Senator Rufai dai bai iya basu amsa ba ya fito ya shiga mota kafin a tayar Junaid ya fito da gudu ya shiga shima. Yana zama senator yace sai ka kwatanta wa Bulus hanyar gidansu yaron. Yaron kuma Alhaji? Ba nema min auren zaka yi ba? Junaid just do as you are told kaina har ciwo yake. Ba gobe ne daurin auren ba? No sai saturday.
Gidan ya fara cika da 'yan uwa da abokan arziki yan daurin aure da biki. Da gudu ya shigo gidan har yana zubar da abincin dake hannunsa wata yayarsu ta janyo shi. Adnan saurin me kake yi ne haka? Yauwa yaya ina baba? Ya amsa yana ta haki. Wannan mutumin da ake nunowa a tv na gani a waje sun zo a cikin motoci masu kyau sai wani mai bindiga yace babanmu suke nema. Kai mai bindiga fa kace...eh wallahi amma na hango na tv din mai kudi ne fa. Jin kamar yana shirme Zainab ta leqa wajen da kanta ai kuwa babu karya wasu jeeps ne guda uku duka bakake amma ta tsakiyar tafi kyau. Ga mutane sun sha suit kowa rike da bindiga.ba shiri ta koma cikin gida ta nufi dakin baban su sai dai a hanya suka hadu har Adnan ya isar da sako. Shima dai mamakin yayi ya matsa wurin daya daga cikin guards din yace shine mai gidan. Yana kallo yaje wurin motar tsakiyar sai ga wasu mutane su biyu sun fito. Ba ko shakka senate president ne Rufai Bukar yasha wata ash shadda kana ganinshi kaga kudi da tsantsar jindadi. Dayan kuwa saurayi ne kyakkyawa amma fa kayan jikinsa kamar anyi wasan kura dashi. Guard din yace ciki zamu shigo. Nan Alh Bashir yace to cikin hanzari yayi musu jagora. Suna shiga jamaa sai binsu ake da ido har falon sa. Maman su Saif ta bi bayansu. Ganin waye bakon ta fito da sauri ta bada kudi a siyo lemuka da ruwan roba.
Alh Bashir ya sake gaishe da senator sai yayi mamakin ganin da kansa ya taso ya bashi hannu. Bayan sun gama gaisawa yace ni sunana Rufai Bukar. Ranka ya dade ai tuni na ganeka ni sunana Alh Bashir. Senator ya kalli Junaid dake zaune kan kujera ba zaka gaishe shi ba. Nan take ya sauko ya gaishe shi. To nasan zaka yi mamakin ganina tare da dana a gidanka ba tare da an sanar da kai ba. Haba ranka ya dade ai nasan dole ce ta sa. To akan maganar yarona ne Junaid... ..haka dai senator ya labartawa Alhaji komai na halayyar dansa da Hafsa da ya gani yana so. Ikon Allah kawai yake fada sannan yace idan na fahimci inda zancen ya dosa so kake Saifullahi ya hakura kenan. Hular kansa ya cire ya dago kai idanunsa da kwalla Alhaji ina tsammanin Allah baiyi maka jarabawar haifar dan da....kai Junaid ku fita. Suna fita ya cigaba da magana wadda sai da hawayen da yake kokarin boyewa suka zubo. Junaid yaro ne me hazaka tun kuruciya amma yanayin aiki da jindadin kudi yasa na sangarta shi. Yaronnan ya janyo min magana fiye da yadda baka zato ga shaye shaye ga....da dai sauran aikin sabo. A bisa amana nake fada maka sirrina Alhaji wallahi wallahi mulki da kudi jarabawa ne sosai daga Allah. Ban farga da munin share lamuran yarana ba sai da naji waazi daga bakin wasu malamai kamar su Daurawa, Kabir Gombe dasu Dr Sani Rijiyar lemo. Nasan nayi barna mara iyaka har ina tsoron ranar mutuwata. To a yau bani da burin daya wuce yaron nan ya shiryu ina ganin wannan zai zama sanadiyar samun rahma a gareni. Da gaske mutumin nan kuka yake Alhaji Bashir ya fada a ransa ganin hawayen senator. Naji dukkan bayaninka ranka ya dade amma yarinyar ba tawa bace. Na sani kuma nasan haramcin nema akan nema. To idan haka ne ko zaka yarda na kira mahaifinta dashi yaron. Ai mai nema ke bi kayi mana jagora gidansu kawai.
********************
Baffa don Allah ka yafe min nasan nayi kuskure wanda bana fatan sake maimaitawa. Hmm Hafsatu kenan ki sani kaza tana taka danta ba don bata sonshi ba sai don ta koya masa hankali. Hakika muna cikin wani zamani da ake tallata zina kamar kayan miya, wanda bai siya ba ma kallon banza ake masa. Amma ina so ke da ku ma...ya kalli Amira da Anisa lallai ku tuna wutar Allah mai radadi ce kuma baya bata da kadan. Sai ka aikata abu ka manta ma dashi watarana ya dawo ma lokacin da baka tsammani. Ki je na yafe miki Allah Ya yi muku albarka. Da farinciki suka tashi dukkansu balle ma Hafsi zuciyarta fes fes. Suna fita Alh Bashir ya kira Baffa ya sanar dashi zai zo gidansa da baki nan da lokaci kadan idan yana gida.
Batul Mamman💖