TUN KAFIN AURE 25

TUN KAFIN AURE💐25


Rigar jikin Junaid ta gama jikewa da gumi saboda tashin hankali. Yana ganin iyayensa sun shige yayo kansu ita da Rosie sam ya manta da Hafsi a falon. Ke don ubanki me kike nema ne a tare dani? Idan ciki ne dake ki sa a ranki har abada Junaid bazai taba zama uba ga abinda ke cikinki ba.

Hafsi tana jin furucinsa ta nemi hanyar barin falon rasa wurin shiga tayi don bazata bi su mommy ba a wannan yanayin da suka tashi. tana turo kofar dakin da take tsammani ma na masu aiki ne taji yo Tilly tana dariya...haba Juni boy ai kowa yaci tuwo dani miya ya sha. Ni ka zane a lagos daga na fadi abinda baiyi ma dadi ba. Rosie ta dan dake ta to banza rage muryarki. Ta maida kallonta ga Junaid ai kai karamin dan iska ne don giyar  kudi ce ta kaika tashar iskanci mu kowa, ta nuna kanta da Tilly wahalar rayuwa ce ta kawo mu kaga dole mu fika rashin imani. Tsayawa yayi ya rasa yadda zaiyi dasu. Ya juya ya fita daga falon tare da buga kofa da karfi har sai da gaban Hafsi ya fadi.

Masu aiki ya tarar a barin nashi ya ma manta wai shara akeyi da sauran gyare gyare. Get out ya fada cikin karaji har su Nafisa suka fito daga ciki ita da Hamida. Sauri tayi ta dafa masa kafada Junaid what is wrong? Ban sani ba wannan karon hawaye yake sosai. Ku fita wallahi ko wani yaji ciwo. Ba shiri duk suka yi waje shi kuma ya shiga sabon bed room dinsa. Bai taba tunanin first day dinshi da Hafsi zai zo masa a haka ba. Tsakani da Allah yake sonta don a yadda ya tsara ma kansa ma bashi da niyyar takura mata. A hankali zai bita ya koya mata sonshi don yasan yanzu baya gabanta. Gashi yar tsiwarta da fadan da suke suna burge shi. Drawers ya rinka budewa kamar mahaukaci yana neman kayan maye ko yaya ya gusar masa da hankali ya manta da bacin ransa.

 Wata taba dogowa ya dauko wacce Imran ya kawo masa tsaraba daga Italy. Kujera ya hau ya rufe idanunsa. Yana kunnawa yaji an fizge ta daga bakinsa yayi saurin bude ido. Hajiyan dangi ce tsaye kansa fuskarta jike da hawaye. Haba dan albarka. Yanzu ashe akwai wani maganin bakin cikin rayuwa bayan ambaton Allah da karatun Quran ko sallah? Ashe duk abinda ake fada maka bayan kunne yake bi. Bakin  gado ta zauna dora kansa a kan cinyarta ya saki kukan da yake ta kokarin boyewa. Kyale shi tayi yayi mai isarsa har yayi shiru don kansa. Bai tashi daga kan cinyarsa ba yace Hajiya sai da nake son na canja halayyata kuma sai wannan masifar ta taso min? Kul ta ce masa tana girgiza masa kai. Allah sarki ne mai dinbin rahma da jinkai ga bayinSa. Shekararka nawa kana saba masa Yana hakuri da kai? Meye baka sha ba da aikin neman mata duk sai yanzu don Ya jarrabe ka kake neman kara fadawa ga halaka. Shin ka sani ma ko silar shiga aljanna ce wannan jarabawar? Dago kansa yayi yana kallonta. Hajiya wallahi yarinyar nan karuwa ce. Na rantse miki da Allah ita ta fara nema na a club. Abinda ta fada duk karya ne ya dan sunkuyar da kansa maganar cikin dai bazan karyata ba kila da gaske ne.

Kayi hakuri ka daure kaci jarabawar nan. To Hajiya zancen Hafsa fa? Ya zanyi da ita idan taki ni. Murmushi Hajiya tayi ,kasa Allah a ranka yarona komai  zaizo da sauki. Hafsa tayi min yanayi da mutanen kirki idan ka nuna mata kai mutumin kirki ne sai kaga Allah Yasa ta zauna da kai lafiya.



Batul Mamman💖


Post a Comment (0)