YAYA AKE YIN ISTIKHARA?



TAMBAYA
========
👇
Dr Don Allah ina son ka koyamin yadda xan yi istahara domin neman xabin Allah. 

Muna soyayya da wata baiyawar Allah kuma muna kaunar junan mu.



AMSA
=====
👇 
  Hadisi Ya tabbata Ruwayar Bukhari Mujallad na 7, Shafi na 162, daga Jabir Dan Abdullahi, Hadisi mai Lamba ta 1162.
 Jabir Dan Abdullahi Allah ya kara masa yarda yace, Manzon Allah saw yana karantar damu ISTIKARA a cikin Al'amuranmu Gabaki daya, kamar yadda yake karantar damu Sura a cikin Alqur'ani, Harma Manzon Allah yana cewa damu, idan dayanku yayi Yunkurin gabatar da wani Abu, sai yayi Nafila Raka'ah biyu, idan ya sallame sai yace, ALLAHUMMA INNIY ASTAKEERUKA BI-ILMIKA, WA-ASTAGFIRUKA BI KUDRATIKA, WA-AS'ALUKA MIN FADLUKAL AZEEM, FA INNAKA TAQDIRU WALA AQDIRU, WA TA'ALAMU WALA A'ALAMU, WA-ANTA ALLAMUL GUYUB, ALLAHUMMA INKUNTA TA'ALAMU ANNA HAZAL AMRA(Sai ki Ambaci bukatarki) KAIRAL LIY FIY DEENIY WAMA'ASHIY, WA AQIBATU AMRIY AJILIHI WA'AJILIH, FAQDIRHU LIY WA YASSIRHU LIY, SUMMA BARIKLIY FIYHI.
    WA INKUNTA TA'ALAMU ANNA HAZAL AMRA SHARRALLIY FIY DEENIY WAMA'ASHIY WA AQIBATU AMRIY AJILIHI WA'AJILIH, FASRIFHU ANNIY WASRIFNI ANHU, WAQDIRLIYAL KAIRA HAISU KAANA, SUMMA ARDINIY BIHI.

 Idan kuma mutum yayi wannan Addu'ar Allah zai rinjayar masa Abinda yafi zama masa Alkairi, sannan kuma ya sanya masa son wannan Abun a zuciyarsa. Kuma ya tabbatar masa dashi insha Allahu.

Allah shine Masani 


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876
Post a Comment (0)