15. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
bukarmada.blogspot.com
...
Na ga kogin nan na Kwara wanda duniya ke ta nema shekara da shekaru, ruwansa sai walkiya wal wal wal ya ke yi a cikin rana, fadinsa sai ka ce Kogin Thames a Westminster, yana gudu yana nufa gabas. Na yi sauri na tafi gabarsa, na durkusa na kafa baki na sha ruwan. Sa'annan na daga kaina sama, na gode wa Sarki Mai kowa da kome, da ya ba ni ikon ida nufina na kai ga bukata, wahalata ba ta zama ta banza ba! Na debe kowace irin shakka yanzu, na tabbata Kwara ta fito yamma ne ta nufi gabas.
Amma ganin Kwara tana fitowa yamma ne tana nufar gabas bai ba ni mamaki ba, ko da ya ke wannan yana cikin abubuwan da na zo in tabbatar. Kafin im fito daga Ingila lalle ban san sahihin inda ya nufa ba, kuma ba wanda ya sani. Amma tun zuwana Afirka, na yi ta tambayar mutane, kowa kuwa sai ya ce mini “Kwara tana nufar inda rana ke fitowa ne.”
Bayan na kare kallon Kwara, sai na tasam ma shiga Birnin Sego. Garin an raba shi hudu ne gungu gungu. Gungu biyu suna gabar arewa, biyu suna ta kudu. Kowane gungu an kewaye shi da ganuwa mai tsawo. Gidajen garin duk soraye ne, har akwai benaye an shafe da farar kasa. Ko’ina akwai masallatai masu kyau, ga gidajen a jere tantsai, titi titi. Birnin Sego yana da ban sha’awa, ga mutane cikinsa makil, ga gine-gine masu kyau, ga gonaki a kewayensa manya, ga jirage sai kaiwa da komowa bisa kogi. Kai, babu dai wanda zai zaci za a sami wuri irin haka a tsakiyar wannan rufaffiyar kasa ta Afirka.
Amma Sarkin yana zaune a daya daga cikin gungun na kudun ne, mu kuwa muna daga na arewa. Da na nemi shiga jirgi don in ketare in tafi wurin Sarki, sai wani yaronsa ya gaya mini wai Sarki ba ya bukatar ganina. Kuma bai yarda in kwana a garin ba, amma zai tambaye ni dalilin shiga kasa tasa a gobe. Sai aka nuna mini wani dan kauye arewa da gari, aka ce in tafi can in sauka. Da na tafi, na zaga gidajen garin duk, amma babu wanda ya yarda ya ba ni wurin sauka. Suka zaci ni dodo ne, ba mutum ba, duk inda na nufa sai ciri. Na roki ma abin da zan ci, suka hana ni. Har rana ta fadi ban sami wurin kwana ba, ban kuwa sa hatsi a baki ba tun safe. Yunwa ta ci karfina, sai na fadi a gindin wata itaciya. Da na ji barci yana alamar daukana, sai na yi niyyar hawa itaciyar, don kuwa akwai kuraye a wurin.
Ina cikin wannan shawara, sai na hango wata mace ta fito gona. Da ta iso wurina, ta tsaya ta dube ni. Ta ga dai alamar na gaji, kuma ina cikin wahala, sai ta tambaye ni abin da ya same ni. Na kwashe labarina duk na fada mata. Tausayi ya kama ta, ta danki sirdina da linzami, ta ce im bi ta. Ta kai ni har cikin dakinta, ta kunna fitila, ta shimfida mini tabarma ta ce in kwanta. Zuwa can ta zo mini da gasasshen kifi, na ci na koshi, na sha ruwa. Bayan na kintsa, ta ce in kwanta in huta. Da ita da sauran iyalan dakinta kuwa suna can gefe guda na dakin, sun sa fitila a tsakiyarsu, suka shiga kadi. Suka dinga kadi suna waka har wajen tsakar dare. Ashe wakar ma tawa ce. Daya daga cikinsu ta ke sa wakar, sauran suna amsawa. Ga abin da su ke rerawa :
“Wannan Nasara abin tausayi ne,
Ya zo kasarmu da gajiya da yunwa.
Shi ba uwa mai ba shi nono,
Kuma ba shi mata mai nika masa dawa !".
Sauran matan kuma sai su amsa baki daya, su ce: “Lalle mu ji tausan Nasaran da ba shi da uwa !"
A wurinka mai karanta wannan littafi, wannan waka ba wata abu ce muhimmiya ba. Amma a wurina da na rabo da kasarmu, na rabo da ’yan’uwa, da masoya, na zo cikin tsakiyar Afirka, ba ni da kowa, ba ni da kome wanda zan rudi mutane da shi, ba ni kuwa da karfin tsare kaina, wannan taimako na tsohuwan nan ba kadan ba ne. Ya wuce alheri, ya wuce karimci, ya wuce agaji. Kai, ya fi kome a duniyan nan !
Da gari ya waye, sai ga yaron Sarkin Sego da wata katuwar jaka ya zo ya mika mini. Da na buda sai na ga farin kudi,watau wuri, har dubu biyar. Ya ce Sarki ne ya aiko shi ya kawo mini sallamata da shi ke nan, dan in rika sayen abinci a hanya. Amma in tashi daga kasa tasa, ya sallame ni. Yaron Sarkin ya ce wai an gaya wa Sarki duk irin halin da na ke ciki, saboda haka ya taimake ni, don ba daidai ba ne Sarki ya ki taimakon wanda ke cikin wahala. Jakadan ya ce amma Sarki ya ce ya raka ni har ya fisshe ni daji, kada ya bar ni sai ya kai ni Sansandin.
Na yi mamakin wannan abu da Sarki ya yi mini, ga shi ya ki ganina, amma ga shi kuma ya yi mini alheri. Na tabbata kowa ya dube ni, ya ga yadda na ke, ba zai yarda ganin Kwara kurum ya sa na kutso kai cikin wannan hadari ba. Don ko shi dan rakiyata, da muna tadin a hanya, sai dariya ya ke yi yana cewa akwai dai abin da ya kawo ni, ba na so ne a sani. Amma in don kogi ne, a kasarmu babu kogi? Ko kuwa duk kogi ba kamarsu daya ba ne ?
Amma duk da wannan shakka da ke zuciyar wannan Sarki, da kulle-kullen da Larabawa suka yi don ya cuce ni, irin alherin da ya yi mini ke nan. Na yi godiya, na shirya, muka yi sallama da tsohuwan nan ta kirki, na tashi. Da na rasa abin da zam ba ta, sai na balle maballan rigata biyu na ba ta. Ta yi murna kwarai, muka yi ban kwana. Ba na manta ta har abada, tsohuwar arziki!
Da na tashi daga Sego, babban garin da na fara isa shi ne Kabba. A can na fara ganin man kadanya da yadda a ke yinsa. Daga Kabba sai Sansandin.
Shi Sansandin gari ne babba, da mutane kamar dubu goma a ciki. Amma na ji wai gari ne wanda ba ya rabuwa da Larabawa, don kuwa masafarta ce babba. Saboda haka sai na ce da dan rakiyata ya bi da ni ta sako, yadda za mu isa masauki ba tare da mun ratsa gari ba, balle Larabawa su gan ni. Na tabbata in sun gan ni za su kashe ni, ko su kama ni, ko da ya ke kasar ba tasu ba ce, Bakar Fata ne Sarkinta. Muka yi ta zaga bayan gari har dai muka isa kofar fada.
Da isarmu, gari ya faso, mutane ba iyaka suka rufe ni. Ashe ko da ya ke mutanen garin sun dauke ni kamar Balarabe ne, amma su Larabawa da suka gan ni sun gane ni Nasara ne, shi ya sa wannan taron. Larabawa da ke garin fa duk suka keto, kura ta ga nama, sun sami abin da su ke so. Suka kore mutane nesa, su kuwa suka zo wurina, suka shiga nuna mugun halin nasu. Suka ce wane addini na ke bi, na ce musu ni ba Musulmi ba ne. Sai suka aika aka kira wadansu Yahudawa da ke garin, suka ce su yi magana da ni, kila na ji harshensu. Su Yahudawan nan, ko da ya ke sun Musulunta, suna salla, suna azumi da zakka, kuma Alkur’ani shi ne littafinsu, amma duk da haka a wulakance kowa ke dubansu, Bakar Fata da Larabawa. Don tsananin wulakanci har sun ce mini ko da ya ke ni Kirista ne, amma darajata ta fi ta Bayahude a wurin Musulmi.
Da na ce ba zan yi kalmar shahada ba, sai wani Sharifi ya taso. Ya rantse ya ce im ban tafi masallaci an yi mini wankan Musulunci ba, za su dauke ni a ka su kai, ko da halin kaka. Kai, babu dai irin abin da ba su yi ba, babu kuwa irin zagin kazantar da ba su jeho mini ba.
Ana cikin wannan harmutsi, sai Sarkin Sansandin, ana kiransa Kunti Mammadi, ya fito. Ya ce musu su rabu da ni, don kuwa ni bakon Sarkin Bambara ne, tun daga Sego ya sa yaronsa ya roko ni, saboda haka ba su da ikon taba bakon Sarki. Su bar ni in kwana, gobe wucewa zan yi. Da suka ji haka suka kyale ni amma suka ce lalle sai in hau wani mataki don duk mutanen garin su gan ni. A kan matakin nan aka tilasta ni na zauna har zuwa faduwar rana, mutane kuwa sai turereniya su ke yi don su gan ni, sai ka ce wanda za a kashe.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
bukarmada@hotmail.com
WhatsApp: +2348021218337
Telegram: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada