AIKIN GWAMNATI GA ƳA MACE MUSULMA

👌👌 *_Yar karamar tunatarwa_*👌👌


    Assalamu alaikum 

*_Aikin gwamnati ga ya mace musulma kuma matar aure_*

An karbo hadisi daga Anas yace Manzon Allah s.a.w yace Duk mutumin da yayi aure ya cika Rabin addininsa domin cika Rabin to ya tsaya yaji tsoron Allah s.w.t..... Ibn majah🙏🏻🙏🏻

Ibn Abbas yace Manzon Allah s.a.w yace *_Aure shine yake wanzar da cikakkiyar soyayya (tsakanin Mata da miji) wadda in ba aure ba babu wani Abu da yake haifar da soyayya irin wannan_*“ Ibn Maajah 


          *Ki fahimta*

Soyayya domin Allah, abu ne wanda yake da asali sosai acikin addini. Kuma yana daga cikin ayyukan da suke janyo ma bawa samun yardar Allah wacce ita ce kololuwar abar nema awajen dukkan Mumini.
Sannan Idan an duba ta fuskar tarihi ma za'a iya cewa dashi ne Addinin nan na Musulunci ya ginu.
Manzon Allah(saww) yana cewa:

"HALAYE GUDA UKU, DUK WANDA YA KASANCE SUNA CIKINSA, TO YA DACE DA SAMUN
DANDANON ZAQIN IMANI:

1. YA KASANCE ALLAH DA MANZONSA YAFI SOYUWA AGARESHI FIYE DA WANINSU.

2. YA KASANCE YANA SON WANI BAWAN ALLAH, BA DON KOMAI BA SAI DOMIN ALLAH (SWT).

3. YA KASANCE YANA QIN KAFURCI; BAYAN ALLAH YA TSAMOSHI DAGA CIKIN, KAMAR YADDA YAKE QIN AJEFA SHI ACIKIN WUTA.

(sahihin hadisi ne, bukhari da muslim suka ruwaito shi).

Tabbas ya halatta kiyi aikinki Amma ki kiyaye da wadannan abubuwa domin duk inda zaki je akwai haqqoqin mijinki akanki kuma ababen tambaya ne Ranar yi miki hisabi 🙏🏻


     *Idan kinje Gurin aiki*

1- ki tuna Mijinki bai lamunce miki kiyi shira da kowa ba sai in abinda ya zama wajibi kuma ya shafi aikinki 👌

2- A matsayinki na matar aure ba wajibi bane sai kowa kin faranta masa rai....... ba faranta musu rai ne ya kaiki ba..... Domin a kokarin faranta musu rai zaki halakar da kanki 👌


3- akwai hijabi a tsakaninki da duk wanda ba muharraminki ba... saboda haka dangane da al'amuran rayuwarki kada ki kokarin yin abinda zasu yaba miki..... domin yabon mijinki ya isheki 👌

4- Gaisuwa ma bata zama wajibi a tsakaninki da wanda ba muharraminki ba sai dai idan gurin zama daya ne ya hadaku a gurin aikin wannan babu laifi 👌

        *Daga karshe*

Da mijinki ya amince kiyi aiki Amana ya baki ke kuma kin dauki alqawarin rike amanar kada ki fada cikin wadannan Alamomin da manzon Allah s.a.w ya lissafa cewa

Duk wanda ya kasance a 
wadannan alamomin shi munafiki ne 1. Cin amana, hakika maci amana manzon Allah )s a w( ya kirashi da munafiki.
2. Mai karya alkawari, shima yana daga cikin alama ta munafurci ashe alkawari ba abin wasa bane.
na Ukunsu shine uwa uba.
3. Qarya

.... Kuma makomar munafiki shine wuta 

Allah s.w.t ya tsare mu 

Daga 
     Zauren 
*MIFTAHUL ILMI*

*_Rubutawa_*:- Yusuf Ja'afar Kura

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren 🔑 _*MIFTAHUL ILMI*_🔑 a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)