***★BAKIN ARTABU**cigaban
**JARUMA*YAZILA★***
Littafi Na Daya {1}
Na Abdul Aziz Sani Madakin gini..
TYPE Suleiman zidane kd...
Whatsapp 09064179602
*****
Marubucin ya fara da cewa:
====================================
Lokacin da aka kacame da azabebban yaki tsakanin jaruma dabira da jaruma yazila acikin keji sai suka wanzu suna masu kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama. Juriya da jarumtaka tamkar jikinsu bana jini da tsokabane. Sai da suka shafe sa a uku cur suna wannan gumurzu amma dayansu bai sami nasarar koda lakuyar jikin abokin gwaminsa ba. ' Yan kallo kuwa da sarki raihan hankalinsu ya dugunzuma ainun bisa ganin yadda ako yaushe yakin nasu dabira kekara tsamari. Tashin hankalinsu sarki raihan shi ne. Idan jaruma yazila ta sami nasarar hallaka dabira sunyi asarar sarkin yakinsu wacce babu kamarta aduk fadin mayakan birnin. Lokacin da sa a uku ta cika sai dabira da yazila suka tsaya da yakin suka jada baya suka yi cirko cirko suna haki da kallon juna kamar zakaru saboda gajiya.
A sannan ne dabira ta fara tunanin hanyar dazatabi ta sami nasarar akan yazila amma kuma bisa mamaki sai taji zuciyarta na bugawa da karfi a duk sa adda ta kalli fuskar yazila.
Abu na biyu daya fado mata arai shi ne batun wannan laya dake wuyan yazila anya kuwa wannan laya dake wuyan yazila ba ita ce tasa nakasa samun nasara akantaba ? Yazama wajibi agareni na cire wannan laya daga wuyan yazila tunda dai tace daga hannun musulmi take.
Koda gama aiyana haka acikin zuciyarta sai tayi jifa da takobinta gefe daya ta dubi yazila tace , ” tunda dai munkasa yiwa junanmu illa da makami saimu gwada yar kashi domin mu kawo karshen wannan gabatamu ”.
Koda jin haka sai jaruma yazila ta bushe da dariyar mugunta irinta ma abota shirka sannan ta murkushe fuska kuma itama tayi wurgi da takobin tace. ” Ai dama haka nakeso. Domin ta haka ne kadai zamu iya bambancewa tsakanin aya da tsakuwa ” ™Nasiru Muhammad™
Nan take duk su biyun suka dunkule hannayensu suka gyara tsayawa sannan suka fara zagaya juna. Kwatsam ! Sai suka kacame da azababban fada suka rinka kaiwa juna naushi da bugu. Hannu da kafa.
Babu abinda zai baiwa mutane mamaki face yadda suke bugun jikinsu tamkar suna bugun buhun hatsi. Ma ana ko gezau basayi. Sai dai kaga sun shanye dukan sun maida martani.
Aikuwa kafin an juma sun hadawa junansu jini da majina. Ana cikin haka ne suka jada baya alokacin guda suka bayar da tazarar taku shida shida sannan suka rugo da gudu kowacce ta daka tsalle sama. Suna haduwa sai kowacce ta gabzawa yar uwar mummunan naushi a kumatu tun a saman feshin jini yai fitsar burgu daga cikin yanayi mai kama da suma
Suma.
Al amarin daya sa gaba dayan mutanen dake fadar suka mike tsaye zumbur cikin firgici domin a zatonsu jaruman biyu sunyi ragas babu wanda hankalinsa yatafi na kowa dugunzuma face sarki raihan domin yana mikewa tsaye a dimauce bai san sa adda maya ruga da gudu izuwa bakin kejin dasu jaruma dabira keciba. Al amarin humaira kuwa dama bata fito ba zata iya kallon wannan gumurzu da za ayi ba tsakanin yazila da dabira.
Lokacin da gari ya waye taji gaba dayan gidan sarautar tayi tsit tamkar babu mai rai acikinsa sai ta gane cewa lallai kowa na can fada ana kallon wannan fada daza ayi. Dama tun a daren jiya tsakanin yarta dabira da tsohuwar abokiyar gabarta tazila wanda tazo musu a siffar tsoho kasim. Bayan humaira ta gama dan kintse kintsenta saita mike tsam ta fito daga cikin turakarta ta kamaa tafiya acikin harabar gidan sarauta inda ta rinka arba da dai daikun dakaru masu tsaro da bayi masu kai kawokai tsaye humaira tawuce izuwa dakin da aka sayki bako ™Nasiru Muhammad™kasim duk inda ta wuce sai aka ga dakaru da bayi suna rissinawa suna gaisheta har ta isa kofar dakin da zuwa ta iske kofar dakin a bude batayi mamaki ganin hakan ba saboda dama tasan yanzu ankama yazila an tafi da ita.
Duk da cewa humaira taga fuskar jaruma yazila ajiya da daddare amma har ayanzu zuciyarta na wasi wasi akan anya kuwa yazila yarta ce?
Zuciyar humaira na bugawa da karfi ta kunna kai izuwa cikin dakin ai kuwa tana shiga tayi arba da jakar guzurin yazila wacce ke rataye ajikin bango. Kawai sai ta dauko jakar ta sauketa akas ta bude.
Nan take idanunta suka yi arba da wadansu surutu wadanda dabira tanada irin su sak. Sannan kuma taga rigar da aka sawa yazila a ranar da aka haifeta wacce dabira ma tanada irinta.
Koda ganin wadnnan tufafi sai humaira ta dubesu ta rungumeshi a kirjinta sannan ta fashe da matsanancin kuka domin a yanzu ta tabbata da cewa lallai yazila yarta ce kuma yar uwar dabira. Tana cikin wani hali ne ta tuno da cewa yanzu haka fa yazila da dabira na can fada suna yaki kuma za su iya kashe junansu.
A firgice humaira ta mike tsaye ta juya da baya a guje ta rungume da wannan tufafi ta nufi filin fada. * * *
Lokacin da yazila da dabira suka baje akas cikin mawuyacin hali. Sarki raihan ya rugo da gudu izuwa bakin kejin yana isowa sai yai turjiya bisa ganin abin daya faru.
Bawani abu bane yafaru ba face tashin yazila da dabira atare lokaci guda kamar wadanda suka farfado daga dogon suma.
A tare yazila da dabira suka mike tsaye. Kowacce ta sake dunkule hannayenta kuma suka goge jinin dake yoyo abakinsu. Kawai sai yazila ta kurawa hular karfen dake kan dabira idanu. Itakuma ta kurawa layar wuyanta ido take suka sake rugowa da gudu batare da sunyi ™Nasiru Muhammad™ yunkuri daka tsalle samaba.
Cikin bakin zafin nama dabira ta kaiwa layar yazila cafka tayi saar damketa kuwa itama yazila saitayi sa'ar damkar hular karfen dabira
. Alokaci guda kowacce ta cire abinda ta damka. Wato yazila tasami nasarar cire hular karfen dake kan dabira. Sai ga kyakkyawar fuskarta ta baiyana a fili dogon gashin kanta mai haske da kyalkyali ya zuba har kasan kwankwasonta.
Dabira kuwa sai tasami nasarar cire layar dake wuyan yazila tayi wurgi da ita. Atare duk su biyun suka naushi juna da kafa a kirji kowacce tayi baya taga taga kamar zasu fadi kasa. Amma sai suka cije.
Adai dai wannan lokaci ne sarki raihan da sauran gaba dayan jama'ar dake fadar suka kame kamar gumaka saboda tsananin mamaki bisa ganin yadda kamannin yazila da dabira suka zo iri daya sak tamkar an tsaga kara yazila da dabira suka kurawa juna idanu kowacce jikinta na tsuma cikin mamaki.
Bisa mamaki kuma sai kowacce ta sunkuya ta dauki takobi suka ruga ga juna suna ihu irin na manyan sadaukai domin su sake kaurewa da sabon yaki. Lokaci guda suka sake tsayawa suka waigo baya sakamakon jiyo muryar humaira wacce ta taho da gudu tana daka musu tsawa bisa umarnin su dakata da wannan yaki. Ai kuwa sai suka kame suka kura mata ido. Da isowar humaira sai tayi sauri ta bude kofar kejin dasu yazila ke ciki ta kamo yazila da dabira ta rungumesu atare ta fashe da matsanancin kuka
Gaba dayan jama ar dake wajen sai suka rude da kabbara ™Nasiru Muhammad™
Cikin yanayin rashin fahinta dabira ta janye jikinta daga cikin na humaira ta dubeta tace. ” Yake ummina yanzu kina nufin kice yazila ce yar uwatace da nadade ina son na gani ? ” Humaira ta gyada kai tace. ” Kwarai kuma ga cikkakkiyar shaida ”. Nan take humaira ta tunawa dabira wannan riga ta tarihi tace, "kin shaida wannan riga kuwa ? Irin taki ce da kike ta ajiyarta.
Ki gafarceni yake 'yata hakiki na boye miki wani babban sirri na dangane da asalinki da kuma tarihin tawa rayuwar. "
Koda humaira ta zo nan azancenta sai hawaye ya zubowa dabira ta dubi yazila tace, "ke kuwa me yasa kika boye kamanninki agareni ? Yanzu ashe ke jini nace amma ban saniba, yanzu inda da tsautsayi da shikenan sai dayammu ya kashe daya".
Yayinda yazila taji wannan batu sai itama zuciyarta ta karaya, hawaye ya zubo mata. Kawai sai ta bude hannayenta biyu tana mai fuskantar Dabira.
Nan take Dabira ta fada kan kirjinta suka rungume juna kuma suka fashe da kuka a lokaci guda suna dada kankame junansu.
A wannan lokaci gaba dayan jama'ar dake fadar suka cika da tsananin mamaki bisa ganin yadda Jaruma Dabira ta rungume babbar abokiyar gabarta.
Bayan dabira da yazila sun dan jima a rungume da juna kuma fadar tayi tsit kamar babu mai rai acikinta, sai yazila ta janye jikinta daga jikin Dabira ta dubeta cikin murmushi tace, "yake 'yar uwata kiyi sani cewa tun daga ranar da nazo garin nan naku naga irin yanayin rayuwarku naga ya banbanta da irin tamu ainun akan adalci,karamci da zaman lafiya, sai naji nakamu da sha'awar wannan addini naku Ina son yanzu take ki shigar dani wannan addininaku. Ina son yanzu take kishigar dani cikin addinin".
Koda jin haka sai Dabira ta cika da tsananin farin ciki batare da bata lokaci ba Dabira ta biyawa yazila kalmar shahada ta maimaita.
Koda sauran jama'a suka ji YaZILA tayi kalmar SHAHADA, sai suka rude da kabbara. Shi kansa sarki Raihan bai san sa'adda yakama murmushi ba saboda farin ciki.
Nan take sarki RAIHAN maya shiga cikin kejin ya kamo hannun DABIRA da YAZILA yajasu suka tafi izuwa cikin gidan sarauta, HUMAIRA nabiye dasu.
A sannanne fadar ta watse kowa ya kama gabansa kai tsaye sarki raihan, humaira, yazila da dabira suka wuce har izuwa turakar sarki raihan suka zauna.
Zamansu keda wuya sai wadansu likitoci mata guda biyu suka hau duba Yazila da Dabira suka samusu magani a fuskokinsu inda jini yafito. ™Nasiru Muhammad™
Bayan sun kammala aikinsu na likitoci sun fita sai Sarki Raihan ya dubi Yazila da Dabira cikin murmushi yace, "ya ku wadannan zaratan jarumai kusani yau ni da mahaifiyarku muna cikin matukar farin ciki bisa ganin yadda allah ya hadaku har kuka gane juna.
Tabbas shigowar yazila izuwa cikin addinin allah cigaba ne babba a garemu. Yanzu dai kafin na yiwa yazila bayanin halin da muke ciki ke humaira sai ki basu tarihin rayuwarki da yadda yazila da Dabira suka rabu tun suna jarirai, har izuwa lokacin da kika gudo izuwa nan kofar birninmu tare da mijinki aka kashe shi a gaban idanunki".
Batare da bata lokaciba Humaira ta kwashe dukkan labarinta ta zaiyane wasu yazila.
Ai kuwa tana gama bayar da labarin, Yazila da Dabira suka fashe da matsanaicin kuka saboda bakin ciki kuma suka harzuka ainun.
Cikin tsananin fusata Yazila ta mike tsaye ta dubi Dabira tace , "yake 'yar uwata kizo mu tafi izuwa birnin kisra yanzu domin mu dauki fansa akan sarkin kisra da sarkin yakinsa. "
Koda jin wannan batu sai dabira ta kama kafadun yazila tace, "yake 'yar uwata kiyi sani cewa zuwa da shiri yafi zuwa da wuri.
Ina tabbatar miki da cewa ahalin yanzu wadannan abokan gabar tamu ba a zaune suke ba, harma sunyi gagarumin shirin yaki sun taho nan garin domin su baje wannan birnin namu. Labari ya riskemu....."
Kafin dabira ta gama fadin abinda ke bakinta sai sarki Raihan ya tari numfashinta yace, "yake Dabira ai wannan jawabi bana bane, nawane".
Dabira tayi murmushi tace, "ka gafarceni yakai abbana hakika na wuce gona da iri".
Shima sarki Raihan sai yayi murmushi sannan ya dubi yazila yace, "yake 'yar uwar Dabira kiyi sani cewa a halin yanzu a ko yaushe abokan gaba zasu iya baiyana a kofar birninmu kuma labari ya riskemu cewa sun zo da mayaka masu tsananin yawa da ya wuce misali domin har gudummawar mayaka suka samu daga sauran kasashen makwabtaka.
Tabbas yanzu bamu da wani zabi wanda yafi mufita mutari abokan gabar nan tun gabannin su iso".
Koda sarki raihan yazo nan azancensa sai yazila ta dubi Dabira tace, "yake 'yar uwata kisani cewa nice sarkin yakin birninmu kamar yadda kike sarkin yakin nan birnin, saboda haka nasan dukkan sirrin mayakanmu da irin yanayin yakinsa, lallai zan bayar da gagarumar gudummawa a wannan yaki daza ayi kuma na tabbatar da cewa ba karamar barna zan yiwa su sarki Daksur ba.
Babban burina shine, na kashe sarkin yaki da sarki Daksur da hannuna".
Koda jin haka sai Dabira tayi murmushi tace, "ni kaina burina kenan domin dole ne mu dauki fansa akansu bisa bakin cikin da suka jefa mahaifiyarmu a ciki.
Ya ke 'yar uwata tunda dai yanzu allah yasa kin karbi addinin musulunci na san cewa zuciyarki zata sake kekashewa ga barin tsoro kuma zaki sami kwarin gwuiwa fiye da da can, saboda haka ina ganin idan muka hada karfi da karfe ni dake a wannan yaki zamu iya samun nasara akan abokan gaba ".
Kafin yazila ta budi baki tace wani abu sai sarki Raihan ya tari numfashin Dabira yace, "ba haka bane yake 'yata,ke dai kawai munemi taimakon allah, amma ai karfinmu ko dabarar mu baza su sa musami nasara ba akan makiya ba domin na tabbatar da cewa suma baza su fito ba kai tsaye sai da kyakykyawan shiri irin wanda basu taba yin kamar saba.
Yanzu abin da nake so dake yake Dabira ki tafi tare da 'yan uwarki yazila ki tara dukkan mayakan kasar nan ku fara shirye shiryen dabaru na yaki wanda yakamata kuyi, nima yanzu zan je na tara dukkan 'yan majalisata domin mutattauna akan wannan yaki, amma dai kusani nine wanda zan jagoranci wannan yaki inyaso kubiyu kurufa min baya idan allah yasa narayu abayan wannan yaki ™Nasiru Muhammad™ kuma nasami nasara za a daura aurena da mahaifiyarku domin mun daidaita junanmu".
Sa'adda sarki raihan yazo nan a jawabinsa sai yazila da dabira suka kamu da tsananin farin ciki basu san sa'adda suka rungume sarki ba a tare lokaci guda suka sumbaci goshinsa.
Batare da bata lokaci ba Yazila da Dabira suka fice daga cikin dakin da sauri suka nufi wani bangare daban na gidan sarauta inda suka iske wani barde a tsaye cikin shigar yaki.
Dabira ta dubi Barden tace, "ma za ka busa kahon tara mayaka domin yanzu nake son mu shirya yadda zamu bullowa wannan yaki". Koda jin haka sai barden yacika Umarni.
Ai kuwa nan take dakaru suka dinga tuttudowa daga wajen gidan sarauta suna rugawa izuwa filin fada suna taruwa da jeruwa a sahu-sahu.
Wannan shine abin yafaru abirnin misra bayan jaruma yazila taga mahaifiyarta da 'yar uwarta Dabira kuma ta karbi addinin musulunci.
*** ***
A can birnin kisra, bayan sarkin yaki da sarki Daksur sun yi bincike a cikin halwar tsafi sun ga duk abinda ya faru ga jaruma yazila wadda ta bijire musu kuma tazama babbar abokiyar gabarsu sai hankalinsu ya duguntsuma ainun domin sun tabbatar da cewa aikin dake gabansu ba kadan bane.
Bisa wannan dalili ne sarki daksur yasa aka shiga sauran kasashen kafirai dake makwabtaka don neman gudummawar Dakarun yaki. Duk sarkin da wasikar ta iskeshi sai yaba da hadin kai ya aiko da dakarun masu yawa da makamai da kuma isasshen guzuri.
A yamma da birnin kisra akwai wata babbar kasa mai suna tashwar.
Birnin tashwar na karkashin mulkin wani sadaukin saurayi ne, kyakykyawan gaske mai tarin arziki da karfin mulki.
Wani iko na allah shi dai wannan sarki baya tsafi kuma ™Nasiru Muhammad™tsafi baya tasiri akansa. Bisa wannan daliline gaba dayan sarakunan dake mulki a nahiyar suke shakkarsa domin ba a taba kai masa hari ba ko wargi.
Shi dai wannan sarki ana kiransa da suna Uhaisu bn kairuf. Sarki uhaisu yana da matukar karfin damtse na allah ya isa, domin komai girman giwa idan yayi mata naushi daya sai ta fadi kasa idan zai jarraba karfinsa ya kansa karti dari su rufar masa shi kadai, sai dai kaga ya bazarda su gaba dayansu sun baje a kasa suna yoyon jini a hanci da baki. Idan kuwa ya naushi mutun iya karfinsa tofa ko kashin karfe gareshi sai ya karye.
Sarki uhaisu bashi da wani addini don haka bai matsawa kowa ba a kasarsa duk addinin da mutun yaga dama yana da ikon yinsa. Wannan ya samo asali ne tun daga iyayensa da kakanninsa, haka ya taso ya samesu, basa addini kuma basa hanawa ayi.
Akwai wata rana sa'adda mahaifin sarki uhaisu ke kan gangarar mutuwa wato yana kwance acikin jinyar cutar ajali awannan yammaci da suka ka daita su biyu kacal a cikin turakar sarki sai uhaisu ya dubi sarki yayin da hawaye ya zubo masa yace, "ya kai abbana ina son nayi maka wadansu tambayoyi guda biyu wadanda suka dade suna yawo acikin zuciyata"
Koda jin wannan batu sai mahaifin nasa ya kamo hannunsa ya dorasu akan kirjinsa kuma ya kura masa idanu alokacin da shima idanunsa suka ciko da kwalla sannan ya budi baki da kyar yace, "ya kai dana na san tambayoyinka dake ranka kuma na dade ina jiran ranar dazaka gabatar dasu agareni.
Tabbas yanzu ne lokacin daya dace kayi mini wadannan tambayoyi domin tun kana karami na boye amsarsu, kuma gashi harka girma kakai munzalin dazaka gajeni amma baka san amsar tambayoyin ba wadannan suke faman damunka acikin zuciya.
TAMBAYARKA TA FARKO AKAN ADDINI CE. Kana so kasan dalilin dayasa bamu da addini? Tambayarka ta biyu kuwa itace kana so ka san dalilin da yasa naki yin aure, kuma kaima ban taba nuna maka ina da ra'ayin kayi aure ba? Kasaurara da kyau kaji amsar wadannan tambayoyi naka kuma kayi amfani da basirarka wajen amfani dasu domin idan baka nutsuba har abada bazaka sami daraja da daukaka ba irin wadanda na samu a rayuwata.
Dalilin dayasa bamu da addini shine, mahaifina kafin yarasu nayi masa irin wannan tambaya, domin yadda ka taso babu addini. Kuma babu aure haka nataso amsar da yabani itace.
"Ya kai dana kayi tunani yanzu addinai sun yi yawa a cikin wannan duniya, akwai masu bautar rana, wata, ruwa, wuta, gumaka, dabbobi da sauransu. Kai wasu ma aljanu suke bautawa. Mahaifina yaga yamin cewa addini guda daya ne, kuma ubangiji daya ne wanda shine na gaskiya mai ikon komai da kowa.
A wannan zamani babu wannan addini kuma kaima zaka riski wannan addininne a karshen rayuwarka, abu ne mawuyaci kasan wannan addini amma wata kila in ka sami haihuwa danka yasan wannan addini.
To ka gaya masa cewa duk ranar da wani gagarumin yaki ya taso ya halarceshi domin a wannan tafarki ne zai san wannan addini na gaskiya har ya fahimceshi kuma ya aminta da shi "
Sa'adda mahaifina yazo nan azancensa sai na cika da mamaki na dubeshi nace, "ya kai abbana ashe baka gaya min cewa yaki ba zai taba zuwa birnin tashwar ba? Ya kuma yanzu kake mini batun yaki ?"™Nasiru Muhammad™
Koda jin haka sai mahaifina yaja numfashi tamkar ransa zai fita, a sannan yace, "bana nufin yaki zai zo har nan ya riskeka, ina nufin za'a aikomaka da sakon gayyata. Lallai ka amsa gayyatar, amma kafita yakin kai kadai, kada ka kuskura ta tafi da kowa idan har kana son kasan addinin gaskiya.
Dangane da tambaya ta biyu dake ranka kuwa ba wani abubane face batun aure. Tun da mahaifiyarka ta rasu ban sake yunkurin aureba.
Haka mahaifina ya kasance, shima mahaifina haka rayuwarrsa ta wanzu har izuwa kan kakanmu na arba'in da daya.
Abinda nake nufi anan shine duk wanda yai aure acikinmu haihuwa daya yake samu kuma sai matarsa ta mutu, shima sai yamutu yabar abinda ya haifa.
Lokacinda aka haifeka sai naji babu abinda nake so a duniya sama da kai, kuma naji ina son kayi nisan kwana a duniya.
A cikin gidan sarautar nan akwai wani daki guda daya wanda ba'a shigarshi kuma kai ma baka taba ganin an shigeshi ba, haka ne?"
Kodajin wannan tambaya sai na jinjina kaina nace, tabbas na san da wannan daki kuma na dade ina mamaki da tunani akansa."
Mahaifina ya sake ajiyar zuciya yace, "Akwai wani aljani bawanmu a cikin wannan daki wanda bama bauta masa shima kuma baya bauta mana, amma zaman amana ne da kauna tsakanin zuri'armu da tasa. Duk abinda zai samemu a rayuwa shi wannan aljani ne ke sanar damu.
Zidane kd.
Marubucin ya cigaba da cewa:
==============================
=============================
A iya tsawon rayuwata ta duniya sau daya na taba. Ganawa da wannan aljani kuma shine ya gaya mini cewa kada na kuskura na kara yin aure a rayuwata. Idan kuwa nayi sai an kawo harin yaki izuwa kasata an kawar dani. Yakai dana kaima kayi amfani da wannan nasiha wacce wannan aljani yayi mini kuma kada ka kuskura ka shiga dakin da wannan aljani yake domin ku gana sai ranar daza ka fita wannan gagarumin yaki da aka gaiyaceka. "
Har kullum sarki Uhaisu baya mancewa da wannan jawabi na mahaifinsa don haka sai ya hakura da batun aure gaba daya a rayuwarsa saboda yana son yayi nisan kwana a cikin daular mulki daya tsinci kansa a ciki.
A ranar da wasikar gaiyata izuwa yaki ta riski sarki Uhaisu daga birnin kisra sai yacika da tsananin farin ciki domin yasan cewa lokacine yazo da zai cika babban burinsa na duniya domin yasan mahaifinsa ya gaya masa cewa bayan anyi wannan gagarumin yakinne zai iyayin aure har ya sami magaji kuma lallai zai yi tsawon rai a duniya.
Lokacin da maga-takarda ya gama karanta wasikar gayyata a fadar sarki Uhaisu fadawansa suka ga ya cika da farin ciki sai mamaki ya kamasu domin su a saninsu babu sarki ya tsana sama da yaki kuma babu abinda yafi so sama da zaman lafiya. ™Nasiru Muhammad™
Sarki Uhaisu ya kasance mutum mai adalci, tausayi da jin kai, gashi da karrama mutane, wato bai iya wulakanci ba bashi da izza da jin kai irin na sarakai, duk da cewa allah ya bashi karfi, kyawu da dukiya mai yawan gaske.
Bisa wannan baiwa da allah ya baiwa sarki Uhaisune ya zama cewa 'yan mata, 'ya'yan sarakai, attajirai da manyann matsafa suka kamu da tsananin kaunarsa, wasu da yawansu a dalilin kamuwa da sonsa ne ma suka kamu da cututtuka saboda rashin samun kaunarsa. Wasu ma sanadin ajalinsu kenan.
A duk sa'adda sarki uhaisu ya ci ado kuma yayi hawa ya fito daga cikin gidansa sai dai kaga mata suna fitowa da gudu domin kawai su ganshi. Idan dakaru suna hanasu zuwa kusa dashi sai kaga suna kuka kamar wadanda akayiwa mutuwa.
Duk wacce ta sami nasarar koda taba dikin sa ma kuwa sai kaga sauran mata na rungumeta don su sami albarkaci. Idan kuwa maca tasami nasarar koda taba hannun sarki Uhaisu ne sai dai kaga ta yanke jiki ta fadi sumammiya saboda tsananin farin ciki.
Daga wannan rana kuwa mata sun dinga kai mata ziyara kenan suna bata kyaututtuka ba adadi.
Hakika a tarihin nashiyar kasar tashawar ba a taba samun saurayi mai farin jini ba a wajen mata kamar sarki Uhaisu, kuma labarinsa ya bazu ko ina, har zuwa ake yi daga kasashe daban-daban domin kawai aganshi.
Tabbas duk mutumin da yake shakka akansa da zarar yazo ya ganshi dole yake gasgatawa. Komai hassadar mutun da kushensa idan yayi arba da sarki Uhaisu take yake sallamawa.
Sukansu maroka idan sarki Uhaisu ya fito suka fara yi masa kirari sai masu rasa irin kalmomin dazasu rinka fada wadanda suka dace da shi akwai wani maroki wanda yafi kowa iya kodashi, shine ya kance dashi:
Kaico! Ina gwanin wani ganawa? Ga saurayi uban samari tauraron kyawawa mai magance yunwa da kishirwar yan mata. ™Nasiru Muhammad™
Gaka jarumi. Sarki sadauki mai ragargazar maza yau fa ga mai tekun zinare mai shanye kogunan attajirai. Ga ruwan sanyi mai sanyaya zuciya talakawa kufara nan ga bargon kankara mai kashe gobara daga kogi. Marhaban da babbar gona nomanta sai shekara dubu ! Aduk sa adda marokin ya haukace ya kama sambatu saboda sai da dinare ya rufeshi ruf tamkar an nutsar da shi a cikin yashi tun yana kirari. Ya koma yin waka sannan ya fashe da kuka ya dinga mari da cizon kansa har sai da aka tattarashi shi da dukiyar daya samu aka kaisu gidansa lokacin da sarki uhaisu yaga fadawansa sun cikada mamaki bisa ganin yadda ya kamu da farin ciki don jin sakon gaiyata izuwa yaki. Kuma ya fahim cewa hankalinsu ya dugunzuma ainun sai ya dubesu yayi murmushi sannan yace. ” Yaku yan majalista ku kwantar da hankalinku. Ku sani cewa wannan yaki bai shafi kowa ba awannan kasa tawa face nikadai. Don haka nikadai zan shirya na tafi wannan yaki. ”
Koda jin wannan batu sai mamaki da fargaba suka dada kama yan majalistar wazirin sarki uhaisu wanda ake mazwan ya dubishi cikin tsananin damuwa yace. ” Haba ya shugaban kasani cewa mu da sauran talakawanka muna. Matukar kaunarka kuma tunda ka hau kan karagar mulki bamu taba rabuwa da kaiba dai-dai da rana daya.
Mun tabbatar da cewa idan babu kai babu wanda zai iya yi mana mulki acikin adalci irin naka. Tayaya kake tsammanin zamu iya barinka ka tafi yaki kai kadai ? Katuna fa cewa baka da mai gadonka bare idan muka rasaka musami halifanka?"
Lokacin da waziri yazo nan a jawabinsa sai sarki Uhaisu ya mike daga kan karagarsa yayi tafiya izuwa tsakiyar fadar sannan ya tsaya ya dubi jama'a gabas da yamma, kudu da arewa, kawai sai hawaye ya zubomasa ya ce, "ya ku jama'ar birnin tashwar kuyi sani cewa a iya rayuwata ta duniya babu abinda nake kishinsa kuma ™Nasiru Muhammad™ nake matukar kaunarsa sama da birnina da jama'ata.
Yau shekara a shirin da takwas a duniya amma ban taba zuwa yakiba.
Duk wannan daukaka da ni'ima wacce nake da ita a duniya bata gani ba sai jitake yi kawai.
Yau gashi dama tazo wacce za a sanni. Bugu da kari. Ina mai sanar daku cewa wannan yaki da zan fita ne zan cika babban burina na duniya harna sami damar aure na sami wanda zai gajeni yaci gaba da yi muku irin mulkin da nake muku bayan babuni. "
Koda sarki UHAISU yazo nan a zancensa sai fadar gaba daya ta rude da shewa, mutane suka cika da farin ciki asannanne sarki Uhaisu ya sallami kowa fadar ta watse nan labari ya bazu ko ina a kasar cewa gobe sarki Uhaisu zai fita yaki shi kadai kuma ga sakamakon da zai biyo baya idan ya fita yakin.
Nan fa jama'a suka yi farin ciki da bakin ciki ba face rabuwar daza a yi da sarki izuwa tsawon kwanaki ko watanni ba a san ranar da wowarsa ba. Haka kuma ba a san irin hadarin da sarki zai gamu da shiba akan hanyarsa, babu tabbacin zai iya tsira da rayuwar sa duk da an san irin gagarumar jarumtakarsa amma kuma ai ba a taba ganin kwazonsaba a filin yaki ba.
Dayawa daga cikin jama'ar gari kuwa basu yi bacciba a wannan dare, musamman mata. Duk gidan da kaje sai kaga ana koke-koke tamkar mutuwa akayi.
Yayin da dare ya raba sai sarki Uhaisu ya shiga cikin wannan daki na musamman wanda tunda aka haifeshi bai taba shiga ba.
Kofar dakin a lullube take da yana gaba dayanta alamar cewa an dade ba'a shigaba tsawon shekara da shekaru.
Batare da fargabar komai ba sarki Uhaisu yasa kwagirin sarauta ya share wannan yana sannan yasa daya hannun nasa ya murza marikin kofar dakin nan take kofar ta bude ya kunna kai ciki.™Nasiru Muhammad™
Da shigarsa sai ya ga dakin faba daya a haskake yake da wani irin haske na musamman wanda bai taba ganin irin saba kuma yarasa daga ina hasken yafito. Babu komai acikin dakin face wata farar kujerar karfe guda daya jal a ajiye agefe daya. Sai sarki uhairu ya dubi gabas da yamma. Kudu da arewa na dakin. Amma bai gawata halita nai rai acikiba. Kawai saiya ya juya da baya domin ya fiche daga cikin dakin. Har ya iso bakin kofa yasa kafarsa guda a waje sai yaji an kira sunansa da wata murya wacce tabbas ya taba jin muryar amma sai yakasa tuno mai muryar cikin hanzari da mamaki uhairu ya waigo. Kawai sai yayi arba da wani tsohon aljani. Siriri mai dogon fuska gashin kansa da gemunsa fari ne fat kai da gani kasan cewa yadade aduniya. Aljanin na zaune akan wannan farar kujera fuskarsa cike da annuri. Kallo daya mutun zai yiwa aljanin ya tabbata da cewa yana cikin koshin lafiya domin akwai alamun kuzari a tare da shi babu wata nakasa mai nuna alamu tawaya ko gazawa bisa dalilin tsufa. Aljanin ya sake kiran sunansarki uhaisu akaro na biyu yace. ” Haba dan uwana ya zaka juya ka fito ko gaisawa bamu yiba alhalin yau ne ranar farko da zamu fara ganawa ”. Koda jin haka sai sarki uhaisu ya mai dawa aljanin martanin murmushi yataho gareshi cikin sanyin jiki. Da isowar uhaisu daf da aljanin sai ya mike tsaye cikin girmamawa yayi masa nuni da kujerar da yake zaune akai yace dashi ya zauna. Uhaisu ya dubi aljanin cikin mamki yace. ” Saboda meza kace na zauna akan kujerarka wacce kasaba zama a kanta tun kafin a haifi kakan kakana ? ”. Da jin wannan batu sai kwallah ta ciko a idanun aljanin sannan yace. ” Yakai uhaisu ka sani cewa kaine sarki na arba in da biyar daga cikin sarakan da suka yi sarauta a gidannan kuma kowanne sarki yayi zamaninsa tare dani. Amma gaba ™Nasiru Muhammad™dayansu babu wanda ya shigo cikin dakin nan ya mai da mini da martanin murmushi sai kai kadai.
Kai ne kadai sarkin daya shi shigo wajena cikin kwanciyar hankali da saukin kai bada jin tsoro ko izza ba. Turbude fuska kamar wanda aka aikawa da sakon mutuwa yace. ” Bani ne zan sanar da kai wanna addini ba kai da kanka zaka ganeshi zuciyarsaka ta gamsu da shi “. Koda gama fadin haka sai aljani aznaihul markas ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a cikin dakin muryarsa na cewa sai mun sake saduwa idan har ka dawo gida a raye cikin nasara. ”Nan take sarki uhaisu ya fice daga cikin dakin ya janyo kofar ya rufeta. Aikuwa yana rufe kofar sai yaga yana ta sake lullubeta tamkar ba a taba bude kofar ba. Nan dai sarki uhaisu ya tafi izuwa turakarsa zuciyasra cike da sake sake da zullumi abinda ya fara yawo a ransa shine. Bayanin karshe da aljani aznaihul markas yayi masa cewa sai sun sake saduwa idan ya dawo a raye kuma cikin nasara. "
Shin wannan batu yana nufin kenan babu tabbacin zai tsira da rayuwarsa ? Kuma babu tabbacin zai sami nasara acikin burinsa na duniya?"
Nan take hankalin Uhaisu ya dugunzuma. Ya rasa abin da ke masa dadi aduniya, amma da yatuna matsoraci bashi zama gwani, kuma ya tuna shima jarumine sadauki mai tarwatsa maza, sai yaji dukkan tsoro ya kau daga zuciyarsa.
Haka dai sarki uhaisu ya isa cikin turakartsa ya kwanta. Kwanciyarsa keda wuya sai barci ya saceshi domin shidai a rayuwarsa bakin ko kishiyarsa, tunani ko ™Nasiru Muhammad™fargaba basu taba hanashi yin barciba domin ya kasance mutum wanda bai taba sa wani abu a ransa ya dame shiba.
Kashegari kuwa tun da dukudukun safiya sarki Uhaisu ya tashi ya kintsa aka kawo masa wani farin ingarman doki gami da isasshen guzuri. A wannan lokaci sarki uhaisu yayi gagarumar shigar yaki, kuma yasa hular karfe wacce ta rufe fuskarsa idanunsa kadai ake ake gani.
A lokacin ne gaba dayan fadawansa da jama'ar gari suka taru a fadar don yin bankwana da shi. Fadar tacika ta batse babu masakar tsinke duk inda mutun ya duba fuskarsa maza da mata daga masu kwalla sai masu zubar da hawaye saboda alhinin rabuwa da sarkinsu uhaisu.
Yayinda sarki uhaisu yaga jama'arsa acikin wannan hali sai ya kamu da tsananin tausayinsu yaji kamar ya fasa yin wannan tafiya amma daya tuna cewa wannan tafiya itace fa cikar burinsa na duniya sai yaji bazai iya fasa taba.
Nan take sarki uhaisu ya cire hular karfen kansa sannan ya hau kan mumbari dake tsakiyar fadar ya fuskanci jama-arsa ya shiga jawabi na rarrashi gami da ban baki, kuma yanuna musu mushimmancin wannan tafiya da zai yi cewar a dalilinta ne zai samu tsawon rai kuma birninsa zai samu daukaka irin wacce bai taba samuba.
Duk da jin wannan bushara sai jama'a suka ji sudai basa son su rabu da sarki Uhaisu domin ji suke kamar zasu rabu da hanyar kirjinsu.
Lokacin da sarki Uhaisu ya gama jawabinsa ya sauko daga kan mumbari ya hau kan dokinsa ya sanya wannan hular karfe. Koda ya kada linzamin dokinsa ya nufi kofar fita daga fadar sai jama'a suka rude da ihu, kuka da dimauta mata kuwa da yawansu yanke jiki suka rinka yi suna faduwa kasa sumammu saboda bakin cikin rabuwa da masoyinsu wanda suka dade suna begensa a cikin zuciyarsu.
Hakika sarki uhaisu ya cika tauraron samari, maganin ™Nasiru Muhammad™ yunwa da kishirruwar 'yam mata, domin babu wata 'ya mace a cikin birninsa wadda bata kamu da sonsaba face matan aure da tsofaffi. Kai wadansu matan auren ma idan sarki Uhaisu zai auresu zasu iya kashe aurensu haka dai sarki Uhaisu yacigaba da tafiya babu waiwaye, kuma babu sassauci har ya fice gaba daya daga cikin birninsa. Sai da ya kwana ashirin ba daya yana keta dazuzzuka da birane sannan ya isa birnin kisra.
Kafin ya iso birnin kisra yayi arangama da 'yan fashi iri-iri da kuma muggan dabbobin daji amma komai yawansu da karfinsu sai ya ga ya tarwatsasu ya kashe na kashewa, masu nisan kwana kuwa saidai su gudu.
Shikansa sarki Uhaisu yayi matukar mamaki bisa ganin irin jarumtakarsa domin bai taba tsintar kansa a cikin irin wannan haliba na yaki a daji da mutane da yawa ko dabbobi.
Lokacin da sarki uhaisu ya iso fadar sarki Daksur sai ya iske fadar a cike makil da manyan baki da sarakai wadanda ke zaune a can saman fadar kusa da karagar sarki Daksur. A kasa kuwa, sauran dakarun yakine masu yawan gaske wadanda suka rako sarakuna don zuwa wannan gagarumin yaki wanda za a yi abirnin Misra.
A wannan lokaci fadar tsit, sarki daksur ne kadai yake bayani ana sauraron muryarsa, kwazam! Sai akaga mutun yashigo fadar bisa kan doki sanye da kayan yaki ya rufe fuskarsa da hular karfe.
Karar kofatun dokin nasa ne tasa sarki Daksur yayi shiru kuma kowa yajuyo yana kallonsa. Mahayin yaci gaba da tafiya kai tsaye ya durfafi inda karagar sarki take batare daya tsaya ya gabatar da kansa ba.
Koda ganin haka sai dakaru sama da dubu suka yunkura zasu afka masa.
Cikin hanzari sarki Daksur ya daka musu tsawa suka tsaya cak! Shima mahayin dokin sai yaja linzamin dokin nasa ya tsaya a waje guda.
Sarki daksur ya mike tsaye ya tako da kafarsa, yazo har gaban mahayin sannan ya risina a gareshi yace, "lale marhaban da sadaukin sadaukai, kuma sarkin sarakuna na wannan nashiya tamu, mai birnin tashwar wato sarki Uhaisu bin kairuf".
Koda akaji sarki Daksur ya ambaci wannan suna sai idanun kowa ya zazzaro aka cika da tsananin mamaki bisa ganin yadda sarki Uhaisu ya iso fadar shi kadai batare da dakarunsa sun rako shiba, sannan kuma sai kowa ya zuba ido domin yaga fuskarsa domin da yawan jama'a basu taba ganinsaba labarinsa kawai suke ji.
Abinda yakara baiwa mutane mamaki shine, yaya aka yi sarki daksur ya gane cewa sarki uhaisune wannan har ya taso ya taryeshi alhalin ba a gabatar da zuwansaba.
Abinda suika manta shine, sarki daksur babban ™Nasiru Muhammad™matsafine.
Nan take sarki uhaisu ya sauko daga kan dokinsa sai sarki daksur ya rungumeshi cikin tsananin farinciki tamkar wanda yaga dan uwansa na jini.
Batare da sarki Uhaisu ya cire hular karfen dake kansa ba sai sarki daksur ya jashi suka tafi izuwa har can inda karagarsa ta mulki take take suka zauna akan karagar mulkin su biyu. Abinda ya daurewa kowa kai kenan, domin babu wani mahaluki wanda sarki Daksur ya taba girmamawa haka ya darajashi sai sarki UHAISU.
Nan take aka kawowa sarki uhaisu abinci da abin sha iri-iri mai daraja irin na sarakai na alfarma wanda babu kamarsa a wajen sarki uhaisu ya saki jikinsa yaci abinci sosai har sai da yaji ya koshi sannan ya dubi sarki Daksur yace, "a kaini masaukina ina da bukatar na kwanta na huta domin na huce gajiyar tafiyar da na sha ".
Batarte da gardamar komai ba kuwa sarki daksur ya kira wani Hadimi yace da shi ya kai sarki uhaisu izuwa masaukinsa, wani wuri wanda shine mafi kyau da tsaruwa a gaba daya gidan sarautar. Nan take kuwa aka tafi da sarki Uhaisu,
A she gaba dayan sarakan dake zaune a cikin fadar ransu ya baci bisa ganin yadda sarki daksur ya tarbi sarki Uhaisu cikin karramawa da girmamawa fiye da yadda aka tarbi kowannesu.
Bayan bacewar sarki uhaisu da hadimin da ya tafi kaishi masaukinsa sai wani sarki mai ji da kansa wanda ya kasance babban abokin sarki daksur wanda ake kira ma aruf bn saurud ya dubi sarki daksur yace "haba abokina ka tuna fa cewa yau kwanamu arba'in anan muna taruwa kullum muna tattaunawa da shiryawa akan yadda zamu bullowa wannan yaki. Yanzu ne muka yanke shawarar mu tafi izuwa yakin amma sai gashi mutum daya yazo ya tsaida komai. Yanzu shikenan sai dai mujira har sai sa'adda yayi barci ya tashi sannan zamu tafi?"
Lokacin da sauran sarakai suka ji wannan batu sai duk ™Nasiru Muhammad™ suka goyi bayan sarki ma'aruf, fadar ta rude da hayaniya.
Shi kuwa sarki Daksur sai ya kama murmushi. Daga can sai ya daga hannu sama akayi tsit sannan yai kyaran murya yace, 'yan uwana ina so ku sani cewa sarki Uhaisu ne zai jagoranci wannan yaki da zamu je kuma dukkan nasararmu na tare da shi, idan muka kuskura muka tafi yakin babu shi tabbas baza sami nasaraba ".
Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke gaba dayan jama'ar dake cikin fadar sarkin yaki ya dubi satki daksur cikin biyayya yace, "haba ya shugabana, yanzu duk yawannan namu amma ka ce ba zamu sami nasara ba face Uhaisu ya jagorancemu? Kai da bakinka kace damu yawanmu ya ninka na abokan gaba sau dari ba. Ai kuwa ina ganin cewa koda Uhaisu ko babu shi dole ne mu sami nasara a wannan yaki. "
Sa'adda sarki daksur yaji wannan batu sai ya mike tsaye ya dubi kowa dake cikin fadar, sannan yayi ajiyar zuciya yace, "yaku 'yan uwa ina so kusani cewa ni nasan abinda babu wanda ya sanshi a cikinku nan gaba daya A halin yanzu sarkin yakimmu ta da, wato JARUMA YAZILA tana can birnin misra kuma ta karbi addininsu, don haka ita da 'yar uwarta JARUMA DABIRA zasu hada KARFI DA KARFE su yakemu.
Tabbbas su biyu kacal sun isa su iya yi mana mummunat barna a wannan yakin, domin a duk fadin wannan nashiya babu wani sadauki ko mayaki wanda wanda ya isa ya taresu face sarki Uhaisu. Ina tabbatar muku da cewa ahalin yanzu babu wani sadauki mai karfin damtse irin na Uhaisu a duk fadin duniyarnan kuma shine mutumin da baya tsafi, kuma tsafi baya tasiri a kansa domin ku gasgata zancena yanzun nan zan nuna muku ku gani da idanunku ".
Koda gama fadin haka sai sarki Daksur yayi nuni da hannunsa izuwa ga saman bangon fadar saiga hoton irin gwagwarmayar da sarki Uhaisu yayi da 'yan fashi da masu yawan gaske wadanda adadinsu ya kai dubu ™Nasiru Muhammad™ ashirin da doriya sun yiwa sarki uhaisu kawanya 'yan fashin sun kasance gabza-gabza masu kirar mutanen farko kuma kowannensu na dauke da muggan makamia lokaci guda suka yiwa sarki uhaisu rubdugu shi kuwa sai ya wanzu yana mai gididdigasu cikin tsananin zafin nama irin wanda ido bai taba ganiba.
Cikin sa'a daya jal ya ragargazasu duka dayansu bai tsira da rayuwarsa ba, sai gashi filin dajin gaba daya ya cika da gawarwakin 'yan fashin, duk inda mutum ya duba sai dai yaga jini na malala da kwaranya tamkar ruwan sama akeyi.
Babban abinda ya baiwa kowa mamaki shine ganin sarki uhaisu a tsaye bisa dokinsa cikin koshin lafiya babu inda jikinsa ya sami rauni koda kwarzanewa kuwa, kai ba ma shiba, hatta dokinsa ma babu abinda ya taba lafiyarsa.
Bayan wannan gwagwarmaya sai kuma aka ga wani azababben yaki da sarki uhaisu yayi da wadansu dodanni wadanda yawansu ya wuce misali domin ninka na wadannan 'yan fashi sau biyar. Sai da sarki Uhaisu ya shafe kwana guda da yini daya yana yaki da dodannin bai gajiba kuma bai guduba sai ragargazarsu kawai yake yi, suna zubewa kasa matattu. Yawan dodannin sai ya zama na banza ya yin da bala'I yakai bala'I da kansu suka rinka guduwa suna neman maboya.
Nan take sarki daksur ya sake nuni da hannunsa izuwa ga bangon fadar hoton komai ya bace. A sannan ne gaba dayan jama'ar dake fadar suka yi ajiyar zuciya a lokaci guda saboda tsananin mamakin ganin irin wannan a zababbiyar jarumtaka ta sarki Uhaisu wacce ko a tarihi basu taba jin taba kuma gashi jarumtaka ce ta zahiri wacce babu sihiri ko tsafi acikinta.
Nan take kowa ya sallama ya gamsu cewa lallai sarki uhaisu nezai jagoranci wannan gagarumin yaki da za a tafi izuwa birnin misra.
Sai da rana ta fadi sannan sarki uhaisu ya farka daga barci domin huce gajiyar shi. A sannan ne kuyangi suka ™Nasiru Muhammad™ kai shi kewaye suka yi masa wanka a cikin bahon zinare mai cike da ruwan kamshi na turaren miski da furanni iri-iri.
Bayan angama yimasa wanka an shafeshi da mai sai aka kawo masa kayan yakinsa ya sake sanya su ya mayar da hular karfensa yasa a kansa sannan ya taho fada yana zuwa cikin fada sai kowa ya mike tsaye don girmamawa, hatta sarki daksur kuwa. Maimakon sarki uhaisu yaje ya zauna sai dubi sarki Daksur yace, "a kawo mini dokina yanzu zamu kama hanya mu durfafi Birnin MISRA.
Batare da gardamar komai ba kuwa sarki Daksur yasa aka kawowa sarki Uhaisu dokinsa ya hau kawai sai ya kada linzamin dokinsa ya juya da baya ya fice daga cikin fadar.
Cikin hanzari sarki Daksur ya bayar da umarni ga dukkan sauran mayaka da a fita ayi hawa abi bayan sarki Uhaisu. Nan da nan kuwa aka bi wannan umarni.
Kaico! Tashin han kali ba a samasa rana.
Inda ace mutun yana wannan wuri idan yaga irin tsananin yawan wadannan mayaka da kuma irin maggan makaman da suka debo dole ne ya firgita domin gani zaiyi kamar zasu iya tashin duniya gaba dayanta a cikin rabin sa'a.
Gaba dayan mayakan da suka fito wannan yakin babu abinda suke son gani face fuskar sarki Uhaisu da kuma irin kirar jikinsa amma sai gashi har yanzu bai cire hular karfen dake kansaba kuma bai kwabe kayan yakin da suka rufe jikinsa ba su kansu kuyangin nan da suka yi masa wanka dukkansu dimaucewa sukai suka fita haiyacinsu saboda ganin irin tsananin kyawun surar da allah ya baiwa sarki Uhaisu.
MENENE ZAI FARU A WANNAN GAGARUMiN YAKI DA ZA A YI A BIRNI MISRA?
WACE CE MATAR DA SARKI UHAISU ZAI AURA? Mu hadu a BAKIN ARTABU na biyu domin jin cigaban wannan kasaitaccen labari.
==============
Domin SAMUN WASU LITTAFAN YAKU YA MANA MAGANA TA WHATSAPP 09064179602