3. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
...
Mandingo mutane ne masu dadin zama, masu son mutane. Galibinsu dogaye ne, samun gajere dukur a cikinsu da wuya, ga su da kokarin aiki da jure wahala. Matansu kuma kyawawa ne, masu son ado ga kuma fara’a. @bukarmada Su ke saka tufafinsu. Mazan su kan sa kaftani da wando iyaka kwauri, da farar tagiya da sambatsai. Matan kuwa tufafinsu biyu ne, da madauri da mayafi.
A cikin abu daya kurum na ga bambanci tsakanin kabiIun Afirka, shi ne wajen kallabi. Misali matan Gambiya wani dan kyalle su kan zagaya kansu da shi, su sauko shi gaban goshi kamar zai rufe musu ido. Mutanen Bondu kuwa wadansu irin fararen @bukarmada duwatsu su ke daurawa a kai a tsakiyarsa su sa zinariya. Na Koson kuwa su da farin kudi, wuri, su ke yi wa kansu ado. In sun shirya shi tantsai ai abin sai kallo! Amma mutanen Ka’arta da Ludamar su doka su ke yi mai bisa, ita ce adonsu.
A kowane gari akwai Sarki, da Alkali da gidan shawara. Duk inda ka tafi cikin garuruwan kasar za ka ga masallatai, za ka ga yara a zauruka, ko gindin bishiyoyi, suna karatun Alkur’ani. Amma an ce galibin mutanen kasar daga bayi ne sai magudantai. Na ga kasuwoyin bayi maza da mata. @bukarmada Im mutum yana bukatar bawa sai ya zo ya zuba kudinsa a sayar masa, ya tasa a gaba sai gida kamar ya sayi jaki. Ciniki bayi shi ne babban ciniki a wannan kasa ta Gambiya. Turawa iri iri suna zuwa daga Turai suna cikon bayi, suna sa su a jirgi su kai Amirka su sayar. An ce bawa ko baiwa, in suna da lafiya da kuruciya, a kan saye su £18 har £20. @bukarmada Dillalan bayi su kan shiga can cikin kasa su samo bayi, su kawo bakin teku su sayar, su yi cikon gishiri da duwatsun wuya su kai cikin kasa. Aikinsu ke nan rani da damina.
Babban abu mai wuya da na lura a cikin halin mutanen Afirka shi ne wajen ciniki. Na ga ba su yarda da kowa ba, suna zaton duk cinikin da kuka yi da su, ka saya ko ka sayar musu, @bukarmada cutarsu ka yi. Saboda haka maganarsu ba abar dogara ba ce. Ko sun ce sun saya, suna iya komo da hajjarka su ce sun fasa, haka in sun ce sun sayar, suna iya komowa daga baya su ce albarka.
NA TASHI DAGA GAMBIYA
Ran 2 ga watan Disamba 1795 na bar gidan Dr. Laidley, na tashi. Ba na mantawa da alherinsa da liyafa tasa har abada. Da zan tashi ya ba ni aron yaronsa @bukarmada Demba ya kuma yi mini hayar wani dan duniya, ana kiransa Johnson. Shi Johnson da bawa ne, har an kai shi Amirka. Daga can ubangijinsa ya ’yanta shi, ya kai shi Ingila. Ya ji Turanci, kuma ga harshen kasarsu, Mandingo. Demba kuwa bai ga duniya ba, amma yaro ne mai ban sha’awa, da son kwalliya. Bayan harshensa @bukarmada Mandingo, yana jin harsuna da dama na kasashen da za mu shiga. Su duka biyu muka shirya abin da zam biya su, aikin Johnson tafinta, Demba kuwa mai yi mini hidima. Ni na sami doki, wani dan kuru managarci, @bukarmada kakkarfa. Johnson da Demba na samam musu jakuna. Kayana ba yawa ba ke gare su, daga abincin kwana biyu sai ’yan duwatsun wuya, da amba (wani irin daskararren karo mai ado), da ganyen taba, don an ce wadannan su ne abin da mutanen kasar suka fi so. Daga wadannan sai tufafina, da laima, da ma‘aunin jiha, da kananan bindiga biyu; da sauran ’yan tarkacena kadan. Dr. Laidley ya yi mini rakiyar tafiyar kwana biyu. @bukarmada
Kafin mu tashi, muka yi sa’a wani mutum wai shi Modibbo zai tafi kasar Bambara, wadansu fataken bayi kuma su biyu za su tafi fataucinsu a Bondu. Su kuma nan suka yi alkawarin za su taimake @bukarmada mu har inda hanya ta raba mu. Su a kasa su ke tafiya, suna kora jakunansu. Dukansu suna dubana da girma kwarai, suna kuwa kula da ni. Am fada musu in suna so su sake komawa kasar Gambiya, lalle kuwa su lura kada su bar wani abu ya cuce ni. Ran da muka tashi muka sauka a Jinde. @bukarmada Da yamma ta yi, muka fita yawon shan iska har wani dan kauye. A can muka tafi gidan wani farken bayi da a ke kira Jemafu Muhammadu, wanda aka ce ya fi duka farken da ke kasar Gambiya arziki. Ya yi murna da ganimmu kwarai, nan da nan ya sa aka ba da wani hurtumin sa aka yanke mana.
Bisa ga al’adar Bakar Fata, ba su cin abincin yamma sai can dare. Saboda haka kafin @bukarmada a kare soye-soyen nama da dafe-dafe, sai muka ce da wani Mandingo ya ba mu wani Iabari. Ya shiga bayarwa, mu kuma muka kasa kunnuwa muna ji. Labarun suna da dadi, don kuwa mun yi sa’a uku ba mu ankara ba. Suna da kama da Iabarun Dare Dubu Da Daya. Har ma ga daya daga cikinsu a takaice :
“Wata rana a zamanin da, zaki ya dami mutanen wani gari na bakin Kogin Gambiya da a @bukarmada ke kira Damasansa. Duk dare zakin nan ya kan zo ya kame musu sa. Da dai barna ta yi yawa, sai tsoro ya fita daga zuciyar mutane, suka daura niyya za su fake shi su kashe. Suka bazu a daji, har suka same shi yana kwance a wata ‘yar duhuwa. Da ganinsa suka kwarara masa bindiga, ya yi tsalle zai fada kansu, sai ya fadi. Amma ganin yadda zakin nan ya yi fushi, yana huci a kwanoe, babu wanda ya iya zuwa kusa da shi. Ga shi kuwa sun yi niyya su kama shi @bukarmada da ransa ne, su kai shi bakin teku, su sayar wa Turawn. Im ba da rai suka kai shi ba, ba zai yi kudi da yawa ba. To fa, ga kudi ga halaka! Suka shiga kawo dabarun kama shi, amma ba wadda ta fita. Sai wani dattijo cikinsu ya kawo wata dabara. Ya ce su je gari su kware jinkan wani daki, su dauko tsaikon su jefa a kan zakin su rufe shi da shi. In kuwa ya taso musu a lokacin da suka zo kusa da shi, to, sai su shiga cikin tsaikon su @bukarmada harbe shi daga ciki.
"‘Yan‘uwana suka ce ai kuwa wannan dabara za ta fita, sai a jarraba. Suka kware daki, suka dauko tsaiko. Kowanensu yana rike da bindiga da hannu daya, hannu daya kuwa yana tallabe da tsaikon. Ta haka suka tasam ma zakin. Amma, a lokacin ya fara murmurewa daga zafin harbin da aka yi masa, sai ya taso musu @bukarmada haikan yana ruri. Maharban nan suka tsorata, suka ga dai babu abin yi sai su shiga tsaikon nan, tun ba su yi kusa da zakin ba. Suna cikin sauke tsaiko, su dai ba su yi aune ba, sai ga zaki a tsakiyarsu, sun shiga tsaiko tare da shi. Zaki ya banke su duka, ya kakkarya su ya kashe, ya cinye. Mutanen Damasansa suka firgita. Har @bukarmada yanzu kuwa bu su sake karambanin kama zaki da ransa ba."
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.wordpress.com/
http://bukarmada.blogspot.com/
bukarmada@hotmail.com
BBM: 2bddd505
BBM: d1d74969
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada