MA'ANAR AZUMI DA KUMA FALALARSA


*MA’ANAR AZUMI DA KUMA FALALAR SA*
 
1- *Azumi*: shine kamewa daga dukkan abubuwan da suke bata Azumi tun daga bullowar Al-fijir har zuwa faÉ—uwar Rana, amma tare da Niyya ta Ibada.
 
2- Azumi yana da *falaloli* masu yawa, waÉ—anda shi mai yin Azumin yake amfanuwa dasu tun anan Duniya haka kuma a gobe Al-Qiyama.
 
Ayoyi waÉ—anda suke bayyanannu sun zo a cikin Littafin Allah mai Girma, suna kwaÉ—aitar damu yin Azumi, domin neman kusanci zuwa ga Allah mabuwayi da É—aukaka, kuma ayoyin sun zo ne suna bayanin falalar sa, kamar faÉ—ar Allah (SWT): 

_(Yin Azumin shi ne yafi muku alkhairi da kunsan irin falalar da take cikin sa)_     
[Bakara: 184].
 
Kuma Manzon Allah ï·º cikin abunda ya tabbata a cikin Sunnah ya bayyana cewa *AZUMI GARKUWA NE* daga sha’awa, kuma garkuwa ne daga Wuta, sannan kuma Allah maÉ—aukaki ya kebance mai Azumi da samun wata Ƙofa daga cikin Ƙofofin Aljannah, haka kuma shi Azumi yana raba Zukata daga Sha’awa, yana raba su da miyagun É—abi’un da suka zamar musu jiki, sai su wayi gari suna masu natsuwa da kwanciyar hankali, zamu dakata anan sai idan Allah ya kaimu gobe sai mu cigaba da bayani kan yadda akayi Azumi ya zama Garkuwa Insha Allah, Allah ya bamu Ladan wannan Azumi, ya biya mana bukatocin mu Ya ye mana halin da muke ciki, Amin. 

*Article 01 Na Ramadan Daga AnnasihaTv*

*Asha Ruwa Lafiyah*

*Domin Samun wa'innan Articles sai kabi wannan link din*
👇

https://t.me/annasihatvchannel
Post a Comment (0)