GYARAN FATA A LOKACIN SANYI

*•••• GYARAN FATA LOKACIN SANYI •••••*


・ yana da kyau lokaci sanyi mu kula da kanmu domin yana da hatsari sosai.

Mussammman masu ( asma & sauran ciwo sanyi ).

Sanna mu kula da yaran mu sosai lokaci sanyi.

Kamar yadda mutane maza da mata suke fama da bushewar fata ayi ta faman sauya kalolin mayuka, cream, lotion,oil amma wasu basu fatar su bata yin dai-dai sai sanyi ya wuce! anan za a fara ganin wasu sunyi duhu wasu kuma adinga ganin kazantarsu, a fili. menene mafita? menene abin yi? da farko akwai gyare-gyare da dole sai mace ta kula dasu sosai a wannan yanayin duk da cewar daman Dole muyi gyara amma yanayin sanyi yana bukatar ninkawa musammam masu dry skin da combination,zan fara da Fata.
* idan za ayi wanka adaina amfani da ruwa me zafi yana lalata ya busar da fata adinga sanya ruwa me dumi,
*shan ruwa kamar kofi 10-12, a rana yana taimakawa wajen hana bushewar fata.
*a dinga amfani da moisturizer daban-daban akan kowacce irin fata, misali .lotion ko cream zai fi aiki akan dry skin.
*serum ko gel na combination skin ne.
*liquid (think toner) don masu oily skin.
*idan za'a kwanta barci a tabbatar an shafa moisturizer, ko da extra virgin olive oil ne, ko flax seed oil
*a zabi oil me kyau saboda yawanci oils sun fi aiki a iya hannu da fuska, misali. mineral oil, primrose ,Shea oil.
*shan green tea yana matukar gyara fata sosai!
*a hada 1tbs na Zuma da 1tbs na yoghurt a hada su wuri daya ashafa a shafa iya fuska kadai minti 15 a wanke, duk sati sau daya akwai sirrin fito da kyau a wannan hadin. kuma duk wata matsala ta fuska zata gushe.
*a hada ayaba da madara ta gari ashafa a jiki zuwa minti 20, sau 3 a sati, fata tana yin fresh.
GYARAN LEBE (LIP)
*idan za'a kwanta a dinga sanya lip gloss ko lip balms amma kada ayi amfani da me kunshe da pepper mint,ko menthol don suna sanya bushewar lebe.
*a hada glycerin da Zuma kadan a dinga shafawa kullum to lebe ba zai bushe ba.
*da yawan mata suna sanya lipstick da yawa to yana sa bushewar lebe kafin ki sanya lipstick ki fara sanya moisturizer ko lip balm, kuma wani sirri da lallai kun sani ba shine idan kina so lipstick dinki ya zauna tamkar dashi aka halicce ki ,kalar sa ta zauna sosai to ki fara goga powder kadan aleben naki ko foundation sannan sai ki dora lipstick hmm ...ba magana.
http://sirinrikemiji.blogspot.com/?m=1
Post a Comment (0)