BANBANCIN DIYA MACE, DA DA NAMIJI.
Wani Dattijo wanda Allah Ya baiwa 'ya'ya masu yawa ya ce; yau da gobe, nasan bambancin halayyar da Namiji 'ya Mace. Misali, in na farka daga barci aka ce wani cikin 'ya'yana yazo ya tarar ina barci, ya ce in na tashi a ce yana gaishe ni, ya tafi to, na san wannan da Namiji ne.
Idan ko aka ce ga wani yana jira sai na farka mu gaisa kome tsawon barcin nawa, to na san wannan 'ya mace ce cikin yaran nawa.
Idan naga an jingine buhun shinkafa an tafi, to wannan kyautar da Namiji ce. Amma in aka zubo dafaffiyar shinkafa a kwano aka sa ni a gaba, aka ce in ci, muna hira, to, wannan aikin 'ya Mace ne.
Idan aka aiko min shadda yadi goma mai tsada, aka ce in yi dinkin Sallah, na san wannan da Namiji ne ya aiko.
Amma Idan aka dinko min doguwar riga, aka kawo aka ce in gwada a gani ko tayi kyau? To wannan sai 'ya Mace.
Haka Idan zan je ganin likita, na ga an turo direba ya sauke ni, na san wannan daga da Namiji ne, amma idan naga anzo da A Daidaita, aka ce in taso mu tafi tare, to, wannan sai 'ya Mace.
Kuma idan Namiji ya biya kudin gado aka kwantar da ni a asibiti, a yi kwanaki ban koma ganinsa ba.
Amma'ya Mace zata bar gidan Mijinta ta tare a wajena tana faman jinya ta, da karbar ma su duba ni har sai an sallame ni.
A fahimta ta, 'ya'ya Mata basu taba rabuwa da iyayensu, kome wahala.
Amma 'ya'ya Maza sai dai abinda ya samu.
Namiji zai yiwa iyayensa kyauta da abinda ransa ya so, babu la'akari da abinda suke so, mace kuwa sai ta tambayi me aka fi so, kuma zata yi iya karfinta.
Kullum Namiji sauri ya ke yi a gaisa ya fice, Mace ko har jan lokaci ta ke a gidansu.
Sai kaga Namiji na wasan zagin uba, amma mace ko fada suke da Mijinta, zata ce ya fadi kome amma ya kiyayi ambaton iyayenta. Sai ka zagi Liman baban Namiji a zauna lafiya, amma mashayin Uban Mace ba ya zaguwa.
'Ya mace zata yi maka, ta sanya Mijinta yayi maka. Amma da Namiji Idan ba Matar kirki ya samu ba, yana iya mancewa da kai.
A Gaskiya diya mace Rahma ce!
Sutura ce!
'Yar halas ce!
Shin hakan ta ke ko a'a ?
Dr miskeeneey