BAKI MAI YANKA WUYA

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴
 *ABOKIN FIRA * 
 *Rubutawa:* _Dr. Muhammad Mansur Sokoto_
 
 *DRS NA 010* 




 *Baki Mai Yanka Wuya*
A wani gari da ake kira Naisabur aka yi wani kasurgumin barawo
wanda ya yi suna wajen fashi da makami. Ya tare wata babbar hanya
yana kashe mutane masu wucewa. An yi juyin duniya domin a kamo
shi amma abin ya faskara. Watarana sai Sarki ya yanke shawarar yi masa afuwa har ma da ba shi mukami don ya zo ya yi saranda a zauna
lafiya. Sarki ya sa aka yi shela cewa, ya ba da aminci ga wannan dan fashi idan ya kawo kansa. Hakan kuwa aka yi. Dan fashi ya ajiye
makaminsa ya koma cikin mukarraban Sarki.
Watarana suna zaune ana cin abinci ana fira sai aka kawo naman gasasshen tsuntsu, sai dan fashin nan ya sa hannunsa ya dauki naman
tsuntsun nan sannan ya fashe da dariya. Sarki ya yi mamaki kuma ya
tambaye shi dalilin dariyarsa. Dan fashi ya kada baki ya ce, wani bawan Allah ne na tuna da shi da ya taba yi min wata irin wauta. Sarki ya ce, kamar yaya? Ya ce, a lokacin da ina fashi da makami ne wani
wawan mutum ya zo zai wuce, sai na tare shi, na neme shi ya kawo
duk abin da yake hannunsa. Bayan ya ba ni duk kudin da yake da su sai na ce masa ya cire tufafinsa. Ba don yana so ba ya cire su gaba daya ya koma tsirara. Har ya juya ya tafi sai na sake kiran sa. Haka kawai rashin imani ya taso mani sai na ji ina son in kashe shi. Ya roke ni don Allah in kyale shi na ce, sam ban san haka ba. A lokacin da zan cire wuyansa sai irin wannan tsuntsu ya shuda zai wuce, saboda tsabar wauta sai ya kira tsuntsun wai ya yi masa shaida cewa, ni na kashe shi.
Ran Sarki ya baci matuka da jin wannan labari, da irin rashin tausayin da barawon ya nuna ma wannan bawan Allah. Sai ya ce, Alhamdu lillahi. Daman ni na amintar da kai ne don ba ni da wata
shaida kakkarfa cewa ka taba kashe wani. Amma yanzu tun da yake
wannan tsuntsu gasasshe ya yi shaida a kan ta’addancin da ka yi ma wannan bawan Allah, kuma kai ka tabbatar da wannan shaidar tasa
babu makawa yau zan dauki fansa a kan ka. Nan take kuwa ya sa askarawa suka kama shi aka lankwashe hannuwansa ta baya aka
daure shi. Sannan aka yi shela kowa ya zo domin shaidar yadda za a
tsire shi. Aka kira Sarkin sara ya tsire shi sannan ya cire kansa, jama’a suna tafi suna murna. Allah ya hutar da kowa da sharrinsa.

 *Darasi:* 

▶ Baki shi ke yanka wuya.

▶ Duk abin da kake yi ka sa tsoron Allah, kuma ka ji tsoron ranar da Allah zai kama ka

▶ Azzalumi komai ta daxe watarana sai Allah ya kama shi. Rana dari ta barawo, daya ta mai kaya.

▶ Tausayi sifar mutanen kirki ce

📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕
Email: jibwissocialmediaktlg@gmail.com
Facebook: Jibwis Katsina L.G 
WhatsApp: 07062584992, 08038977817, 08034453678, 08036958490.
Post a Comment (0)