TUN KAFIN AURE 15

 TUN KAFIN AURE💐 15


Hajiya da maigidanta sun rasa yadda zaayi a dauko Junaid saboda Baba baya iya tuka mota idan dare yayi. Suna ta shawarwari ne suka ji karar motar sa. Da sauri  suka fito motar duk ya buge ta a hanya har fitila daya ta lotse. Haka suka kama shi yana ta tangadi sosai suka shiga dashi dakinsa. Hajiyan dangi sai kuka take jin yana ta sumbatu yana cewa ko a aura masa pretty ko ya saceta ta karfi. Haka Hajiyan Dangi ya zauna dashi har yayi bacci shi kuma Baba ya kira senator Rufai ya sanar dashi halin da ake ciki.

Jirgin karfe 7 na safe suka biyo shiyasa kafin karfe 9 sun iso kano. Motoci uku ne suka je tarbar maigirma senate president da matarsa Hajiya Salama.

Gyadigyadi suka nufa gidan Hajiyan dangi. Mommy tana ganin Hajiya ta soma kuka. Bana son irin haka Salama baki san hawayen iyaye cuta ne ga 'ya'yansu ba? Share idon tayi tace kinga irin yadda nake fama da yaronnan ko. Ni fa har cewa nayi baban nasu ya dena saka masa kudi a account amma yaki. Hajiya tace abar maganar nan yanzu bari mu gani ko ya tashi. Su hudu iyayen suka dunguma zuwa dakin da Junaid yake mahaifinsa ya bude kofar ya tarar dashi a kwance yana ta busa taba. Kwarai yayi mamakin ganinsu ya tashi da sauri...mommy na sannu da zuwa. Hannun daya kawo zai tabata ta doke tare da jan tsaki. Yasan fushi take yayi murmushi kawai ya kalli babansa. Oldman ya hanya? Wannan karon Hajiya ce ta doke masa baki. Uban naka kake kira oldman kuma junaidu? Dole kayi ta ganin ba daidai ba a rayuwarka tunda iyayenka ma basu da kima a idanunka. Da ace ka maida hankali kan addini da kasan cewa iyaye sun fi karfin wasa. Duk zama suka yi Senator Rufai ya cire hularsa yasa hannuwansa ya dafe kansa. Ya rasa yadda zaiyi da Junaid fitinarsa kullum karuwa take. Hajiyan Dangi ce ta labarta musu dukkan abinda ya faru game da yarinyar da Junaid yace yana so mai suna Hafsa. Ya maimaita sunanta a ransa yafi a kirga. Baya jin komai game da maganganun da suke yi. Hankalinsa ya tafi can tunanin yadda zai mallaki yarinyar nan mai suna Hafsa.

A wace unguwa suke? Ita ce kalmar da yaji daga bakin mahaifinsa. Da sauri yace sabontiti. Shi kuma wanda zata aura fa? Nan ma Junaid ya bada amsa. Alhaji zaka nema min aurenta? Wallahi nayi maka alkawarin zan shiryu indai na aureta. Hajiyan dangi tace Rufai me kake shirin yi ne? Shima Baba cewa yayi hala ka manta haramcin neman aure akan na wani? Mommy dai binsu ta rinka yi da ido don itama bata san me mijin nata yake nufi ba.



Batul Mamman💖


Post a Comment (0)