TUN KAFIN AURE 22

TUN KAFIN AURE💐 22


Ko kayan jikinsa bai canja ba ya fita zuwa hotel din da abokinsa Imran yayi masauki. A waje ya tsaya yayi masa waya. Sai a karo na uku ya dauka ya sanar dashi yana wurin parking ya fito.

Suna hada ido Imi yace yace ya mutumin you sounded worried fa. Me ya faru ne? Envelop din Junaid ya mika masa. Imi ya rinka dariya bayan ya karanta harda hawaye a idonsa. Can ya daki kafadar junaid...haba mutumina kada ka bada ni mana. Yanzu har akwai wata chick da zata ce kayi mata ciki ka yarda? Matan nan fa sun fi mu tsoron faruwar hakan tunda su ke da wahala. Wani abin kawai take so. Fuskar Junaid babu sauran kwanciyar hankali uhm uhm Imi aure fa zanyi kuma Allah Ya sani ina son yarinyar ina kuma son gyara rayuwata. Kaima Allah Ya baka tagari. Kayya yaro gigin soyayya ke dibanka bari romon ya kare zaka neme ni ne. Bayan ina  kallo dazu amaryar taka ta murguda maka baki. Kansa ya shafa yana dariya da irin tsokanar fada ne yaga tana kulashi shiyasa yake mata haka a fili yace Kai kam kamar ana kada maka gangar shaidanu..ya ina cewa zan shiryu kana min mugun baki. To yi hakuri na Hafsa Imi ya fada yana dariya...yanzu dai ka manta da wannan yarinyar kada ma ka sata a rai. Idan ta sake nemanka kaci ubanta da kyau wallahi zata kyaleka. Kada ma ka fara bata kudi don sai tayi blackmailing dinka. Nan suka yi ta shawara sai wurin ukun dare Junaid ya koma gida.
******************

Bacci sam yaki zuwa idanun Hafsi sai tunani take kala kala. Wannan Junaid din dabiunsa na bata tsoro( wai ma don ya rage!) Gashi haka hankalinta bai kwanta da matar da ta bashi envelop ba. Maganar Tilly duk ta tsaya mata a rai wai sun rigata lasar zumar.....ehew abin kyankyami ma zancen ta fada a fili tana yamutsa fuska. Anya ba yan is...sai tayi shiru zargi babu kyau don haka mafitar ta daya shine ta mike ta dauro alwala ta tayar da sallah. Haka tayi ta nafila har asuba tana addua sannan ta yi bacci.

Sai wuraren goma na safe ta farka. Shima Hadiza ce ta tasheta da dundu...to kasa ana shirin fita daurin aure kina kwance kina bacci hankali kwance. Mutssika idanu tayi ta mike...ina ummati ta tafi Yaya? Debo miki ruwan zafi kiyi wanka. Kinsan dai baffa yace karfe biyu zaa bar kano so kiyi da jiki kafin a dawo daga daurin aure. Ta kalli agogon wayarta...Allah sarki nan da mintuna arbain da bakwai kin zama matar aure. Cikinta taji yace kulululu da gaske abin yazo. Kuka tasa wa Hadiza inama basuyi wadannan hotunan ba tun kafin aure da yanzu Saif ta aura. Ummati ta ajiye bokitin hannunta ki gode Allah baa daura dashi ba don yadda aka ce Junaid yayi bayan yaga hotonki da kila a gidan auren zai biyo ki ko ma ya kashe auren. Hadiza tace kyale ta ummati ai tasan wani baya auren matar da ba tasa ba.

Kayan da mama ta dinka da aka hanata sawa daren jiya su tasa ai kuwa tayi kyau sosai. Katon mayafi ta yafa ga kamshi ko ta ina.

Taro yayi taro don manyan mutane na kusa da nesa sunzo bikin dan manya. Junaid yasha cream shadda harda babbar riga da brown din takalmi da hula maroka suna ta sanaar su. Daga karshe dai Liman ya daura auren Junaid Rufai Bukar da Hafsa Aminu Garba.

Mijin Hadiza ne ya bugu ya sanar da ita an daura auren kan sadaki dubu dari gida ya cika da guda da hayaniya. Wata 'yar makarantarsu tace gaskiya Hafsa Aminu kinyi saa muma Allah Yasa mu a danshinku. Yan Amin kuwa suka amsa.

Ansha koke koke lokacin dasu Hajiyan dangi suka zo daukar amarya. Mama kasa daurewa tayi ta kulle kanta a daki. Baffa ma yana mata nasiha yana sharar kwalla. Bai taba tunanin zata yi auren nesa ba, aure ma irin na gidan Senator Rufai Bukar. Motoci har wajen layinsu Hafsi. Cikin motocin kuwa harda wadda Rosie da Tilly suka dauko haya suka bi ayarin kai amarya. Don karfin hali har mutane uku suka dauka aka dauki hanyar abuja.



Batul Mamman💖


Post a Comment (0)