🔮🔮🔮🔮🔮🔮
*ƳAN MATAN ZAMANI*
🔮🔮🔮🔮🔮🔮
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI.
Matan wannan zamani dai da yawan su sun faɗa halaka, wasun su jefa su aka yi, wasu kuma jefa kansu suka yi, Yayinda wasu kuma sakaci ne ya jawo har suka faɗa cikin halakar, sai dai koma menene dalilin, Muna fata Allaah Ya Shirye mu baki ɗaya.
A yau In Shaa Allaah ina so ne inyi magana akan Iri matan da su da kansu suke cusa kansu cikin halaka saboda Soye-soyen zukatan su. Haƙiƙa ni na yarda cewa kowane ɗan Adam yana laifi, kuma yana buƙatar Nasiha, Addu'a da kuma Uzuri. Sai dai abubuwan da na gani da idanuwana da kuma waɗanda naji daga Majiyoyi Sahihai ne suka sani yin wannan tsokaci a yau.
WACECE MACEN ZAMANI?
* Macen Zamani Ita ce wacce babu ruwanta da duk wata Koyarwar Addinin ta na Musulunci ko kuma kyawawan Al'adun da ta gada.
* Ita ce macen da bata damu da abin da zai je ya dawo ba, matuƙar dai ya dace da tunanin ta ko ra'ayin ta.
* Ita ce wacce Bata damuwa don ta taka dokar Allaah, saboda tana taƙamar babu wanda ya isa ya tanka mata.
* Ita ce Wacce tunanin Wayewar ta ya kai wani mataki yasa take yiwa kowa kallon hadarin kaji.
* Ita ce wacce take ganin cewa dai-dai ta ke da kowa.
* Ita ce wacce take ganin cewa ta fi ƙarfin Shari'a, don iyayen ta ko dangin ta kuwa, bama a bi ta kansu.
* Ita ce wacce kullum Malaman da ke Nasiha kan Abi Allaah suke shan Zagi a wajen ta ba ƙaƙƙautawa.
* Ita ce wacce Aure baya gaban ta, a dai huta kawai.
* Ita ce wacce ta Rungumi ɗabi'un YAHUDU da NASARA hannu bibbiyu.
Ya ke ƴar uwa ta, shin me ya kaiki ga shaye-shaye? Ashe bakya ganin maza ma masu shaye-Shayen wasu ƙananun dodanni suke komawa? To ina ga ke? Me ya kaiki yawace-yawace? Shin kina tunanin cewa wannan hanyar itace mafita a gare ki?
Wani ƙarin abin haushi kuma shi ne, shuwagabannin da ya kamata ace suna sa ido tare da bada gudunmuwa wajen gyaran tarbiyan Al'ummah, sai ka taras da su suna sheƙe ayar su da irin waɗannan ƴan matan, da kunni na naji wata tana faɗin sunan wani hamshaƙin ɗan siyasa da ke nan Kaduna da kuma farshin da yake biyan duk wacce ya kwanta da ita, na bincika kuma Majiyoyi da dama sun tabbatar da hakan. Amma da anyi magana sai kaji ana kawo wasu dalilai na banza da wofi don a kare kai.
Ya Allaah ka kiyaye mu, ka shirye mu, ka yafe mana laifukan mu, ka amshi tuban mu kuma ka yi mana rahama ba don ayyukan mu ba.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaika.
<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________
●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●
<••••••••••••••••••••••••••••>
👳🏻♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>
*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng
*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees
*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees
*_"""""""""""""""""""""""_*
🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...