TUN KAFIN AURE 45

TUN KAFIN AURE💐45




Da kyar ya mika hannu ya dauko wayarsa don ya kira imran. Kansa ne yake juyawa saboda tsabar ciwo ga zazzabi da ya rufar masa lokaci guda. Missed call din Hafsi ya gani take yaji zuciyarsa tayi masa sanyi. Kiranta yayi amma har wayar ta kare ringing bata dauka ba.

Tsaki tayi ganin me kiran ta wurga ta kan gado tare da tayar da sallah. Husna ce ta shigo dakin jin waya tana ringing ta dauka ta fita Maama ga wayar Mama Hafsa tana ringing. Nafisa ta ajiye remote din hannunta ta kalli Husna. Yanzu wa yace ki dauko mata waya? Maama sallah take yi. Kinga an sake kira ma. Nafisa ta karba ganin sunan Junaid tayi saurin dauka. Tana jin muryarsa ta mike tsaye Junaidu  kana ina? Jikinta har rawa yake yace sis kece? Sautin kukansa taji yace i need you please. Kizo gidana yanzu. Kwalawa Hafsi kira tayi ki fito muje gidan Junaid Hafsi ina jin akwai matsala don maganar da yake ma ya dena. Hafsi najin haka itama kukan ta fara suka dunguma waje driver ya kaisu unguwar maitama inda gidan Junaid yake. A hanya ta kira mummy ta fada mata itama duk ta rude don tasan ko ba a fada ba dan nata yana cikin matsala.

A falo suka tarar dashi yana ta rawar sanyi ga gumi ya gama wanke shi har rigarsa ta jike. Nafisa tace da drebansu yazo ya dauko musu shi asa shi a mota. Hafsi tace bari a rage masa kaya jikinsa yayi zafi sosai. Ina ne kitchen ma, duk ta rude tayi nan tayi can. Nafisa ta nuna mata da hannu tana dago kan Junaid.

Wata irin faduwar gaba taji lokacin da taga Tilly kwance muzuru yana bin jikinta yana lashewa. Ko motsin kirki ta kasa yi don duk inda ta motsa sai ya yakushi wurin. Yanzu ma cinyarta muzurun ke lasa. Auzubillahi minash shaidanir rajim. Abinda ya fito daga bakinta kenan. Tilly cikin kankanuwar murya tace taimake ni...muzuru ne ya dare kan fuskarta yana lasar mata baki saboda ta motsa bakin.




Batul Mamman💖

Post a Comment (0)