TAMBAYA 1,715
Aslm_Alaykum Malam,
Inada Tambayoyi kamar haka;
Kamar yadda muka sani ana samun yarane tahanyar aure idan namiji ya sadu da matarsa.
Amma scientifically ana iya samun yara tahanya biyu,
{1} Hanyar saduwa tsakanin miji da mata {Natural Reproduction}
{2} Hanyar hada maniyyin namiji da mace {Artificial Reproduction}
TAMBAYA;
Idan mutun Allaah bai bashi haifuwa ta hanyar Natural Reproduction`ba sai yaje aka samarmasa da yara uku {3} ta hanyar Artificial Reproduction.
Bayan faruwan haka da wasu shekaru sai Allaah ya azurtashi da haifuwan yara biyu {2} ta hanya Natural Reproduction.
1.Tambaya; Menene halaccin yin haka a Musulunci?
2. Wadancan Yara uku {3} da`aka samu ta hanyar Artificial Reproduction, yaya rabon gadonsu zai kasance da yara biyu {2} da`aka samu tahanyar Natural Reproduction?
AMSA
1. Baya halatta a musulunci sai Idan an kiyaye sharuda kamar haka
- ya Zama dole sai anyi hakan za a samu yaron babu wata hanya koma bayanta
- ya Zama da maniyyi uba da kwan uwa za a Yi hakan
- ya Zama babu wata illa Mai girma da hakan za jawo ma rayuwar matar bayan yin hakan
- ya Zama a mahaifanta za a saka ba a mahaifar wata ba Wanda daga Baya za a dawo dashi mahaifar uwar
- ya Zama har karshen zangon a cikin mahaifar ta zai zauna Kuma ita zata haifeshi.
2. Dukkansu matsayinsu daya a musulunci saboda dukkansu yayansu ne don hakan yanda Allah ya raba haka za a raba musu
Wannan bayanin na cikin gayawa musdafa Murad
Wallahu aalam
Amsawa Mal Adam Daiyib
