9. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
bukarmada.blogspot.com
...
Da fa suka ji haka wayyo ni, ai sai ka ce na zuba musu garwashi. Suka kuwa yiwo ashashan bisa kaina. Kowa na fadin albarkacin bakinsa, mai zagi na yi, mai bakar magana na yi. Wadansu ma suka @bukarmada ce sun ji Nasara suna cin mutum, wai shi ya sa na ke so in cire kafar wannan yaron don in ci.
Suka ce su ba su taba jin wannan irin hanya ta warkad da mai ciwo ba. Nan da nan suka ture ni, suka kore nidaga kan yaron. Sai suka kira wadansu malamai, suka zauna kusa da yaron, suna ta addu'a a kansa. Da malaman nan suka ga alamar ajalinsa ya kusa sauka, sai suka sa shi ya yi kalmar @bukarmada Shahada, yana gamawa sai ya cika. Kashegari kuma sai na bar garin.
NA SHIGA KASAR LARABAWA
Kila duk cikin labarin tafiyata babu abin da ya fi dadin ji kamar shigata kasar Ludamar, da haduwata da Larabawa mutanen kasar. A nan na sami labarin Manjo Houghton, da yadda mutanen kasar @bukarmada suka washe shi, suka bar shi a daji, yunwa da kishi suka kashe shi.
Na ji wai da ya zo Jarra sai ya sadu da wadansu Larabawa fatake. Suka ce masa hanyarsu guda ce, don su za su tafi Tishit ne, wani gari na tsakiyar hamada inda a ke samun gishiri. Sai Manjo Houghton ya yi tsada da su su tafi tare da shi, maganin 'yam fashi, ya ba su bindiga da ganyen taba ladansu. An tabbata Larabawan nan sun yaudare shi ne. Niyyarsu su washe shi ne, su bar shi a cikin hamada ya mutu. Haka kuwa aka yi. @bukarmada Don bayan sun yi tafiyar kwana biyu sai ya gane niyyarsu, ya ce zai koma Jarra. Da suka yi suka yi da shi ya ci gaba ya ki, sai suka kwace masa kayansa kaf, suka bar shi daga shi sai ransa. Ganin haka bai yi kokarin yin gaba ba, sai ya komo a Rasa har zuwa wata rijiya ta Larabawa, ana kiran wurin Tarra. Ya yi kwanaki ba ci ba sha kafin ya zo nan, saboda haka da ya sami Larabawan nan suna diban ruwa sai ya roke su. Ga kishi kamar zai kashe shi, amma suka hana shi ko makwarwa guda ya hadiye, Daga nan ne ya ba da zuciyarsa ga mutuwa. To, ko fa yunwa da kishi suka kashe shi, ko kuwa Larabawa ne suka yanka shi, Allah @bukarmada kadai ya sani. Amma an ga gawarsa an yar cikin daji daga gefen hanya. An nuna mini wurin da ya mutu, na gani da idona.
Kasar Ludamar babbar kasa ce, kuma Larabawa su ne sarakunanta, amma mutanen kasar bakake ne. Da shigata kasar, sai na sauka a wani babban gari da a ke kira Jarra. A lokacin nan ba ni da kome. Amma wanda na sauka a gidansa wani farken bayi ne ana kiransa Daman Jumma. Ya saba zuwa Gambiya, kuma ya san Dr. Laidley. Har da zan taso Dr. Laidley ya ba ni takarda in kawo masa, don ya ba ni wadansu kudi da ya ke binsa. Ya biya ni rabin abin da ya gani a takarda, ya kuma yi mini @bukarmada taimako da shawarar yadda zan ketare kasar Larabawa.
Na ce ya aika a gaya wa Ali zan shige ta kasarsa, saboda haka ina neman izni. Na ga ba shi yiwuwa in sami biyan bukatata da baki kurum, sai na hada da kaftani shudda guda hudu da na saya gun mai masaukina, na ce gaisuwata ke nan. Aka yi kwana kamar goma sha hudu dan sako bai komo ba. Sai ran nan ga shi tare da wani Jakada, wai Ali ya @bukarmada aiko shi ya nuna mini hanya, ya fid da ni har iyakar kasarsa. Shi Jakadan kuma ya ce ba zai cika wannan umurni na ubangijinsa ba, sai na kawo wani abu na ba shi. Sai na ba shi riga guda, muka yi niyya. Ga mu nan sai wani gari wai shi Dina.
Galibin mutanen Dina duk Larabawa ne. Da ganina suka kewaye ni a dakin da na sauka tare da Jakadan Ali. Daga nan na shiga shan wulakanci irin wanda ban taba gani ba a duniya. Ga ni mutum ne dan'uwansu, amma abin da suka yi mini, ko kare ka ji tausayin @bukarmada yi masa. Mai harara na yi, mai tsaki na yi, mai ihu na yi, mai zagi na yi. Kai, wadansu dai har kaki su ke yi su tofa mini a fuska, wai dai don in yi fushi, su sami hanyar kwace kayana.
Suka ga wannan bai ci ba, sai suka ce to, ai ni Kirista ne, saboda haka dukiyata halas ce ga jama'ar Annabi Muhammadu. Da fa suka rike wannan hujjar, suka kuwa shiga wargaza kayana, haba, abin ai sai wanda ya gani. @bukarmada Suka yi mini karkaf, ba su bar ni da kome ba, sai abin da ba su so. Shi kuma wanda ya ce Jakadan Ali ne, shi ko ganinsa ban sake yi ba, ashe da ma ya kawo wa kuraye 'yan'uwansa abinci ne.
A nan ne fa, ganin yadda na sha waso haka, sai yarana duka, har Johnson tafintana suka yi mini bore. Suka ce daga nan Jarra in sun cira kafarsu baya za su yi, su koma Gambiya. Na yi ban maganar, na yi rarrashin na yi musu alkawarin karin ladansu, amma a banza, ba su yarda ba. @bukarmada Ko da ma sun rigaya sun firgita da irin abubuwan da suka same mu kafin mu kawo Dina, balle yanzu da suka ji labarun Larabawa. Amma ni ban zarge su ba, don kuwa Larabawa ba su da kyau. In sun tsare mu a daji, za su yi mana kaca-kaca ne, balle ba su ga wani abin kirki a kayammu wanda za su dauke ba, kashe mu za su yi, ko su kama mu su bautar. Kutsa kai cikin halaka irin wannan. kuwa ya fi karfin mutumin da ya ke aiki don kudi kawai. Aiki ne na mutumin @bukarmada da ke da wani kishi a zuciyarsa na taimakon jama'a ko yaye wa kansa da sauran duniya duhun jahilci.
Saboda haka muka yi sallama da su. Na rubuta labarin tafiyata duka, da abubuwan da na gani a Afirka, tun daga Gambiya har Dina, na ba Johnson, na ce ya kai wa Dr. Laidley. Amma kofe biyu na shirya, na daya gare ni, don ko wancan ya bata, wannan yana nan. @bukarmada Suka juya, ni kuma na yi gaba ni kadai daga ni sai raina.
Na tashi Dina, ni kadai, har na yi dan nisa, sai na ji kira daga baya. Da na waiwaya, sai na ga ashe yaron nan nawa ne Demba. Dan kirki ya ga da ya ci amanata ya bar ni ni kadai, gwamma ya bi ni, in kamu kamu, in kisa kisa. @bukarmada
Da ya zo, ya ba ni labari wai Jakadan nan na Ali ya koma Benaum don ya fada wa Ali, babban Sarkin kasar Ludamar, cewa ga ni zan tsere. Da jin haka na san tafiya ta baci. @bukarmada
Muka dai yi ta tafiya har Dalli. Na sauka gidan wani mutumin kirki. Ya yi mini liyafa mai kyau, abinci sai wanda na ke so za a kawo mini. Muka tarar ran nan garin ana biki, sai kade-kade da algaitu ke tashi. Hankalina ya kwanta, na fara sakin zuciya game da tsoron Larabawa. Duk na kosa in kai Gumba, saboda haka, ko da ya ke akwai mutanen Dalli masu @bukarmada zuwa can, ban iya tsayawa in jira su ba. Sai na ci gaba, na isa wani kauye da a ke kira Sami. Ashe kaddara ke kirana. Na sauka a gidan Sarkin garin, ya kuwa karbe ni da murna ya yanka tumaki biyu, ya shirya dina domina, ya gayyato abokansa.
Kashegari kuma haka. Don murnar saukad da bakon Bature, mai masaukin nan nawa bai bari na tashi da safe ba, sai ya ce im bari sai da maraice rana ta yi sanyi. Ni kuma da ya ke na ga sauran tafiyar kwana biyu ne kurum im fita kasar @bukarmada Ludamar, ban kula ba. Muka yini ran nan muna ta nishadi da bakaken mutanen nan. Hakika na ji dadin zama da su kuma na tabbata zuciyarsu tana da taushi, da son mutane. Kai, don jin dadin hirarmu da mutanen nan har na manta da tsoron Larabawa, zuciyata ta dauke ni @bukarmada sai bakin Kwara, wai ga ni a bakin wannan kogi ina kallon ruwa!
Ina cikin wannan mafarki, kwaram sai muka ji kofaton dawaki sun nufo mu a sukwane. Ashe Larabawa ne. Da suka shigo dabin, suka ce mini Ali ne ya aiko su su tafi da ni, ta kowane hali. In na bi su, shi ke nan, amma in na ce zan yi gardama, an ce su dauke ni a ka su kai. Tsoro ya rufe ni, har na kasa ce uffan. Suka ce mini amma kada in tsorata, @bukarmada domin abin da ya sa Ali ke son ganina wai matarsa ce Fatima ta ce tana jin labarin Nasara, amma ba ta taba ganinsu ba. Saboda haka, da suka ji ina cikin kasarsu, ta ce tana son in tafi ta gan ni. Da dai na ga jayayya da tirjewa duka ba su yiwuwa, sai na bi. Suka tasa ni da yarona a gaba sai ka ce fursuna, sai Dina, garin da dan Ali ke zaune. Muka same shi da mutanensa @bukarmada suna alwala, suna shirin salla. Na yi gaisuwa, amma ko dubana bai yi ba. Maimakon amsa gaisuwar sai ya jefo mini wata tsohuwar bindiga, ya ce in gyara masa. Na ce da yarona Demba, wanda ke mini tafinta, ya gaya masa ban san yadda a ke gyaran bindiga ba. Da jin haka sai ya ce karya na ke yi, sai da kyar dai ya yarda. Amma ya ce im ban iya gyarar bindiga ba, to, sai im ba shi wuka da almakashi. Na ce a gaya masa ba ni da irin @bukarmada wadannan abubuwan. Yaronsa bai gama rufe baki ba sai muka ga dan Sarkin nan ya suri wata bindiga, ya dura harsashi ya dana.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
bukarmada@hotmail.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada