TUN KAFIN AURE 36

TUN KAFIN AURE💐 36



Senator Rufai yace Allah Yasa magajiya ce sai ka aureta. Yau kaine kake kiran wata karuwa? Ka manta irin kukan da mahaifiyarka ta rinka yi lokacin da kake bibiyar matan banza. Yau gashi a sanadiyar hakan Junaid wasu yan iska suna neman bata min suna. Duk rayuwar da nayi a politics ina taka tsantsan saboda abokan gaba. Hajiyan dangi dake zaune a gefe ta dago kai cikin fushi lallai ma Rufai ashe duk abinda kake ba saboda lahirar mu kake yi ba. Dama saboda mutumcin siyasa kake yi. To wallahi ka sa a ranka duk abinda ya sameka kai ka jawo tunda babu abinda kake don Allah. Mommy dai kuka take don abin yayi mata yawa. Hajiya tace Junaidu? Ya amsa mata cikin kuka. Ina so kayi wa babanka biyayya hakan shine shaidar ka shiryu. Kuma da yardar Allah zaka ci jarabawar da Yake yi maka. Tashi ka tafi Allah Yayi maka albarka. Yana fita mommy ta hau rokon a janye maganar aure. Yace kun kasa fahimta ta ne Hajiya. Nasan ina son kare mutumci na amma ki duba ki gani indai yayi mata cikin da gaske kada su sami abin tozarta shi nan gaba. Bani da burin da ya wuce  naga iyalina suna zaune cikin kwanciyar hankali amma hakan bazai taba yiwuwa ba sai mun toshe duk wata kofar da wani zai iya samun damar daga mana hankali. Senator yayi iya kokarinsa wurin ganin iyalinsa sun amince da auren don a iya tunaninsa da haka ne kawai zaa iya toshe bakin su Talatu.

Kamar wanda aka jefo daga sama kawai ganinsa tayi a cikin dakinta. Yar tsiwar data yi niyar yi masa saboda ya shigo mata daki ba sallama ma kasawa tayi saboda wata irin runguma da yayi mata. Cikinta ne ya soma zafin wurin da ta kone ta fara neman ya sake ta. A kunnenta taji yana magana cikin muryar kuka har hawayensa na sauka a kafadarta. Hafsi please dont ever leave me. Dole ta hakura ta tsaya har ya gaji don kansa sannan ya ja hannunta suka zauna a bakin gado. Kansa ya dora kan cinyarta sannan ya fara magana. Alhajinmu yace lallai sai na auri Tilly. Dama tasan haka zata iya faruwa sai dai tayi shiru ganin kamar bai gama magana ba. Na fada masa karya tayi min amma yaki yarda. Hafsi ke kadai kin isheni rayuwa ina tsoron hadaki da kwararriyar yar bariki. You are too innocent bazaki iya kishi da ita ba. Gashin kansa ta shafa indai Alhaji ne ya baka umarni to don Allah kayi masa biyayya. Kada ka manta aljannarka tana tare da farin cikin iyayenka a kanka. Tana gama magana yaga ta share kwalla yayi  tashi zaune kingani ko tun yanzu kin fara kuka. Sai kuma ya kashe mata ido ko dai kishi ne ya motsa. Kyakkyawan rankwashi ta sakar masa ya dafe kai yarinya baki sanni ba ko. Sai a lokacin ya kula ashe daga ita sai wani towel iya gwiwa. Yayi wata dariya yau zaki gane nima mugu ne. Towel din ya kama daga daidai kirjinta yana ja tana ja. Muryarta na rawa tace zan maka ihu fa? Ai idan kika ji mace tana zanyi ihu ba yin zata yi ba. Besides ba zaki so a shigo a ganki a haka ba. To naji ta ce masa, don Allah kayi hakuri bazan kara ba. Kallonta ya rinka yi cike da so yace come here. Sake rungume ta yayi yana shakar kamshin  jikinta. Shima kansa yana mamakin yadda yake iya kasancewa da ita kuma ya iya hakura ba tare da ya nemi biyan bukatarsa ba. Ya amince wannan shine true love.

Haka suka kasance suna nunawa junansu kulawa har ranar asabar ta zagayo wadda ranar Baffan Hafsi da Alh Bashir zasu iso abuja kuma ranar ne auren Junaid da Talatu Jibo Aka Tilly.


Batul Mamman💖

Post a Comment (0)