TUN KAFIN AURE💐 12
Tun kafin ya iso Hajiyan Dangi tasa su Sayyada yi masa abinci. Kusan tafi iyayensa murnar zuwansa ma tunda mommy tayi mata waya ta sanar da ita yana hanya. Alkawari ta daukarwa kanta da yardar Allah yaron nan sai ya shiryu. Ita da kaninta kawai iyayensu suka haifa,tunda bata da nata 'ya'yan nasa sune natan. Idan ta bar dan uwanta ya cigaba da sangarta danshi lallai taci amanar mahaifiyarsu.
A falo ya risketa tana karatun Al-Qurani cikin murya maidadi take karanta suratul Sajda. Wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali yaji yana ratsa masa zuciya ya kasa karasawa cikin falon. Sai da ta kai karshen aya ta ajiye tare da yi masa nuni da ya karaso ya zauna. Bayan tayi addua tace Junaidu dan gudun hijra ka dawo? Murmushi yayi tare da sosa keya. Yi hakuri Hajiyana bazan kara ba. Kallonsa kawai take yi hatta tafiyarsa irin ta babansu ce. Kamar su ta baci. Inama ace yayi koyi da halayen Malam na kwarai.
Haka ta kira 'yan matan gidan nata suna gaisawa dashi. Wai Hajiyan Dangi ta iya kiwo ya fada a ransa. Ba don yunwar yarinyar hoton nan bace kawai a ransa ai da yasan yadda yayi a sami 'yar rage dare ko da daya ce. Wani shegen murmushi yayi, Hajiyan Dangi dake gafe tana kallonsa tayi tana murmushin...sai na gyara maka zama yaro.
*******************
Ko kafar gida Hafsi bata zuwa yanzu Saif dinma Baffa ya hanashi zuwa a cewarsa sa hadu idan an daura aure. Duk abin duniya ya isheta gashi dai zata auri wanda take so amma babu wannan farincikin ko kadan a ranta. Duk surutunta yanzu ta zama wata abar tausayi. Yan uwanta kuwa sai shirye shirye suke yi hankali kwance.
*******************
Ya kusa awa biyu a gefen gidan sannan yaga fitowar wanda yake jira. Tabar hannunsa yayi saurin kashewa ya tada mota ya bishi a baya. Yinin ranar duk inda Saif yayi Junaid na binsa a baya ba tare da ya sani ba. Takaici ne ya isheshi don kuwa baiga alamun anzo gidan da yake nema ba. Karamin tsaki yayi ganin sun kusa karasawa gidansu Saif din. Horn ya rinka matsa masa kamar hauka dole Saif ya tsaya yayi parking. Wannan takun kasaitar ya dinga ya har ya isa kusa da motar Saif. Ganin bai sanshi ba sai ya mika masa hannu su gaisa. Kin karbar hannun Juni yayi daya tuna yadda suka kankame abar sonsa.....abar sona??? Ya tambayi zuciyarsa. Sannu dai, Saif ko? Eh ya amsa masa fuska a sake...Saif akwai fara'a. Shiru yayi don bashi da abin fada abin har ya fara isar Saif. Ban fa gane ka ba wa kake nema ne? Hoton cikin wayar ya nuna masa idanun Saif har wani kankancewa suka yi don tsabar bacin rai. Yayi imani ko mutum daya bai turawa hotunan ba kuma Hafsi ko wayar kirki bata da ita shiyasa ma bai tura mata ba. Juni ya katse masa tunani I want her kuma zan iya biyanka ko nawa ne ka kaini wurinta. Ikon Allah....kai kuma daga ina? Kana ma da hankali kuwa? ba ko kunya balle tsoro kake fada min hakan. To bari kaji na fada maka this coming saturday zata zama mallakina. Kasa karasa magana Saif yayi saboda tsabar takaici ya tsaya yana magana da kwancen hauka. Shafa kai Juni yayi plan dinsa is working. Sai kuma ya yamutsa fuska tunda baka jin lallami kasani cewa nan da ....sai ya dubi agogonsa kamar 20 minutes yarana zasu dauko min ita su kai min ita hotel. Wani mari yaji a kuncinsa kamar wuta kafin ya dawo hayyacinsa kuwa Saif ya shiga mota ya tayar. Shege ya fada yana shafa kunci amma fa marin da zafi...kodayake its worth it.
Bayan Saif yabi har kofar gidansu Hafsi. Yana tsaye a can gefe ya hango wani dattijo mai cike da kamala ya fito sunyi magana da Saif. Yasan bai wuce barazanar karyar da yayi ba Saif din yake fada shi kuwa bukata ta biya dama plan dinsa yaga gidan kuma ya gani. Sauransa jin sunanta duk da a zuciyarsa ya rada mata suna pretty.
Batul Mamman💖