TUN KAFIN AURE💐13
Wallahi Baffa kamar mahaukaci fa yake magana kuma nayi tunanin da gaske yake. Gyara tsayuwa yayi to Saifullahi ai kadan ma kuka gani. Illar irin wannan abin dama ba na lokaci daya bane. Me zaku fadawa yaranku idan suka ci karo da hoton nan gaba? Shin kuna da bakin tsawatar musu bayan sun san borin kunya kawai kuke yi. Allah Ya kyauta ka tafi gida kawai in Allah Ya yarda babu abinda zai faru. Saif kallon Baffa kawai yake yi don yaga kamar bai yarda da abinda ya fada ba. Shi kadai yasan abinda ya gani a idon yaron nan. Jiki a sabule ya juya ya tafi.
********************
Wannan tafiyar kasaitar yake yi har ya shigo gida yana dan fito don yau zuciyarsa fes take. Tunda yazo kano bai sha giya ba sai taba da shisha suma duk a waje saboda sa ido irin na Hajiyan Dangi. Tsohuwar nan akwai hana ruwa gudu. Turus yayi da ya ganta zaune a kan gadonsa. Fuskar nan babu fara'a koma waje kayi sallama ka shigo kamar dan arna kana min fito kamar mai kiwon kare. Haba Hajiya ai dakina ne kuma nasan babu kowa a ciki meye na sallama kuma. Ashe baka san cewa akwai aljanu da malaikun Allah a ko ina ba. Don baka ganinsu hakan ba yana nufin babu su ba. A duk lokacin da zaka shiga wurin da babu kowa sai ka ce Assalamu alaina wa ala ibadullahis salihin. Ai na iya Hajiya bafa complete jahili bane ni. Naji koma dai kayi. Fita yayi yayi mata kyakkyawar sallama ta amsa sannan ya shigo. Cire kaya ya fara yi yana wurgi dasu tace maza ka gama ka tsince min su ga tsintsiya nan ka share dakin. Me??? Ni din Hajiya? Kai mana Junaidu ko kana jin saurayi kamar ka zan bari a share masa daki. Ni wallahi bacci nake ji duba fa ki gani na dawo da wuri shadaya bata yi ba. Ta mike Allah sai ka gyara dakin nan idan ba haka ba zaka ga yadda zanyi da kai. Tana fita ya fada gado sai dai bai gama gyara kwanciya ba ta dawo. Yauwa kayi sallah kuwa?... .au kwanciya kayi ko to tashi ta fada tana dukansa da slipas din kafarta. Dole ya mike Hajiya bana so fa. Sallah kuma nayi don nasan ina da ayyuka a gabana shiyasa ma tun da Baba yazo muka je muka yi sallar asuba ina dawowa nayi duka sallolina ya kare maganar da murmushi. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun shi kawai take fada. Junaidu lalacewar taka har ta kai haka? Shiyasa ka gagara shiryuwa mana. Ta share wasu zazzafan hawaye dake sauko mata. Ashe baka san cewa wutar masu barin sallah daban take ba? No Hajiya nifa nayi ko bakiji abinda na fada bane. Bakin gado ta zauna Junaidu babu wata sallah da zaka yi ba a lokacinta ba da gangan Allah Ya karba. Harma gara lokacin ya wuce maka bisa kuskure sai ka rama. Ita fa sallah kariya ce daga aikin sabo da alfasha. Rayuwa da mutuwa gaskiya ne Junaidu, azaba ko rahmar kabari gaskiya ne, wuta da aljanna ma gaskiya ne. Maganar Hajiyan Dangi da hawayenta sun taba masa zuciya har bai san lokacin daya dora kansa a cinyarta ba yana bata hakuri. Junaidu ka kiyayi Allah sai Allah Ya kiyaye ka. A yau alkawari daya nake nema a wurinka shine na tsayar da sallah. Nayi miki bazan kara bari naji kiran sallah na kasa tashi ba. Ta shafa kansa Allah Yayi maka albarka. Amin
******************
Ummati ana ta rawar kai biki ya gama matsowa da kyar aka barsu zuwa salon don ko gyaran jiki Hafsi bata yi ba. Wannan kuma duk yana cikin punishment din da aka tanadar musu a gida saboda laifin da sukayi don a cewar Maman Ummati itama haka zaayi mata tunda bakinsu daya.
Sai da Saif yayi jan ido sosai sannan kanwarsa Zainab ta fada masa gaskiya ita ce garin binciken waya taga wadannan hotunan a wayarsa ta tura wayarta, daga nan kuma ta tura wa kawayenta. Da belt ya zane ta tana ihu tana bashi hakuri. Ko da mamansu taji dalilin dukan Allah Ya kara tace musu duk su biyun. Ke banda gulma me ya kaiki bincika masa waya....bayan zainab ta koma daki da kuka Maman tace gobe ma ka sake daukan yar mutane kuje yin hoton rashin kunya....istigfar ya rinka yi a zuci. Allah Yasa daga wannan bazasu fuskanci azabar Allah ba. Don kam shi da Hafsi sunyi nadama sosai.
Batul Mamman💖