YADDA AKE SHAYARWA TARE KUMA DA SHAYAR DA NONON UWA ZALLAH HAR WATA SHIDA BAYAN HAIHUWA



*_السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته_*
➖➖➖➖➖➖➖➖
*_” بسم الله الرحمن الرحيم_*

_*Daga zauren*_
_*📚Ana- muslim📚*_
..
.
YADDA AKE SHAYARWA TARE KUMA DA SHAYAR DA NONON UWA ZALLAH HAR WATA SHIDA BAYAN HAIHUWA 
.

.
_Inganta Shayar da Nonon UWA Zalla har wata shida bayan Haihuwa:-_

1- Yana da amfani matuka a shayar da
jariri acikin mintuna talatin (30 minutes)
bayan haihuwa domin samun nono a lokacin da ya dace.

2- Ki tabbata kin shayar da nonon farko
mai kalar rawaya (dakashi) ko Colostrum a turance. Wannan zai iya kare jaririnki daga cuttuka.

3- Nonon Uwa yana iya bada isashshen ruwa tare da abinci da jariri yake bukata a tsawon watanni shida na shayarwa.

4- Ki guji hada nonon uwa da madara ko wani abinci, domin lafiyar jaririnki acikin watanni shida da haihuwa.

5- Idan zaki fita ko kuma yin nisa, kina da za6in matse nononki a mazubi mai tsafta domin shayarwa a yayin da bakya nan.

*・YADDA ZA A AIWATAR DA SHAYAR DA NONON ZALLAH・*

Ki tabbata kin fara shayar da jaririnki da zarar kin haihu cikin mintuna talatin da haihuwa.

*・MENENE SHAYAR DA NONON UWA ZALLA HAR ZUWA WATA SHIDDA???・*

Shayar da Jariri na tsawon wata shida; Ana nufin bada nogusauqa kadai batare
da ruwa ko koko ba.

1> Kike yawan hada jaririnki da jikin ki,
domin hakan na tabbatar da shayarwa mai kyau.

2> Kike yawan hada jaririnki da jikin ki,
domin hakan na kara wadatar nono.

3> Kike yawan hada bakin jaririn da kan nono, domin hana tsagewar nono da kuma kuraje a bakin nononki.

4> Domin tabbatar da haduwan jaririnki da nonon sai:-

- ki taba le6en jaririnki da bakin nononki.
- ki saurari bude bakin jaririnki.
- ki hanzarta saka jaririnki ga nono.
- ki tabbata jaririnki na shan isashshen
nono ya zamo sai ya saki don kansa.

*ALAMOMI NA KYAKKYAWAR HADUWA:*

a) Bakin jaririnki ya kasance a bude.
b) Le6en bakin yaro a waje kamar a nade.
c) ki tabbata leben ya ta6a nono.
Jaririnki zai tsotsi nono a hankali kuma cikin nutsuwa. Zai kuma kasance jaririnki bashi ba matsalar kumburin ciki.
Ruwa, ko madara, ko abinci ko kuma
wani abin sha. Ruwa ma sai dai nashan
magani bisa umarnin likita/ma'aikacin asibiti.

*ABINDA YA KAMATA KI SANI*

Kamar sau nawa ya kamata in shayar
da jaririna?

= Ki shayar da jaririnki a duk lokacin da ya bukaci nono dare da rana akalla sau 8 zuwa 12 a rana.

= Shayarwa akai-akai yana kara madaran nono.

= Ki ci gaba da shayarwa hatta nono ta kare, sannan, ki shayar da na biyu sai
jaririnki ya ki.

= Zaki iya sanin ko jaririnki a koshe yake
idan yana fitsari akai akai, kamar a kalla
sau 6 a rana, sannan kuma yana kara
nauyi.

= Ki samu ishashshen lokaci kuma ki kawo jaririnki kusa dake domin shayarwa.

*HANYOYIN DAZA A MAGANCE MATSALOLI YAYIN DA AKE SHAYARWA*

1- Ki tabbata kin rike jaririnki kusa da
nononki domin hana kaucewa ko kuma
tsagewan bakin nono, domin shayarwa bata da illa.

2- Yayin daki ka samu tsagewar bakin nonon, saiki shafa nono akan tsagun kada kisa man shafawa ko kuma
magani sai da izinin ma'aikacin lafiya.

3- Ki shayar da danki akai-akai domin ki
guji samun kumburin nonon.

4- Yayin da baki samu kin shayar da jaririnki ba, sai ki matse nonon domin kiss nonon yai laushi.

5- Kina da za6in ajiye ajiye nonon da
kika matse a waje mai sanyi zuwa tsawon awa shida 6 zuwa takwas 8.

6- Yayin da daya daga cikin nononki, ko
kuma duka biyun kanyi zafi ko ciwo idan an taba sai ki sami ma'aikacin lafiya a asibiti.

7- Ki bincika ko akwai kuraje abakin jaririnki. Idan kika ga akwai kuraje, saiki sanar da ma'aikacin lafiya.

8- Idan kina da matsalar shayar da jariri nono zalla har wata 6, to sai ki tuntubi shawarar kwarraren ma'aikacin lafiya.

*ABUBUWAN DA ZA'A LURA DASU*

1- Shayar da jariri nono yana inganta lafiyar uwa da jariri, da kuma kyautata lafiyar iyali domin cigaban kasa.

2- Shayar da nono zalla zuwa tsawon
wata shida yana taimakawa wajan hana
samun sabon ciki, muddin al'ada (period) bata zo ba.

Ki tuntubi
kwararren ma'aikacin lafiya da zarar kin
haihu.

3- Idan jariri ya rika wata shida, kici gaba da shayar dashi nono tare da bada
Karin abinci.

4- Ki lura da cutar. gudawa, da zazzabi,
da matsalar numfashi da rashin cin abinci ga jariri domin wadannan matsaloli ne da suke bukatar dubawa.

5- Idan mace tana da kanjamau (HIV)
kada ta shayar da nono idan bakin nonon Nada kuraje ko tsagu ko kuma
yana jini, don haka sai ta shayar dashi da nono mai lafiya, sannan kuma ta
matse nono daga Wanda yake da ciwo ta zubar.

6- Kamuwa da cutar kanjamau na kara
hatsarin kamuwar jariri wajan shayarwa;

yi jima'i ta hanyar amfani da kwaroron
roba akullum akan ka'ida.

7- Domin kare jaririnki yana da kyau kisan matsayinki akan kwayar cutar kanjamau ta hanyar yin gwajin (VCT).

8- Shayar da nonon uwa zalla na tsawon wata shida shima rigakafine na ciwon hanta.
.
```Allah ta'ala yasa mudace```
.
_Gabatarwa: *sadêêQ ทagogo {βlчпgч}*_
.
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_
*--------------------------*
*_​•Ga mai sha'awar shiga Zauren 📚Ana -muslim_​*📚
_*​ta whatsApp sai yayi cikakkiyar sallama tare da suna da Address nasa zuwa⬇ ga lambar mu*_​​​​   
      _*08093347777*_
 _*08085777555*_   
〰〰〰〰〰〰〰〰〰 _*Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ ɴα ғαcєвooк ѕαι α lαtsα ɴαɴ*_ ⬇
https://www.facebook.com/Ana-Muslim-Group-156263338266984/
        ​
Post a Comment (0)