TUN KAFIN AURE💐6
Jikinta ne ya hau bari kamar wadda akayiwa wanka da ruwan sanyi a watan december. Iya karfinta ta sa ta fito daga motar har tana ture baffan nata. Da gudu ta tafi gida kafarta ko takalmi babu. Saif kasa motsi yayi a cikin motar ya sunkuyar da kansa. Baffa bai ce masa komai ba ya juya ya nufi gidansa.
Yadda ta shigo a firgice yasa Mama saurin tashi. Hafsa lafiyarki? Me ya faru? Me ya sami yayarki? Ko daya cikin tambayoyin bata amsa ba durkusawa kawai tayi a gabanta tana kuka. Amira ce ta kula da kafarta ta dama tana jini. Mama kinga kafar Hafsi jini take yi. Subhanallahi ke ko hatsari ku ka yi a hanya ne? Ana magana kinyi shiru kamar wata bebiya. Cikin Hafsi har wata kara yayi da jin sallamar Baffa. Bai jira an amsa ba yaja hannun Hafsi zuwa dakinsa. Garammm ya banko kofar har gaban su Mama ya fadi. Ihun Hafsi kawai suka ji tana bawa Baffa hakuri. Tuni Mama ta karasa bakin kofar dakin tana bugawa. Su Amira kuwa sai kuka don tun suna jin kukanta har murya ta dashe. Babu irin magiyar da Mama bata yi masa ba amma yaki budewa.
Baffa ya bude kofa Hafsi na kwance a kasa Mama ta shiga dakin hankali a tashe. Baffan yara me ya faru...ke Hafsa me kika yi? Da kyar Baffa ya iya fada mata tana ta kuka. Ita kam Hafsi hawayenta ba na zafin duka bane kawai. A yau tayi dana sanin abinda ta aikata. Tayi Allah wadarai da maza da matan da basa jin komai lokacin da suke hada jikinsu da juna alhali babu aure a tsakaninsu. Yau ina ranar son zuciya da biyewa shaidan da mukarrabansa wadanda suke tallata irin wannan watsewar da sunan wayewa. Mama da bata zagi yau duk wanda yazo bakinta dankarawa 'yar tata take yi. Tashi ki bani wuri mara mutumci tasa kafa ta haure ta. Jiki a sanyaye haka ta fita tana share hawaye.
*******************
Yau kwana biyu kenan Junaid yana wasan boya da Hajiyan Dangi da mommyn sa. Tun sallar asuba yake fita sai tsakar dare yake dawowa. Hajiyan Dangi lamarin ba karamin bata mata rai yake ba. Sai da ta cika sati a gidan Senator Rufai ya dawo. Bayan ya huta cikin dare wuraren karfe tara yaje dakin da yayar tasa ta sauka.
Hajiyarmu babbar Hajiya zama da tashi cikin girma. Kirarin da ya saba yi mata kenan yau ma bayan yayi sallama tun kafin ta amsa ya fara. Murmushi tayi tana kallonsa Rufai bazaka girma ba. Ai indai ina ganinki bazan girma ba Hajiya. A kan kafet ya zauna kusa da ita. Bayan sun gaisa tace Rufai kayi min laifi gaskiya. Nasani Hajiya kiyi hakuri don Allah. Lamarin Junaid ba karamin bata min rai yake yi ba amma na rasa yadda zanyi da yaron nan. Dole ka fadi haka mana tunda aiki yafi maka akan rayuwar iyalinka, wannan karon cikin fushi take maganar. Kana gefe kana turowa yara kudin da yafi karfin aljihunsu dama me kake tsammani ga yaro da kudi. Shiru yayi don sam baya iya mata musu kuma ma yasan gaskiya take fada masa. Tace to ni na yanke shawara ayi masa aure kawai. Tun zuwana garin nan yaron nan yake gudu na. Anya zaka iya haduwa da Allah akan yadda kayi wasarairai da amanar da Ya baka na yara? Ni bama wannan ba Rufai kaga Allah Ya baka matsayi a cikin al'ummar kasar nan kuma ni da kai munsan ba iyawarka bace tasa ka samu. Zabi ne kawai na Allah saboda haka ina dada baka shawara kamar kullum ka tsaftace dukiyarka. Ka kiyaye haram don ita kadai zata wargaza duk wani al'amarinka. Kafin ta gama magana idanun senator sun cika da kwalla. Dukiya kam suna kai suna wasa da ita son ransu. Ya Allah Ka bamu ikon gyarawa ya fada a zuci.
Gyara zama yayi to Hajiya wa kike jin za'a aura masa? Sayyada ta bashi amsa a takaice. Sayyada ya maimaita shima ban gane ta ba. Bama ka santa ba. Yar wajen Atika ce kanwar Baba(maigidanta). Tun da ta gama secondary ta dawo hannuna bana ma zata gama Buk. Yarinyar tana da hankali da nutsuwa kuma bata daukar wulakanci shiyasa nake ganin zata taimaka wajen shawo mana kan Junaidu. Har zuciyarsa yayi murna. Yace Allah Ya shige mana gaba kuma don Allah a taya mu addua.
Junaid yasha fada wurin mommy karshe tace yaje ya bawa Hajiyan Dangi hakuri. Yana zuwa bakin kofar dakin yaji maganar da suke yi da babansa. Wata dariya ce taso kubuce masa...wa yaga Junaid da auren dole. Ai ko zai dena holewarsa a waje zancen aure bai ma taso ba. Juyawa yayi a hankali tare da yankewa kansa shawarar barin garin a washegari daidai lokacin da yaji Alhajinsu yana cewa idan Hajiyan Dangi zata koma kano zasu tafi tare.