http://sirinrikemiji.blogspot.com/2018/07/yadda-zaki-samu-shiga-wajen-uwar-mijinki.html
Iyaye sunada matukar tasiri a zamantakewar aure da 'ya'yansu a kowani hali da kuma yanayi.
Don haka nema a zamanin baya iyaye ne ke zabawa 'ya'yansu maza ko mata wadanda zasu aura, hakan kuma yayi matukar tasiri a wannan lokacin ganin yadda ake samun aure na mutu ka raba sabanin abubuwan da suke faruwa a yanzu. Duk kuwa da wasu gidajen har yanzu iyaye ke da alhakin nemawa 'ya'yansu wadanda zasu aura.
Rashin jituwa ko fahimta da ake samu a tsakanin iyayen miji da matarsa ya fi yawaita a tsakanin uwar miji, domin yana da matukar wuya kiga cewa uban miji ne ya takura matar dansa ko kuma basu zaman lafiya da juna. Wannan dabi'ar da ko nace al'ada yafi yawaita ne a tsakanin uwar miji da kuma matar danta, wanda wasu da dama na mamakin abubuwan dake haddasa irin wannan matsalar.
Ga duk wata matar datake son more zaman aurenta, ya zamemata wajibi ta sha maganin zama da uwar mijinta ko da kuwa ba a gida daya suke ba ko kuma gari guda kai koma kasashen da suke zaune ya babbanta.
Muddin uwar miji bata yi dake, to ko bongon duniyan nan kika tafi da mijinki kuka zauna don gudun matsala ko tashin hankali, to kinyi a banza muddin dai suna haduwa da danta ko tana magana dashi. Don haka abun yi kawai shine duk irin son datake miki kamin aure, to ki tabbata kin kara samu wasu dabarun iya zama da ita.
Kuskuren da akasarin mata suke yi shine, na rashin yiwa uwar miji ladabi da biyayya don wai tana tunanin cewa mijinta yana sonta. Babu dan kwarai da zai bari matarsa ta wulakanta masa uwa don dai yana sonta. Dole ne duk darajar ki ko na gidanku ki nunawa uwar mijinki ladabi da biyayya fiye ma da iyayen da suka haifiki domin ke dolen iyayenki ne amma ba dolen uwar mijinki bace.
Komin tsufanta, komin talaucinta ya zama babu raini ko tsana tskanin ke da ita, koda kuwa a zahiri bata sonki, ki ci gaba da yi mata biyayya watara dole ta saduda
Wani abun kula kuwa shi ne, kada ki sake ki aure namijin da kika tabbatar da cewa uwarsa bata kaunarki komin son da kike masa ko kukewa juna ki hakura, idan kuwa kika ki auren bazai jima ba kina iya zama bazawara.