaho, bai ankara ba kawai sai ganinta ya yi a tsaye bakin gadon. Ah sis saukar yaushe...harara ta galla masa kafin ta fizge tabar. A jikin wandonsa ta kashe ta ai kuwa ba shiri yayi ihu tare da mikewa yana kokarin cire dogon wandon. Sis don mugunta sai ki kona ni me nayi miki kuma daga zuwanki. Ko da ya cire wandon saman gwiwarsa ya fara alamun tashi. Ta zauna ai kadan ma ka gani wutar can tafi wannan. Jin yanayin maganarta yasan mommy ta kai shi kara wurinta ne. Daure fuska yayi yace to idan kinzo ganewa idonki ne kinyi sa'ar gani sai ki fita....rayuwa kowa da tasa so please let me be. Duk ranar da na gaji ke zan fara sanarwa. Yana gama magana ya shige toilet tare da banko kofar da kafa daya. Har zuciyarta taji sautin ta mike a sanyaye. Zuwan Junaid America certificate kala kala ya samu banda na school harda na shaye shaye, neman mata da tsabar kin ji. Baya ganin kowa da gashi ciki kuwa harda mahaifin nasu da ya dage sai dansa yayi karatu mai tsada.

Dakin mommy ta shiga ta zauna a gefen gado tayi tagumi tana jira mommyn ta idar da sallah. Ya dai Nafisa kunyi magana da kanin naki. Hmm mommy ai lamarinsa sai addua kawai ta fada tana tabe baki. Nan ta labarta mata yadda suka yi. Mommy tace to ni dai na gaji zan sanar da Hajiyan Dangi halin da ake ciki kafin yaron nan ya dauko mana magana. Zaro idanu Nafisa tayi cikin tsoro  tace Hajiyan Dangi....wai .



Batul Mamman💖

Post a Comment (0)