MUNGO PARK MABUDIN KWARA 08



8. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
bukarmada.blogspot.com
...
Amma abin mamaki shi ne ko sa'a biyu ban yi ba da shiga Sulo ashe har labari ya kai kunnen Sarkin Koson a Kunyakare. Muna zaune sai ga Sambo, dan Sarkin ya ce wai ubansa ne ya aiko shi ya ji dalilin da @bukarmada ban tafi Kunyakare ba, na toge a Sulo. Salim Daucari ya ba shi magana, ya ce ya je ya gaya wa ubansa ga mu nan tafe da maraice. Rana na sunkuyawa za ta fadi, sai muka tashi har da Salim Daucari sai Kunyakare. Kafin mu isa, Sarki ya shiga gida ya kwanta, @bukarmada saboda haka ba mu gan shi ba sai da safe. Sambo Sego ya kai mu gidansa, muka kwana.
SADUWATA DA SARKIN KOSON
Misalin karfe 8 na safe, ran 15 ga Janairu, 1796, na tafi gaban Sarkin Koson, Demba Sego Jalla. Mutane sun taru a kofar fadar, kowa yana so ya gan ni, sai da kyar na sami hanyar shiga. Na tafi gaban Sarki, na dukad da kaina na gaishe shi. @bukarmada Na same shi a zaune bisa tabarma a cikin wani babban daki. Dattijo ne, shekarunsa sun kai misalin sittin. Kuma an ce jarumi ne wajen yaki, kuma karimi ne, saboda haka talakawansa suna sonsa kwarai. Ya yi mini duban tsanaki, ya tambayi Salim Daucari, farken bayi mai masaukina, inda zan tafi, da irin abin da na ke nufin yi a kasar Bakar Fata. @bukarmada Da Salim ya gaya masa na tafo don ganin kasar ne kurum, da irin halin zaman mutanenta, nan da nan ya yarda, ya kuma yi alkawarin zai ba ni 'yan rakiya har zuwa kan iyakar kasarsa. Ya gaya mini sun sadu da Manjo Houghton, har ya ba shi doki kili. Amma bayan ya wuce kasarsa ya shiga ta Larabawa, an ce sun kashe shi.
Bayan mun dan yi magana da Sarki sai ya sallame ni, na komo masaukina. Da na komo na shirya 'yar kyauta daga dan abin da ya rage cikin kayana, na aika masa. A lokacin ba ni da kome, don ban rigaya na karbi kayan da Dr. Laidley ya aiko Salim da su ba. @bukarmada Da aka kai wa Sarki ya yi murna kwarai, ko da ya ke kyautar ba ta da yawa. Shi kuma ya aiko mini da hurtumin bajimin sa fari.
Salim Daucari ya ba ni zinariya da bawa uku cikin abin da Dr. Laidley ya ce ya ba ni. Na ji karfi-karfi, don na sami abin yi wa sarakunan da zan shiga kasashensu gaisuwa ke nan. Amma ina kafin kwana biyu labari ya bazu duk gari wai Salim Daucari ya ba ni zinariya da yawa. Labari ya gangara har kunnen Sarki. Ran nan ina zaune, sai ga Sambo Sego, dan Sarkin, ya zo tare da wadansu bisa dawaki. Ya ce ya ji na sami zinariya, saboda haka yana son ya san yawansu, kuma ko nawa ne, lalle im ba Sarki rabi. Kuma lalle in yi wa masu dawakin da ke tare da shi dan alheri, don kuwa duk 'yan'uwan Sarki ne, shi kuma yana son nasa rabon. Da jin haka sai na tsorata, don kuwa na san irin abin da zai auku im ban yi musu yadda su ke so ba. Duk da haka dai na shiga rarrashi, na nuna musu ni bako ne, ba ni da kowa, ba ni da mai kare ni sai su sarakuna. Amma a banza. Zuwa can Salim Daucari ya shiga ba dan Sarkin nan @bukarmada magana, da kyar ya ciwo kansa. Ya ce da Sambo zam ba shi 'yan kudi, kuma zam ba shi albarushi. Ya karba, suka juya.
Da safe, ran 1 ga Fabrairu, sai ga mutum biyu Sarki ya turo su daga birni, su zo su raka ni har zuwa kan iyakar kasarsa. Na shirya, muka yi sallama da Salim Daucari na tashi. Muka yi kwanaki muna tafiya. Muka wuce Karankalla, sai Kimu. Tsakanin Karankalla da Kimu muna tafiya sai na ratse daji don in debo 'ya'yan itace na marmari. Ashe na saki hanya da nisa ban san daidai inda mutanena su ke ba. Na rasa abin yi, ga ni ni kadai a kungurmin daji. Can sai na hangi wani tudu, na ce bari in je in hau in hanga, kila na hango mutanena. Na doshi tudun ke nan sai ga wadansu masu dawaki su @bukarmada biyu a sukwane kowane da bindigarsa. Da ganinsu gabana ya fadi, sai na ja linzamin dokina. Su kuma sai na ga sun ja. Hankali bai komo mini ba sai da na ga ashe su ma tsoro suka ji da ganina, kila ba su taba ganin mutum da farar fata kamar tawa ba. Sai na yi kaimi na matsa gaba, sai na ga daya ya firgita ya tausa linzami, ya sheka daji a sukwane. Gudun kuwa kila ma ya suma ne saboda tsoro, don dai ya ga ina matsowa wajen da ya ke sai ya rufe idonsa da hannuwansa, yana ta addu'o'i, bai san lokacin da dokinsa ya juya da @bukarmada shi ya nufi inda dan'uwansa ya nufa ba. Can sai suka gamu da mutanena a hanya, suka ce musu sun ga wani aljani a daji, fatar jikinsa kamar takarda ta ke don fari.
Suka fa shiga kara wa labarin nan gishiri, suka ce aljanin nan da suka gani ba shi da iyakar tsawo, duk jikinsa kuwa rufe ya ke da doguwar riga. Suka @bukarmada ce ta wajen da na bullo, wai suna jin wata iska mai karfi, da sanyi ta yi ta saukowa bisa kansu kamar ana sako musu ruwa.
Da na hau tsaunin, na hanga, na sake hangawa, sai da kyar na ga mutanena can sun yi nisa. Na gangara, na yanki daji, na cim musu, muka mika. A nan ne suka shiga fada mini irin labarin da mutanen nan suka gaya musu.
Da shigarmu Kimu sai na nufi fada. Amma kafin in kai kofar fadar mutane suka rufe ni, suna bi na da kallo. Ko dokina da kyar ya ke samun wurin takawa saboda yawan mutane. Sarki ya aiko in tafi masauki. @bukarmada Ya kuma ce a hana mutane bi na. Mutane ba su bar ni ba dai, suka bi ni har daki, Ga shi na gaji, ina so su bari in dan kwanta ma im mike, suka ki.
Da maraice Sarki ya aiko, na tafi. Bayan mun gaisa na gaya masa irin abin da ke tafe da ni, kuma da taimakon da na ke so ya yi mini don im fice kasarsa lafiya. Ya ce, "Haka ne. Amma ba na iya yi maka yadda ka ke so domin muna cikin yaki ne da kasar da ke gaban tawa, wadda za ka shiga.@bukarmada Mansong, Sarkin Bambara, ya zo har kan iyakarmu, yana niyyar zuwa nan da yaki. Saboda haka hanya ba ta biyo. In kuwa ka yanki daji, za ka gamu da namun daji, ko mutanen Bambara su kama ka, su ce dan rahoto ne, su kashe ka. In suka yi haka kuwa. mutanen kasarku za su zarge ni, su ce ni na kashe ka. Don haka na ba ka shawara kada ka ci gaba, kada ma ka tsaya a garin nan, sai ka yi maza @bukarmada ka koma Koson, ka dakata a can sai yaki ya jare. Tsananin yakin dai duka wata uku ne, bayan lokacin nan, in ina da rai, sai im ba ka dan rakiya, in kuwa an kashe ni 'ya'yana sa taimake ka."
Wannan lalle shawara ce ta kirki kuma abin da ya same ni duk ni ne abin zargi. Amma ni na gaya masa tun da na rigaya na dauko alkawarin wannan aiki daga wurin manyana a gida, lalle ba shi yiwuwa in koma da baya. Muna cikin zama, sai ga wani mai doki ya zo a sukwane, ya ce ga Sarkin Bambara nan ya tasam ma Ka'ata da mayaka @bukarmada ba iyaka. Da jin haka Sarki ya sallame n i, ya ba ni 'yan rakiya wadanda za a kai ni har kan iyakar kasa tasa, su kuma sa ni a hanya mai lafiya.
Muka yi sallama, na tashi Kimu. Muka yi ta tafiya har muka kai wani gari wai Funinkedi. Da muka doso garin, mutane duk suka firgita, don suna tsammani Larabawa ne suka zo hari. Amma sai muka yi sa'a muka sami wani farken bayi wanda ya kan tafi har Gambiya, ya saba ganin Bature. Muka sauka a @bukarmada gidansa. Ya gaya mana hanyar gabammu ba ta da kyau, saboda yawan fashi na Larabawa.
Su Larabawa din nan 'yam fashi ne kwarai, kuma mutane suna tsoronsu da gaske. Har ma ran nan ina barci a kan kilagon sa da azahar, sai na ji ihu, da kara. Na farka firgigi, na ji gari duk ya yamutse. Ni ma da ina ce mutanen Bambara ne suka kawo yaki. Sai na hango yarona a kan rufin wani daki yana kallo. Na tambaye shi, ya ce wai ai Larabawa @bukarmada ne suka zo satar shanu. Na hau bisa kan wani daki sai na hango Larabawan nan tafe suna kora shanunsu. Da suka iso daidai inda dangwalin mutanen garin ya ke, suka zabi shanu masu kyau guda goma sha shida suka hada da nasu, suka kora. Duk abin nan kuwa ga mutanen garin sun yabe kan ganuwa suna ganinsu, amma ba su ce musu kome ba. Kamar sau uku ko sau hudu kadai na ga sun harba bindiga, ko shi ma kuwa da ya ke albarushi ne kurum sai @bukarmada hayaki wofi ya tunnuke.
Zuwa can sai na hango wadansu mutane sun taitayo wani yaro a bisa doki sun nufo gari da shi. Ashe dan kiwo ne ya yi kokarin hana Larabawan nan kwance shanunsa, su kuwa suka harbe shi da bindiga. Mutane suna rike da yaron ga uwarsa kuma a gaban dokin, ta rude ta firgice, ta sa hannu a kai, tana rausa kuka, Sai yabon danta ta ke yi tana cewa, "maffo foniyo". Wai "bai taba karya ba." Aka dai @bukarmada shigo da shi gari, aka kai shi gidansu, nan da nan mutane suka kewaye shi, suka rude da kuka.
Bayan dan jimawa, sai aka ce in zo in duba raunin ko kila na iya taimako. Da na je na duba, na ga abin dai babu kyaun gani. Harsashi ya fasa kashin kwauri ya ratattaka shi har ya hurce. Jini sai kwarara ya ke yi, yaron kuwa yana kwance sumamme. Na ga dai lalle ba @bukarmada zai rayu ba, saboda yawan jinin da ya zuba daga jikinsa. To, gudun kada im fada wa 'yan'uwansa haka hankalinsu ya tashi, sai na ce mikin nan da harsashi ya yi masa ba ya warkuwa. Maganinsa daya ne sai a yanke kafar.
Da fa suka ji haka wayyo ni, ai sai ka ce na zuba musu garwashi. Suka kuwa yiwo ashashan bisa kaina. Kowa na fadin albarkacin bakinsa, mai zagi na yi, mai bakar magana na yi. Wadansu ma suka @bukarmada ce sun ji Nasara suna cin mutum, wai shi ya sa na ke so in cire kafar wannan yaron don in ci.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
bukarmada@hotmail.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)