BAƘIN ARTABU 2 COMPLETE

Iᴬᴮᵁᴮᴬᴷᴬᴿ Quyraemey: ***★BAKIN ARTABU**cigaban
**JARUMA*YAZILA★***
Littafi Na Daya {2}
TYPE A
***Nasiru**Muhammad**Tijjani***
Marubucin ya cigaba da cewa:
==============================
=============================
KOFAR birnin misra ta cika ta batse da dakarun yaki, babu masakar tsinke. Amma gaba dayan mayakan adadinsu bai wuce dubu dari uku da ashirinba.
Tsaye a gaban rundunar masu jagorantarsu mutun ukune. Na farko shine sarki Raihan, na biyu kuwa JARUMA YAZILA, sai kuma JARuMA DABIRA.
Yazila da dabira sun yi shigar yaki ne iri daya kuma duk sun sanya kayan karfe, kowannensu ya rufe jikinsa ruf! Baka isa ka gane cewa sun kasance mata ba saboda sun rufe kansu da hular karfe sun boye gashin kansu.
Shikuwa sarki raihan shigar bakin sulke yayi, kuma takalminsa ma bakine na kafa. Hatta kufen takobinsa da garkuwarsa duk bakake ne.
Kwatsam! Sai aka jiyo bugun tambura da ganguna yana tashi daga sama. Nan da nan sautin ya cika dodon kunne, kai kace makadan duniya ne suka taru suke buduri.
Lokacin da tawagar mayakan ta matso kusa kuwa aka ga yawansu sai kowa ya firgice, aka razana ainun, saboda yawansu ya ninka na mayakan birnin misra sau dubu.
Kura ta tshi ta turnuke sama, karar kofatun dawakai da haniniyarsu ta cika dodon kunne.
Kai! Komai jarumtakar mutun idan ya hango wannan runduna ta susarki DAKSUR dole ne ya firgita ya yi zaton ma yakin duniya ne ya barke.
Bisa mamaki sai rumdunar su sarki daksur suka ga kokadan abokan fadan nasu basu razana da ganinsu ba. Maimakon masu firgice ko su dimauce sai suka kara nutsuwa kuma kowa ya tsaya a inda yake, jira kawai yake yaji umarnin daza a bashi.
Bawani abubane yasa basu razanaba face addu'ar da suke ta. Faman karan tawa acikin zukatansu gami da neman taimakon allah.
Lokacin da su sarki Daksur suka hango abokan gamansu suka gansu 'yan kadan a gabansu tamkar a ajiye dan tsako a gaban shirwa. Kuma suka ga kokadan basu firgitaba, sai al'amarin yayi matukar basu mamaki, ya zamana cewa allah ya juya tsoro da shakku a zukatansu.
In ka dauke mutum uku da suke dasuke jagoran tarsu, gaba daya sauran mayakan duk sai tsoro ya darsu a cikin zuciyarsu harma suka sauka fara nokewa abaya kadan-kadan kawai jira suke yi suga yadda zata fara wakana ga manyan jarumansu a baban dogaronsu.
Sarki Uhaisu ne akan gaba, yana tafiya kai tsaye ba tare da shakkar komaiba , har maji yake kamar ya sauka daga kan dokinsa ya ruga da gudu izuwa cikin abokan gaba ya hausu da sara da suka saboda zakuwa da dakewar zuciya irin ta JARUMAN KWARAI.
A hannun daman sarki Uhaisu, sarki Daksurne. A hagunsa kuma sarkin yakine.
Lokacin da ya rage saura baifi taku arba'inba tsakanin rundunadunonin biyu sai rundunar su sarki daksur suka yi tirjiya aka fara kallon-kallo.
Sai da kura ta lafa sannan aka fara ganin juna sosai. Sarki daksur da sarki Raihan suka kurawa juna ido jaruma dabira da sarki uhaisu ma suka zubawa juna idanu. Ita kuwa yazila ta kurawa sarkin yaki idanu.
Jaruman shida suka kama tsuma ya zamana cewa kowannensu ji yake kamar ya zabura ya afkawa abokan gabarsa.
Da yake rundunar tazo kusa sai yazamana cewa babu bangaren da yake tunanin yayi amfani da mayakansa masa kibiya. Nan take sarkin yaki ya fara baiwa 'yan kasansa masu mashi da garkuwa umarnin su fara kai hari.
Ai kuwa sai suka hau kan sawun gaba, kowannensu ya saita mashinsa yana mai fuskantar a bokan gaba koda ganin haka sai shama sarki raihan ya baiwa nasa mayakan kasan umarnin su fito gaban filin daga wadanda adadinsu ai wuce su dubu arba in ba. Su kuwa dakarun arnan. Yan kasa adadinsu ya kai kusan dubu dari biyu da hamsim lokacin guda aka baiwa kowanne bangare umarnin su afkawa juna aikuwa sai kowanne banagare suka rugo da gudu suna kartar kasa kafirai suna ihu. Musulmi suna kabbara. Ahaka aka kacame da mummuna azababen yaki aka fara sokaiya da bugegeniya sai aka ga masu na fasa kirazan maza. Jini na tsartuwa da fallatsi. Mazaje na zubewa kasa suna zama gawa kai kace sassabe ake yi a gona. Sai da aka shafe sa a daya da rabi ana wannan bakin artabu sai gashi gaba dayan dakarun sun zama gawa. Dayansu bai tsira da raiba. Al amarin dai ya matukar dugunzuma hankalin kafirai ke nan suka cika da tsananin mamakin yadda aka yi wadannan kalilan din musulmin suka yi ragas da dakarunsu na kafirai wadanda suka nin kasu sau biyar a yawa? Koda sarki uhairu yaga wannan abu daya faru sai ransa ya baci zuciyarsa tafara tafarfasa kamar zata kone nan take ya zare takobinsa ya dagata sama ai kuwa sai sarki daksur da sarkin yaki ma suka zare nasu takobin. Koda ganin haka sai sarki raihan dabira da yazila ma suka zare nasu takubban. Kamar hadin baki sai kowanne runduna ta zabura ta durfafi abokiyar gabarta. Wohoho! Masifa idan ta zo babu makawa saita afku. Saboda tsananin karfin takun sawun mutane da dawakai sai da suka haddasa girgiza kasa a wannan wuri tamkar zata ta rufta. Kururuwar maza kuwa da haniniyar dawakai ta yawaita ainun har kai cewa da yawan mayakan sun firgice tun gabannin a hadu a fara gumurzu. Ai kuwa ana haduwa aka kacema da azabebban bakin artabu mai tsanani firgitawa daban tsoro nan fa aka bude kasuwar daukar rayuka. Sai gashi sassan jikin bil adama na shawagi asama tamkar ruwan samansu akeyi ji kuwa ya rinka fantsama yana malala akas kai kace teku ce ta balle. Babu abin da zai baiwa mutun mamaki face yadda arna ke ihu aya yin da suke mutuwa. Sannan kuma babu abin da zai baiwa mutun sha awa yajefashi cikin farin ciki face yadda musulmai suke kabbabra aya yin da mutuwarsu tazo duk sa adda sarki uhaisu sarki daksur dasu sarkin yaki suka kutsa cikin dakarun musulmai sai dai ka ga mazaje na zubewa kasa suna yin shahada. Haka ma a bangaren musulmai duk sa adda yazila dabira da sarki raihan ma suka kutsa cikin arna saidai kaga kamar sassabe sukeyi agona.
Komai lurar mutun bai isa ya gane bangaren da kke samun nasara ba. Wani babban abin mamaki shine babu yadda su sarki Daksur basu yi ba don su hadu da su sarki raihan ba amma ya gagara saboda yawan turmutsutsu da cakudewa gami da rudewar mazaje.
Sai da aka shafe sa'a uku da rabi ana wannan masifaffen yaki a sannan ne kowanne kowanne bangare ya gane kurensa domin an gane cewa babu bangaren daya samu rinjaye don gawarwakin kowanne bangare sun yawaita a kas.
Koda sarki Uhaisu ya lura da cewa ya kasa gane abin da ke faruwa a filin yakin sai ya fisge wani kaho da ke hannun wani badakare nasu ya busashi.
Nan take yaki ya tsaya kowanne bangare suka ja da baya. A sannan ne aka tsaya ana kallon-kallo. Nan take su sarki Daksur suka cika da tsananin mamaki bisa yadda kalilan mutane suka yi Ragas da mutanensu. Al'amarin daya matukar kona zukatansu ke nan aka sake yin cirko-cirko ana kallon juna. Nan take sarki Uhaisu ya nuna yazila da tsinin takobinsa yana mai nuni da cewar da ita yake son karawa yanzu.
Sarki daksur yai nuni izuwa ga sarki Raihan. Shi kuwa sarkin yaki yai nuni izuwa Dabira. Ba tare da sanin ko da wa zai gwabza ba.
Abinda suka sani kawai shine wadannan mayaka guda biyu wadanda suka saanya kayan yaki iri daya kuma suka rufe fuskokinsu da hular karfe, ba wasu bane face JARUMA YAZILA da DABIRA.
Da gudu. Aikuwa suna a tsakiya suka rufe junansu da sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta.
Tun kafin yazila ta fara gumurzu da sarki uhaisu tayi ta karanta wata addu a ta musamman a cikin zuciyarta. Bisa mamaki kuwa sai taji ta sami wani irin gagarumin karfi ya shiga jikinta irin wanda bata taba jinsa ba gami da azababban zafin nama na gaban kwatance. Aikuwa sai gashi ta zamewa sarki uhaisu alakakai ya rasa yadda zai yi da ita ya zamana cewa karfi yazo daya. Al amarin daya matukar baiwa sarki uhaisu mamaki ke nan. Domin shi a saninsa bai taba haduwa da jarumin dazo daya ba sai wannan karon.
Babban abin bakin ciki ma shine. Sarki daksur yayi masa bayanin cewa lallai da mace yake yaki. Kuma ba zai wuce jaruma yazila ko dabira ba.
Lokacin da sarki uhaisu yaga ya mace na neman bashi kunya sai zuciyarsa ta kufulo ta kama tafarfasa kamar zata kone don haka sai ya kara zage dantse iya karfinsa yaci gaba da kai mata wawan sara da suka cikin sauya salo al amarin da janyo ta rude kenan ta daina cigaba da karanta addu ar dake bakinta. Aikuwa damar da uahisu ya samu ke nan ya yai mata wani wawan duka da hannunsa cikin shammata a fuska saboda karfin dukan saida jini ya fetso daga cikin bakinta tamkar an yi wurgi da takarda haka ta fado daga kan dokin ta baje a kasa cikin matukar galabaice koda ganin haka sai sarki uhaisu ya dako tsalle daga inda yake tsinin takobinsa na kallon kas da nufin ya tsire cikin yazila. Duk da cewa yazila tana cikin wani mugun hali idanunta na gani dishi dishi. Koda ta hango sarki uhaisu yana shirin tsire mata ciki sai kwallah kabbara da karfi ta kaucewa harin nasa cikin matukar zafin nama. Take tsinin takobin tasa ta chaki kasa ta lume cikin kasar kafin yazare takobin tayi wuf ta mike tsaye zumbur kamar sifirin kawai sai ta daka tsalle sama ta doki kirjinsa sau uku. Yayi taga taga da baya kamar zai kife kasa amma sai ya cije saboda jarumta da juriya irin tasa ya tsaya cak yana kallon cikin tsananin mamaki domin itace bil adama ta farko wacce ta sami nasarar iya taba jikinsa haka.
A dai-dai wannan lokacinne abokan gaba suka yanyame jaruma yazila zasu hallakata. Ai kuwa sai ta tarwatsasu duk inda takai sara ko suka sai dai kaga ana zubewa kasa tana samarwa kanta hanya da karfin tsiya tana durfafar inda sarki Uhaisu ke tsaye.
A haka ta samu ta karaso inda yake suka sake ruguntsumewa da sabon masifaffen yaki.
Koda Uhaisu yaga cewa lallai karfi yazo daya shi da abokiyar gwaminsa sai ya sake shammatarta ya doki hannunta mai rike da takobin. Takobin tayi tsalle sama sai yazila ta daka tsalle sama domin ta cafo takobinsa shima sai ya daka tsalle saman ya doki kafafunta da kafarsa guda.
Nan take yazila ta rikito kasa arude kuma a hargitse, kanta na buguwa da kasa sai hular karfen ta ta cire, kyakkyawar fuskarta ta baiyana a fili karara.
Har sarki uhaisu yaji ya kamu da tsananin son jaruma yazila, don haka sai ya mike tsaye daga durkushen da yake yaja da baya a lokacin da suka fara kallon-kallo tsakaninta da shi tana mamakin abinda yasa ya fasa kasheta. Itama a lokacin ne ta lura da irin tsananin kyawunsa da kyawun surar halittarsa. Bisa mamaki sai itama taji ta kasa afka masa suci gaba da yaki.
A can bangaren jaruma dabira da sarkin yaki kuwa, labari ya shabanban domin kwarmazuwa suke yi har ta kai cewa kowannensu ya yiwa dan uwansa rauni sau biyu. Ita ta yankeshi a damtsensa na hannun dama da kuma gefen kirjinsa jini na zuba amma ko gezau bai yiba. Shikuma ya yanketa a gadon bayanta da cinyarta ta hagu gashi itama jini na diga amma bata sare ba sai dada fafatawa suke.
A bangaren sarki raihan da sarki daksur kuwa al'amarin ba kyangani domin nema suke yi su yi RAGAS saboda kowannensu ya yiwa dan uwansa rauni sama da guda biyar, duk jikinsu yai fata-fata da jini, har ta kai cewa suna layi, jiri na dibansu, suna layi kamar za su bingire kasa.
A na cikin wannan hali ne kawai aka ji an busa kahon tsayar da yaki. Faruwar hakan keda wuya sai sarki Uhaisu yaruga izuwa inda dokinsa yake yai tsalle ya haye kansa sannan ya zabureshi da gudu ya nufi can baya inda sansanin su na yaki yake amma yana juyowa yana waigen jaruma yazila alokacin da itama ta bishi da kallo kawai.
Sarki raihan da sarki Daksur kuwa, sai suka yanke jiki suka fadi kasa sumammu.
Dabira da sarkin yaki kuwa, suka ja da baya suna kallon juna cikin cizan yatsa da tsananin ta kaici domin ba haka suka soba.
A binda suka so shine a barsu su fidda raini ya zamana cewa daya ya kar daya. A guje kowanne bangare suka rugo suka dauke sarkinsu.
Nan take kafirai suka kwashe gawarwakin mutanensu da marasa lafiyarsu suka koma da baya izuwa can sansanin nasu sukuwa musulmi sai suka kwashe jama'arsu da dukkan kayayyakin nasu suka koma cikin birnin misra aka mayar da kofar birnin aka rufe.
A guje aka tafi da sarki raihan a cikin keken doki izuwa gidan sarauta. Jaruma yazila da dabira na biye da shi hankalinsu a dugunzume bisa ganin halin da yake ciki ko kadan ma basu damu da raunikan dake jikinsuba.
Cikin hanzari aka shigar da sarki cikin turakarsa aka kwantar da shi akan gado. Nan da nan aka kirawo likitan sarki yashiga aikinsa. Ai kuwa ba a dadeba sai sarki ya farfado ya dawo cikin haiyacinsa.
Yana bude idanuwansa yayi arba da Humaira tsaye akansa tana zubar da hawaye, dabira mana tsaye kusa da ita tana kuka, sai kuma Yazila a can gefe daya ta kura musu idanu cike da kwalla.
Bisa mamaki sai suka ga sarki raihan ya dubesu cikin matukar mamaki, kawai sai ya yunkura ya mike zaune yana mai cewa, "mu yiwa allah godiya daya bamu nasara akan makiya".
Koda jin haka sai mamaki ya dada kamasu. Dabira ta matso dab da shi ta zauna akan gefen gadon ta dubeshi tace, "haba ya abbana saboda me zaka ce mun sami nasara alhalin bamu kashe manyan shugabannin abokan gababa , kuma bamu kai tutarsu kasba? Ai burina shine mu ragargazasu kuma mu cafkesu a matsayin bayi sannan mu kwashe dukiyoyinsu a matsayin ganima kuma muje har can birninsu mu kafa tutar musulunci".
Lokacin da Dabira tazo nan a zancenta sai sarki Raihan ya sake yin murmushi a karo na biyu yace, "ai abinda da nake nufi da mun sami nasara shine, basu cimu da yaki ba. Duk da cewa sun ninkamu ninkin-ba-ninkin a yawa kuma mun yi matukar basu mamaki da tsoro domin basu taba tsammanin cewa hakan yakin zai kasance ba. Kuna ganin dai da kansu suka busa kahon tsayar da yakin suka ja da baya. Babban abin daya kara faranta min rai shine, wannan bakon jarumin da suka zo da shi bawani bane face sarki Uhaisu sadaukin da babu wani mayaki da ya kaishi jarumtaka da sa'ar yaki kamarsa, amma sai gashi ya kasa karar damu kuma a karshe ma sai na ga jikinsa yayi sanyi, haka kawai ya janye yakin ya ruga da gudu ya hau dokinsa ya bar filin dagar.
Ko shakka bana yi addu'ace ta kwacemu a wannan yaki, amma ba dabarar muba ko iya yakinmu ko jarumtakarmu. Yanzu abinda nake so daku shine, kuje ku yiwa jikinku magani sannan kowa ya huta. Idan allah ya kaimu yammaci sai mu zauna mu tattauna akan yadda zamu bullowa wannan yaki saboda tabbas sharar fage muka yi yanzu ne za a fara yakin. Suma abokan gabar tamu sun koma masaukinsu ne domin suyi sabon shiri da tsananin dabarar daza su yi su sami nasarar mallakar wannan birni namu mai albarka.
Ba tare da wata gardama ba su jaruma dabira suka yiwa sarki raihan sallama suka fice daga cikin turakar tasa suka barshi tare da likitansa da Humaira.
Lokacin da jaruma Yazila da 'yar uwarta Dabira suka isa turakarsu sai suka zauna suka shiga yiwa kansu magani. Da yake ita yazila bata da rauni sosai a jikinta sai ta fara sawa dabira maganin.
Duk da juriya irin ta dabira da jarumtakarta sai da ta rinka runtse idanu saboda tsananin zafi da zogin da take ji, har yazila taji ta kamu da dan tausayinta.
Yazila tayi ajiyar zuciya sannan tace, "yake 'yar uwata kiyi sani cewa na so ace nice na kafsa yaki da sarkin yaki domin bani da burin dayafi mu dauki fansa akansu shi da sarki Daksur. "
Dabira ta numfasa tace, "ni kaina nayi matukar mamaki bisa yadda aka yi na kasa samun nasarar hallakashi farat daya. "
Yazila tace, 'Ai ban yi mamaki ba domin kinsan cewa shi makiyi ko yaushe a cikin neman sa'a yake da sauya dabaru na yaki. Kinga wannan bakon jarumin sarkin da suka zo da shi wanda muka fafata da shi ba karamin tai maka musu yayiba, in ba don shi ba ma da farat daya zamu yi musu, hatta salon yakin da naga sarkin yaki keyi irin nasa ne. "
Koda jin haka sai dabira ta waigo ta dubi yazila ta ce, "tabbas biri yayi kama da mutum, domin yadda kika bani labarin yadda kuka fafata yaki da shi a wancan karon karfinsa da jarumtakar sa sun karu yanzu, in ba don haka ba lallai da sai na samu nasarar hallakashi. Wai shin dama ina son nayi miki wata tambaya. Lokacin da kuke bakin artabuke da wannan jarumin sarkin, duk da cewar ina cikin yaki na lura da lokacin da ya sami nasarar dukan kafafunki kika fado kasa a matukar galabaice. Harya daga takobinsa zai dankara miki sara ya hallakaki a dai-dai lokacin da hular kanki ta cire ta fadi can gefe daya sai kuma na gaya fasa. Shin ko kin san dalilin daya sa ya fasa hallakaki?".
Sa'adda yazila taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace, "ya za a yi nasan dalilin da yasa ya fasa kasheni? Nidai kawai naga jikin sa yayi sanyi a sa'adda yayi arba da fuskata babu mamaki nayi masa kamane da wata 'yar uwarsa".dabira tace haba yazila ya a a yi a sami wata mai kama dake in ba niba ? Ai a gaba daya nahiyar nan nida ke mun fita daban domin ke ma kin san cewa ba karamin kyau allah ya bamu ba ni dai kawai abinda na fahimta shine nan allah ya jarrabi wannan sarki da kamu da sonki. Wannan shine kadai dalilin daya sa ya fasa hallakaki sa adda yayi arba dake ” yazila tace haba ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki? In ban da abinki yau ne fa kadai ya fara ganina ” dabira tayi yar karamar dariya sannan tace ai shi so farar daya yake shigar mutun ba sai an shaku ba kiji tsoron allah ki gaya mini gaskiya ke kanki baki ji kin kamu da sonsa ba ? Rantse da girman iyayenna ban taba ganin kyakkyawan da namiji ba kamarsa gashi da kyan sura. Gashi sarki kuma gawurtaccen jarumi. “ Yazila ta maidawa dabira murmushi sanna tace. “ Ai koda ina sonsa kuwa daga yanzu da na daina sonsa tun har kika yi masa irin wannan yabo. Domin alama ce cewar kin kyasa kema kina so idan har zai karbi addinin allah nan gaba zan tsaya tsayin daka naga kin aureshi “.
Koda jin wannan batu sai hankalin dabira ya dugunzuma ainun tace, "Ai koda nima ina sonsa ba zan yarda na bashi soyayyata ba tonda ke ya gani yace yana SO ba niba. Ina nufin ke ya fara gani, don haka lallai keya kamata ki mallakeshi".
Abu kamar wasa sai gardama ta karde tsakanin jaruma yazila da jaruma dabira. Daga karshe bayan itama Yazila ta sawa Dabira magani sai ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin nasu domin kawai ta katse wannan muhawara dake tsakaninsu.
*** *** ***
A can sansanin su sarki Daksur kuwa, lokacin da sarki Uhaisu ya iso bakin tantinsa sai ya sauko daga kan dokin nasa ya daure dokin. Har yayi nufin shiga cikin tantin nasa sai ya fasa ya taka da kafafunsa ya shige izuwa cikin daji ya shige duhuwar wadansu dogayen bishiyoyi ya sami karkashin inuwa mai sanyi kusa da wata korama mai ruwa garai-garai.
Koda ganin wannan korama sai farin ciki ya lullubeshi tun sa'adda yake fafata yaki. Nan take ya tsugunna a gaban wannan korama ya zuba hannayensa guda biyu ya kwarfo ruwan domin ya kai bakinsa ya sha.
Kawai sai yaga hoton fuskar jaruma Yazila a cikin ruwan tana yi masa murmushi.
Nan fa ya kasa shan ruwan ya zubar ya sake debo wani ruwan, aikuwa sai ya sake ganin yazila a ciki, sai da ya yi hakan sau uku sannan ya rintse idanunsa ya sha ruwan. Koda ya bar bakin koramar ya koma karkashin bishiya ya jingina bayansa a jikin bishiyar yaci gaba da ganin yazila a wuri daban-daban tana masa gizo.
Koda ya fashinci cewar idanunsa ne suke yaudarar sa han kalinsa ya duguntsuma ainun don yagane cewa ya fada cikin tekun SOYAYYA kuma tekun da bai san iyakar zurfinsa ba.
Nan fa yaji babu abinda yake so a duniyar gabadaya sama da sake ganin JARUMA YAZILA a zahiri.
Ta yaya zan sake ganinta har ya nuna mata abinda ke zuciyarsa ko ya furta da bakinsa alhalin ta kasance abokiyar gabarsa suna kokarin hallaka juna ? Yanzu haka ma ai yazila tana can cikin birnin misra kuma an kule kofar garin.
Koda ba a rufe ba ai baza a barshi ya shiga ba domin ana ganinsa maza a afka masa don hallakashi.
Nan fa sarki Uhaisu ya fara tunanin zuci yana mai cewa, Ai kuwa idan sarautata da jarumtakata basu sana mallaki wannan kyakykyawar budurwa ba, to kuwa basu da wani amfani a gareni".
Nan take sarki Uhaisu ya kudurce a cikin zuciyarsa cewar ta kowanne hali sai ya tabbatar da cewa ya mallaki Jaruma yazila.
Al'amarin sarki daksur kuwa, lokacin da suka dawo sansanin su inda suka kafa tantinsu sai suka ga dokin sarki Uhaisu a daure a kofar tantinsa sai suka yi tsammanin ko yana ciki dan haka sai sarki ya tura aje akirawoshi a gaya masa cewa yaje tantin sarki Daksur domin su tattauna dan gane da wannan gagarumar matsala da aka samu a filin yaki.
Kai tsaye sarki daksur da sarkin yakinsa da dukkan sauran wakilan sarakunan da suka halarci wannan yaki suka dunguma suka shiga cikin tantin sarki Daksur aka zauna aka fara tattaunawa dangane da a bubuwan da sukafaru a wannan yaki na ban al'ajabi wanda miliyoyin mutane suka kasa kawar da 'yan tsiraru.
Ana cikin wannan hali sai manzon da aka tura tantin sarki Uhaisu ya shigo ya sanar da sarki Daksur cewa sarki Uhaisu baya cikin tantin.
Koda jin haka sai hankalin sarki Daksur ya duguntsuma ainun yarasa abinda kemasa dadi. Nan take ya tashi mutun goma yace su bazama neman sarki Uhaisu a cikin daji.
Bayan tafiyar mutane goman ne sarki daksur ya dubi jama'ar tasa cikin nutsuwa yayi gyaran murya. Sannan yace, "ya ku rundunar karya makiya kuyi sani cewa a duniya ba a taba yaki na ban mamaki irin wanda aka linka abokan gaba sau dubu amma suka zo suka gagara. Babban wani abu daya bani tsoro kuma ya firgitani shine ganin yadda a bin dogaronmu sarki uhaisu ma ya sare a wannan yaki koda yake ba sarewa yayiba, ga dukkan alamu akwai wani abu daya faru gareshi.
Ko dai sihirin wadannan abokan gaba tamu ya shigeshi ko kuma ya fada tarkon soyayya domin tabbas ya sami damar da zai kashe daya daga cikin jaruman matan nan walau Yazila ko Dabira amma sai ya fasa. Ina kyautata zaton dai abinda nake zargi gaskiyane. Koma dai menene ai an ce waka abakin mai ita ta fi dadi. Idan ya zo zai yi mana bayani da bakinsa.
Yaku 'yan uwana ina so kusani cewa wannan ita ce kadai damar da muke da ita wacce zamu iya hallaka wadannan abokan gaba tamu. Idan muka yi sakaci aka tashi daga wannan yaki bamu baje birninsu. Ba mun kama dukkan mazajensu mun yankasu,sannan mu afkawa matayensu muyi ta saduwa dasu har sai sun haife irinmu to har abada bazamu sami nutsuwa da kwanciyar hankaliba a wannan nashiya domin sai an wayi gari ma sun rushe dukkan addinanmu kuma sun kama kasashenmu".
Lokacin da sarki daksur yazo dai-dai nan. Zancensa wadannan mutane goma da aka tura neman sarki Uhaisu suka shigo cikin tantin.
Take suka zube kasa a gaban sarki babban cikinsu yace, "ya shugabana mun duba ko ina a cikin wannan daji bamuga sarki Uhaisuba a nan kusa ba, kuma bamuga inda sawayensa sukeba" koda sarki daksur yaji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya mike tsaye zumbur yace, "ai kuwa bamu ga ta zamaba domin nasararmu a wannan yaki ta dogara ne akan kokarin sarki Uhaisu, yazama dole muje mu nemoshi mu dawo dashi wannan sansani namu kafin a sake busa kahon cigaba da wannan yaki"
Koda gama fadin hakan sai sarki Daksur yaja dakaru sama da mutum dari uku suka nausa izuwa cikin daji.
====================================
Anan zamu dakata
Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani
[7/2, 11:12 PM] ᴬᴮᵁᴮᴬᴷᴬᴿ Quyraemey: ***★BAKIN ARTABU**cigaban
**JARUMA*YAZILA★***
Littafi Na Daya {2}
TYPE B
***Nasiru**Muhammad**Tijjani***
Marubucin ya cigaba da cewa:
==============================
=============================
AL'amarin Sarki Uhaisu kuwa lokacin da tunani ya addabe shi sai kawai ya yanke shawarar kawai ya tabi birnin kisra ya mika kansa amatsayin ganimar yaki wata kila ya sami damar da zai sake ganin kyakykyawar fuskar yazila a karo na biyu koda kuwa zai rasa rayuwarsa.
Koda sarki Uhaisu yagama aiyana hakan a cikin zuciyarsa sai ya zagaye ta bayan tantin sansanin nasu ya bita cikin duhun ciyayi da rub da ciki har sai da yayi tafiya mai nisa ya isa bakin kofar birnin misra ba tare da ya rike makami ba.
Batare da shakkar komai ba sarki Uhaisu ya durfafi bakin kofar inda dakaru masu gadi suke tsaitsaye wa danda adadinsu yakai mutum dari uku.kowannensu rike da kwari da baka ya dameta iya karfinsa.
Harsun yunkura zasu saki harbi sai shugabansu ya daka musu tsawa yace, "kada dayanku ya kuskura yayi harbi shin bakwagani abokin gabartamu bai zo da makami ba, kuma shi kadaine ya durfafomu? Ku tsaya yazo muji abinda ke tafe dashi".
Duk dajin haka dakarun basu saki jikinsuba, kuma basu sauke makamansuba, sai suka jirashi.
Ai kuwa yana isowa kusa dasu wasu suka rufeshi daduka har suka kaishi kas, a garin hakanne suka fasa masa baki da hanci saiga jini yana yoyo.
Nan dai suka turmusheshi. Da karfin tsiya suka sanya masa sasari a hannayensa da kafunsa, a sannan ne aka bude kofar birnin aka tusa keyarsa gaba aka shiga da shi ciki aka sake rufe kofar.
Kai tsaye aka nufi fadar sarki Raihan da shi, dakaru kimanin mutum dari na kewaye da shi rike da makamai suna rakashi.
Duk da cewar dakarun na rike da makamai a tsorace suke gani suke kamar ko yaushe zai iya tsinka sasarin jikinsa ya hallakasu. Babban ma abinda ya daure musu kai shine, tunda aka shigoda shi cikin birnin sai kalle-kalle ya keyi yana ta murmushi kai kace wanda akayiwa albishir ne da sarautar duniya duk da wulakancin da akai masa bai dameshiba.
Shi kansa yan mamakin yadda ya tsinci kansa a cikin wannan matsayi, don haka sai ya fara zancen zuci yana mai cewa aransa.
"Hakika SO makaho ne, domin idan yakama mutum idanunsa rufewa suke yi kuma hankalinsa gushewa yakeyi har ya aikata abinda zai zubar da kimarsa da darajarsa. Yanzu in banda aikin SOYAYYA ya za ayi nabari na wulakanta haka a matsayina na sarki mai isashshen iko kuma sadauki mai jarumtaka taban al'ajabi. "
Tun kafin su isa gidan sarauta da sarki Uhaisu labari ya riski Sarki Raihan cewa gashi nan an kamo sarki Uhaisu.
Koda jin haka sai sarki Raihan yace karyane, wannan ai zan cen banzane zancen wofi. Ya ya za a zo masa da abin da bazai taba yuwuwaba? Ai ko dakarunsa ne na yaki zasu taru bazasu iya kamo sarki Uhaisu ba da karfin tuwo ba".
Sa'adda manzon da ya kawo labarin yaji abinda sarki raihan yafada sai ya rantse masa da girman allah akan cewa labarin da yazo da shi na gaskiyane, amma idan sarki yana shakka ne to yaje da kansa yaga zahiri ko kuma ya saurara a iso da sarki Uhaisu domin ana hanyar kawoshi nan fada".
Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube sarki raihan yaji ma ba zai iya jira ba.
Nan take yasa aka kawo masa dokinsa ya hau sannan yasa aka shirya dakarun yaki sama da mutum dubu uku suka take masa baya suka bi hanya.
Ai kuwa suna isa tsakiyar gari suka hango sarki Uhaisu a daure cikin sasarai an taho da shi ana ingiza keyarsa a wulakance. Cikin tsananin mamaki sarki Raihan yaja linzamin dokinsa yatsaya cak, suma dakarun dake bayansa sai suka yi cirko-cirko.
Koda aka iso da sarki Uhaisu daf da sarki raihan sai aka tsaya cak aka kama kallon tsakanin Raihan da Uhaisu, a lokacin da uhaisu yake ta faman murmushi.
Sarki raihan ya kurawa uhaisu idanu ya kare masa kallo tsaf cikin nutsuwa sannan yace, "yakai wannan sarki, kai kuwa menene dalilin daya sa ka kawo kanka garemu alhalin karfimmu bazai iya sawa mu kamakaba?
Tabbas ruwa baya tsami banza, lallai akwai dalilin daya sa ka kawo kanka cikin ruwan sanyi. Ko dai kana son ka yaudaremu ka cutar da mu, ko kuma kana da wata bukata a wajenmu wadda bamu santa ba. Kayi min bayani na gaskiya ko yanzun nan nasa a hallakaka".
Lokacin da sarki Uhaisu yaji wannan batu sai yayi murmushi yace, "ya kai wannan sarki kayi sani cewa na rantse da girman iyayena da kuma darajar karagata banzo gareku domin na yaudare kuba kona cutar daku ba nazo ne domin ina da wata bukata guda daya a wajenku wacce sai ni da kai zan iya fadinta".
Koda jin wannan batu sai sarki raihan ya cika da tsananin mamaki, kawai sai sarki raihan ya cika da tsananin mamaki, kawai sai ya dubi dakarun dake janye da uhaisu ya basu umarni su kwanceshi. Nan fa dakaru suka tsorata ainun suka kama noke-noke, har sai da sarki ya daka musu tsawa sannan suka cika umarni. .
Maimakon sarki raihan ya sake hawa dokinsa sai ya jera tare da sarki uhaisu a kas suka tako kafafunsa suka nufi fada su biyu kacal tamkar sun kasance aminan juna. Domin tuni sarki raihan ya sallami dakarunsa gaba daya sunyi gaba.
Lokacin da sarki uhaisu da sarki raihan suka jero suna tafiya sai suka kama hira, inda sarki raihan yace, "ya kai abokina yanzu ai saika sanar dani dalilin daya sa ka kawo kanka garemu tunda babu mai jinmu".
Koda jin haka sai sarki uhaisu yayi murmushi ya ce "haba abookina hanzarin me kakeyi ne haka ? Ai a matsayina na bakonka kamata yayi ka bani masauki tukunna da abinci domin na huta sannan sai muyi magana cikin nutsuwa".
Koda jin haka sai sarki raihan yayi murmushi ya ce "ka gafarceni, hakika nayi kuskure kuma nayi gaggawa amma ba komai ne yajanyo hakan ba face tsananin kaguwa da zumudin sonjin bukatarka da kazo mana da ita tunda aka fara wannan tafiya a cikin birnin misra sarki uhaisu ya cika da tsananin mamaki bisa ganin yadda mutanen garin suke tafiyar da harkokinsu sabanin irin na jama'ar birninsa.
Abinda ya fara daure wa sarki uhaisu kai shine, duk inda suka gifta sai yaga mutane cikin shiga ta mutunci maza da mata babu inda yaga anyi shiga mai nuna tsaraici.
Kowa ya kalla kuma sai yaga ko dai yana sana'a ne ko kuma yana gabatar da wani aikin mai muhimmanci, ko sau daya baiga inda ake ashararanci ba ko wata dabi'ar banza wacce bata dace ba nan take sarki uhaisu yaji dabi'ar mutanen birnin misra ta burgeshi gami da bashi mamaki domin shi irin labaran da ake kai masa akansu ba haka ya gani ba da idanunsa.
Lokacin da suka zo zasu gifta ta masallaci kuwa ya hango mutane a ciki wasu suna nafilfilu wasu kuma suna karatun Qur'ani sai nan take yaji tsikar jikinsa ta tashi gaba daya yagane cewa lallai wannan addini addinine wanda yakamata ba tsangwamawa ba. Saboda ana yinsa ne a cikin hankali da nutsuwa.
Addini ne wanda yakamata ayi bincike sosai a kansa domin a gano gaskiyarsa ko rashin gaskiyar.
Haka dai raihan da uhaisu suka ci gaba da tafiya har suka iso cikin gidan sarauta.
Duk inda suka ratsa sai kaga mutane suna ratsewa da rakubewa cikin alamar tsoro domin gani suke yi kamar ako yaushe sarki Uhaisu zai iya birkicewa ya hau mutane da sara da suka amma har suka iso tsakiyar fadar babu abinda ya faru.
Abinda ya daurewa sarki raihan kai shine, yaga sarki Uhaisu yana ta waige-waige da kalle-kalle alamar cewa so yake yaga wani.
Abin tambayar anan shine waye wanda sarki uhaisu ke son gani kokuwa wata makarkashiya ya shirya ne so yake jama'arsa su hauro katangar birnin su afkamusu da yaki? Koda gama aiyana hakan sai kuma wata zuciyar ta ce da shi "ai kuma hakan bazata taba yiwuwa ba tunda akwai dakaru akan ganuwa wadanda suke kula da tsaro dare da rana, ko yaya suka ga wani abu zasu gaggauta sanarwa bayan sun iso tsakiyar fadar sai sarki raihan ya kirawo sarkin gida ya umarceshi da yakai sarki uhaisu izuwa ga masuki na musamman inda aka saba saukar manyan baki.
Har sarki uhaisu ya budi baki zai tambayi sarki Raihan wani abu sai kuma yafasa.
Raihan ya dubeshi cikin murmushi yace, Bakinnan naka akwai magana. Amma kuma kayi shiru bakace komaiba".
Sarki uhaisu ya maidawa sarki raihan martanin murmushi yace, "babukomai idan muka zauna don tattaunawa zaka ji komai".
Nan take suka yi sallama sarkin gida ya tafi da sarki Uhaisu izuwa ga masaukinsa.
Har suka yi nisa a cikin gidan sarautar suka kule sarki Uhaisu bai daina waige-waige da kalle-kalle ba. Kai da gani ka san cewa a cikin zakuwar son ganin wani yake.
Lokacin da sarki Raihan ya isa turakarsa ya kwabe damarar dake jikinsa sai ya shiga kewaye sannan ya fito ya zauna a harabar turakarsa yana alwala domin ya tafi masallaci saboda lokacin sallar azahar ya kusa.
A dai-dai wannan lokaci ne ya hango jaruma Yazila da Jaruma Dabira sun taho gareshi da sauri fuskokinsu na nuna alamun tsananin damuwa da fargaba.
Da isowarsu daf da shi sai suka durkusa suka kwashi gaisuwa sannan suka yi shiru har sai da ya idar da alwalar sannan Dabira tayi gyaran murya tace "ya kai abbanmu kayi sani cewa labari ya riskemu cewa sarki Uhaisu ya shigo cikin birnin nan harka bashi masauki acikin gidannan.
Bayan su dabira sun koma tura karsu sun zauna Dagacan sai Dabira tayi ajiyar zuciya sannan ta dubi YAzila tace, "yake 'yar uwata nifa abinda na fahimta shine, sarki Uhaisu ke ya biyo.
Duk yadda akayi tunaninki da begenki ne suka addabeshi yakasa hakuri, shine ya sallama rayuwarsa ya kawo kansa domin kawai ya kashe kishirwar rashin ganinki".
Koda jin wannan batu sai jaruma Yazila ta hade fuska cikin alamun fushi tace, "Ai wannan tunanin naki dai-dai yake da mafarki, yaya za a yi sarki kamar Uhaisu mai daraja, daukaka da jarumtaka haka zai zubar da kimarsa da mutuncinsa saboda kawai soyayya?
Ni kam ina kyautata zaton lallai akwai wani mugun nufi a zuciyarsa amma ba wai soyayya ba".
Sa'adda dabira taji wannan batu sai ta kyalkyale da guntuwar dariya sannan tace, "ko da yake dai ni dake duk bamu taba yin SOYAYYA ba, amma ai ga yadda muke samun labarin zafinta da sharrinta babu abinda masoyi ba zai iya yiba domin ya mallaki masoyinsa.
Ko shakka bana yi saboda ke sarki Uhaisu ya mika wuyansa.
Ni shawarar da zan baki itace, idan har zai karbi addinin allah toki amince masa ya aureki domin yin hakan zai janyo miliyoyin mutane su karbi musulunci. Idan kuwa hakan ta faru ladan daza ki samu ba kadan bane.
Koda jin haka sai yazila tayi murmushi tace, "yake 'yar uwata kiyi sani cewa yadda nake kaunarki a yanzu cikin zuciyata nafi son ace kece kika sami wannan lada mai tsoka bani ba. Kuma duk yadda zanyi saina yi domin na tabbatar da cewa kece kika samu wannan lada. Kada ki sake zuwa mini da uzurin cewa ni sarki Uhaisu ya fara gani kuma nice wadda ya kamu da SO Ina soki gane cewa ni dake kammanninmu daya ne sak tamkar an tsaga kara.
Ko a yanzu in banda mahaifiyarmu babu wanda yake iya bambantamu a zahiri. A matsayina na wacce ta fara zuwa duniya kafin ke, naci girma na bar miki sarki Uhaisu idan har ya karbi addinin musulunci.
Idan kuwa yaki karbar musulunci tofa dani dake duk zamu hakura da shi".
Lokacin da yazila tazo nan a zancenta sai hawaye ya zubowa Dabira ta kama kafadun Yazila ta rike tace, "yake 'yar uwata kiyi sani kina son ki dora mini nauyin da zuciyata bazata iya dauka ba. Na rantse da girman iyayenmu indai kina raye bazan iya auren mijin dana san cewa sonsa ya darsu a zuciyarki ba koda kuwa gwargwadon kwayar zarra ne. "
Koda gama fadin hakan sai Dabira ta juya da sauri ta fice daga cikin turakar tana ta zub da hawaye, Yazila na kiranta amma sai taki komowa.
Al'amarin da yai matukar girgiza hankalin Jaruma yazila kenan, ta rasa abinda kemata dadi a duniya kuma taji kamar ta dora hannu aka ta rafka ihu.
Al'amarin sarki Uhaisu kuwa, bayan yaci ya sha yai hani'an sai ya baje akan gado.
Abinka da gajiyayye nan da nan jikinsa ya mutu amma duk da haka sai barci ya gagareshi saboda tunanin zuci nan fa yaji kamar ya mike tsaye yaje ya nemi iso a wajen sarki raihan domin su gana ya sanar da shi abinda ke ransa, amma sai ya kanne domin kada ya nuna zalamarsa.
Haka dai sarki Uhaisu yayi ta juye-juye akan gado ya rasa sukuni har tsawon sa'a biyu. Yana cikin wannan hali sai kawai yaji an kwankwasa masa kofa.
Cikin hanzari ya mike tsaye yaje ya bude kofar kawai sai yaga sarki Raihan a tsaye fuskarsa cike da murmushi.
Sarki raihan ya dubeshi yace, "ka gafarceni ya kai abokina, kayi sani cewa na kasa yin komai saboda zakuwa da son jin bukatar da zaka zo mini da ita, shiya sa na zo maka yanzu tun gabannin ka sami cikakken hutu".
Sa'adda sarki Uhaisu yaji wannan batu sai yayi murmushi yace, "ya kai abokina kayi sani cewa irin halin da kashiga nima haka na tsinci kaina, don haka yanzu sai mu zauna na sanar da kai bukatar da na zo maka da ita nan take suka zauna a tare bisa gefen gado. Sarki Uhaisu ya nutsu kuma yai gyaran murya yace, 'ya kai abokina kayi sani cewa a iya sani rayuwata tun daga kuruciyata kawo izuwa girmana ban san daci da zakin so yayyaba sai a yanzu dana halarci wannan yaki da muka fafata mu daku.
Ina mai sanar da kai cewa na rasa sukuni da kwanciyar hankali sakamakon kamuwa da tsananin son jarumtar wacce tayi yaki dani. Tun a lokacin dana sami nasarar bugeta ta fado kasa a galabaice har hular karfen dake kanta ta cire, ina yin arba da kyakykyawar fuskarta na kamu da sonta nan take.
A cikin kowacce da ika begenta nake, a yanzu haka idan ban gantaba a yau dinnan rayuwata zata iya shiga cikin mugun yanayi.
Ni yanzu a binda nake so da kai shine ka bani auren wannan jaruma a shirye nake na dawo bangarenku a wannan yaki muddin zan samu wannan biyan bukata, kuma duk abinda kuke bukata na dangane da dukiya zan bayar.
Kai in takaice maka ma ko karagata kake so zan iya baka ita muddin zan mallaki wannan jaruma domin babu wani abu da yakai matsayinta a cikin zuciyata".
Lokacin da sarki Uhaisu yazo nan a zancensa sai sarki Raihan ya cika da tsananin mamaki domin bai taba tunanin cewa wannan ce bukatar da sarki Uhaisu zai zo masa da itaba.
Sarki raihan ya sunkui da kansa kas, alokacin da ransa ya baci, zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone don haka sai ya dubi sarki uhaisu a fusace yace, "A ina ka taba ganin ruwa da wuta sun hadu a waje daya?
Kai kafirine mu kuwa musulmine, babu yadda za a yi mu baka auren 'yarmu idan har kana son na baka auren wannan yarinya dole ne kayi abu uku.
Abu na farko shine, dole kakarbi addinimmu. Abu na biyu, dole ne ka je ka yankomin kan sarki daksur da kan sarkin yakinsa.
Abu na uku wanda shine na karshe, dole ne kaje ka kafa tutar addinin musulunci a birninka da birnin sarki Daksur.
Duk sai na tabbatar da cewa ka sami nasarar aiwatar da wadannan abubuwa guda uku sannan zan baka auren wannan 'ya tawa"
Lokacin da sarki Raihan yazo nan a jawabinsa sai idanun sarki Uhaisu suka ciko da kwalla yace, "tabbas kazo min da manyan al'amura wadanda bazan iya gabatar dasuba don kawai biyan bukata taba.
Kafin sarki uhaisu ya gama rufe bakinsa tuni sarki raihan ya tafa hannayensa sau biyu kawai sai sarki Uhaisu yaji anmaka masa makami akeyarsa.
Nan take ya sulale kasa maga shiyan cikin mummunanan hali.
Nan take wasu dakaru su uku suka baiyana suka turmushe sarki Uhaisu aka sake zuba masa sarkoki a hannunsa da kafafuwansa.
Sarki raihan ya dubi dakarunsa yace, "kutafida shi izuwa kurkuku ku kulle shi.
Nan take kuwa dakarun suka dauke sarki Uhaisu suka fice dashi.
~WANNE MATAKIN SU SARKI DAKSUR ZASU DAUKA IDAN BASUGA SARKI UHAISU BA?
~SHIN ZA A CIGABA DA WANNAN YAKI NE KO KUWA ZA A DAKATAR DA SHI?
~TSAKANIN YAZILA DA DABIRA WACECE ZATA MALLAKI UHAISU?
Muhadu a BAKIN ARTABU na uku don jin cigaban wannan kasaitaccen labari
====================================


Post a Comment (0)