Wayewa ko Fasikanci?
*BUDURWA A DAKIN SAURAYI A MATSAYIN MURNAR SALLAH*
Wannan fasikanci ne ba wayewa ba, kuma dabi'a ce ta Yahudu da Nasara. Wannan ba al'adar mu ba ce, saboda wannan ya saba umurnin Allah da Manzonsa. Allah ya ce:
{وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا } [الإسراء: 32]
"Kada ku kusanci zina, saboda ya kasance alfasha ne kuma mummunan hanya".
Babu abin da ya kai kebancewa a daki tsakanin mace da namiji kusantar zina.
Annabi (saw) ya ce:
لا يخلون أحدكم بامرأة، فإن الشيطان ثالثهما
مسند أحمد (1/ 269)
"Lallai kar dayanku ya kebance da wata mace, saboda Shaidan ne na ukunsu".
Saboda haka a matsayinki ta mace Musulmah, haramun ne ki kebe da namiji wanda ba muharraminki ba ne, saboda babu wani abun da ke tsakanin mace da namiji in suka kebe banda Shaidan.
Shaidan ne zai kasance a tsakiyarsu, ya yi ta kwadaitar da su sabon Allah mai girma, ya yi ta rairaya musu alfasha.
Ya ke yar uwata, ki sani wannan ba wayewa ba ne, bata ce, kuma ba mutuncinki ba ne.
Kawai namiji wanda bai aure ki ba ya gayyace ki dakinsa, ke kuma ba kunya ba tsoron Allah ki kama hanya ki je?!
To ke a tunaninki, in kin je me zai faru?
Ba wani Alkhairin da zai faru sai sabon ALLAH.
Me zai sanya ki zuwa dakin saurayi?
Soyayya?
Son kudi (abin Duniya)?
Ko wayewa?
Yar uwata duk saurayin da yake sonki na gaskiya, so na aure ba zai taba ce miki ki zo dakinsa ba, ko ku tafi wani otel, sai dai in daman yaudararki yake. Domin duk saurayin da yake kaunarki dan Allah zai taya ki kare mutuncinki da neman kusanci ga Allah mai rahama.
Son abun Duniya: da yawa wasu matan son abun Duniya da rashin tsoron Allah ke sanya su zuwa dakin saurayi, domin da man su na banza in ne, sun san zinar ce za su aikata, domin samun abin Duniya da fasikanci sai su je.
Wasu dan sun ga kawayensu, sun sanya kaya masu tsada sai su fara tunanin ko ta ina su ma sai sun yi kokari sun sanya, to daga nan sai su fara neman kudi ko ta ina, ko ta hanyar Haram bai dame su ba.
Wasu kawaye ne ke jefa su a wannan harkar. Wata qawa ce za ta zuga ta ta nuna mata ba komi, ai mai wucewa ne, ita kuma mara tunani idan ba a yi sa'a ba ta amince. Shi kenan ta halaka!
Wallahi gara kin zauna a Duniya yar uwata, ba ki da abun kyalkyalin Duniya, da ki je lakhira ki zamo cikin wuta. Kina nadama.
Dan Allah mata a kiyaye, mu zamo masu tsoron Allah.
Dan Allah Yar uwata, duk wata qawa da ta ce miki: ki raka ta dakin saurayi ki rabu da ita. Domin mata da dama ta dalilin haka rayuwarsu ta lalace, wasu sun dawo mazinata, wasu an bata musu rayuwa, wasu sun gamu da matsalar fyade.
Wayewa: ke yar uwata da man akwai wata wayewa da ta fi ta addini Musulunci?
Addinin da ya ba ki duk wata gata?
Me ya sa ba za ki yi aure ba, ki je ki waye a dakin mijinki?
Da an tabo ki, ki ce ba yanzu ba aure, amma kuma kullum ga ki a wancan dakin saurayin da kuma wancan otel. Ke ba ki tsoron gamuwarki da Allah mai tsananin Azaba?!
Yar uwata kar ki yadda wani saurayi ya ce ki kawo masa abinci a wani gida ko wuri ko anguwansu, ai ke ba ki zama matarsa ba.
Yar uwata duk saurayi da ya nuna miki hanyar sabon ALLAH, kika yi mai nasiha ya ki ji, to dan Allah rabu da shi. Allah zai ba ki wani. Ke dai ki zamo mai neman zabin Allah da imani da kaddara. Ki godewa Allah a duk halin da kika sami kanki.
Ki guji zina, zina muguwar cuta ce. Haramun ne, akwai azaba mai radadi ga masu yinta.
Zina tana cire kunya, tana fusata Ubangiji. Allah ya hana zina, kuma Annabi S A W ya isar mana sako.
Shin kin san ranar mutuwarki?
Shin ba ki tsoron gamuwarki da Allah?
Ba ki tsoron kar ya zamo kina aikata zina ki mutu?
Meye makomarki?
Shin kin san cewa; mai zina ba ya kasancewa da imani?
In kika koma ga Allah ba imani 😭 me ma'anarsa?
Mazinaci ba ya kasancewa da imani a sanda ya ke zina....
«لا يزني الزاني حين يزني وهو مؤمن»
Bukhari da Muslim
✍Rashededah Bintu Abubakar (daughter of Islam).