ALKHAIRI MAI YAWA DA LADA MAI GIRMA 1

ALKHAIRI MAI YAWA DA LADA MAI GIRMA


Darasi na farko-(1)


1-Shin kana son Allah ya karba addu'ar kuma a biya maka buqatunka kuma a gafarta maka zunubanka???


Amsa:
Manzon Allah SAW yace:
*(Lallai Ubangijina Allah wanda albarkarsa ta yawaita kuma ya Daukaka,yana saukowa a kowane dare alokacin da kashi ukkun karshe na dare ya rage,yana cewa;
*"Wanene zai rokeni in amsa masa"*
*"Wai zai fadi buqatarsa na biya masa"*
*"Wanene zai nemi gafarata in gafarta masa"*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ.

2-Shin kana son yin Sadaka daga dukkan gabbanka na jiki??

Amsa
Manzon Allah SAW yace;
*(A kowane yini gabban dan Adam suna wayewar gari akan an dora masu aikin sadaka,kowane Tasbihi Sadakane,kowane Tahmidi sakadane,kuma kowane Tahlili sadakane kowane Takbiri sadakane,yin umarni da kyakkyawan aiki sadakane,hani daga aikata mummunan aiki sadakane,yana isar maka ladar sadaka akan kowanr gabbai naka,yin sallar Wallaha raka'a biyu)*.
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ.

3-Shin kana son samun ceto har a gafarta maka zunubanka???

Amsa
Manzon Allah SAW yace;
*(Lallai akwai wata sura acikin alqurani,tana da ayoyi guda talatin,tana ceton mai yawan karantata har sai angafarta masa,itace Suratut Tabarakal llazi biyadihil mulku)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ.


Allah ne mafi sani.


Allah ka bamu ikon aikita aiyukan alkhairi masu yawa tare da kyakkyawar niyya amin.
Post a Comment (0)