ALKHAIRI MAI YAWA DA LADA MAI GIRMA 2

ALKHAIRI MAI YAWA DA LADA MAI GIRMA


FITOWA TA BIYU-(2)

*4-Shin kana son samun lada dubu kuma a kankare maka zunubai guda dubu??*

Amsa;
Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Shin yanzu dayanku zai kasa ya gajiya akan samun lada dubu a kowane yini??*sai Sahabbai R.A suka tambaye shi,Ta yaya dayanmu zai sami lada dubu a yini?? Sai Manzon Allah SAW yace;
*(Mutum yayi Tasbihi guda dari"Wato yace SUBHANALLAH sau dari",sai a rubuta masa Lada guda dubu kuma a kankare masa laifuka guda dubu)*.
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ.

5-Shin kana son Allah ya jikanka kuma Rahamar Allah ta sameka??

Amsa
Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Masu jin kai da tausayi suma Allah mai jinkan da rahama yana jinkansa yayi masu Rahama,kuji kai da tausayin bayin Allah da suke kasa,sai wanda yake sama Allah yaji kanku yayi maku Rahama,sunan ZUMINCI an ciro sane daga sunan Allah ARRAHMAN,duk wanda ya sadar da zuminci shima Allah zai sadar da shi,wanda ya yanke zuminci shima Allah zai yanke shi)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ.

6-Shin kana son samun haske daga Juma'a zuwa wata juma'a??

Amsa
Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Dukkan wanda ya karanta suratul Kahfi a ranar juma'a,Allah zai sanya masa wani haske daga wannan juma'ar zuwa wata juma'a)*
@ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ.

7-Shin kana son Allah ya gafarta maka abinda ya gabata na zunubanka??

Amsa
Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Dukkan wanda ya azuminci watan Ramadhana yana mai Imani yana mai kwadayin lada,an gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa)*
@ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ.


Allah ne mafi sani.


Allah ka bamu ikon aikita aiyukan alkhairi masu yawa tare da kyakkyawar niyya amin.
Post a Comment (0)