# GAREKI_MASOYIYATA
Ya tauraruwar
dake haskaka
ilahirin bishiyoyi furannin
dake lambun
zuciya ta.
Nayi al-qawarin kasancewa
tare dake matuqar zuciyata tana
bugawa,
kin mamaye gurbin
zuciya ta
domin ke kadai nake gani, muryar kikadai
nake ji, kuma surar ki kadai
nake kallo.
A yau na mallaka miki furen
soyayyar mu
domin ki cigaba da kula da ita tare da
bata kariya.
Soyayyarki tadade da
daskarewa a
farfajiyar zuciyata, kamshin ta yana nan
yana cigaba da yaduwa a
birnin zuciyata.
Tabbas ! na sanya matakan
tsaro a kofar
zuciyata babu mai shiga sai da umarninki.
Masoyiyata Ke kadai ce
macen dake
haskaka zuciya ta tayi farifat.
yar autan
jimina, daya tamkar da
dubu,
kin yiwa
tsara zarra, sa gabanki
inda kike so
indai kina tare da ni. Farin wata kike sha kallo,
hasken rana kike
idan kika fito tafin hannu yai
kadan ya tare ki