SHARHIN FIM ƊIN THOR THE DARK WORLD



SHARHIN FIM ƊIN THOR: THE DARK WORLD

* Bada Umarni: Alan Taylor

* Ɗaukar Nauyi: Kevin Feige

* Rubuta Labari: Don Payne/Robert Rodart

* Tsarawa: Christopher Yost/Stephen McFeely/Christopher Markus

Thor: The Dark World Fim ɗin jarumta ne da aka fitar da shi a cikin shekara ta 2013 a Ƙasar Amurka. Labarin fim ɗin ya samo asali ne daga littattafan almara mai suna THOR wanda Stan Lee, Larry Lieber da Jack Kirby suka rubuta a ƙarkashin kamfanin Marvel Comics. Kamfanin Marvel Studios shi ne ya ɗauki nauyin shirya fim ɗin, yayin da Kamfanin Walt Disney Motion Pictures ya rarraba shi. Fim ɗin shi ne na biyun Fim ɗin Thor Da ya fita a 2011, kuma shi ne Fim na takwas daga cikin Fina-Finan duniyar Marvel mai suna Marvel Cinematic Universe (MCU).

Wannnan Fim ya sha suka a wajen 'yan kallo da ma wasu masu sharhin Fina-Finai a lokacin da ya fita, sai dai hakan bai hana shi kawo maƙudan kuɗaɗe a harkar Kasuwancin Fina-Finai na duniya ba, domin Fim ɗin ya kawo kuɗi kimanin Dala miliyan $644, hakan yasa ya zama Fim na goma daga cikin Fina-Finan da suka fi kowanne kawo kuɗi a 2013. An yi na ukun Fim ɗin inda aka sa masa suna THOR: Ragnarok.

LABARIN FIM ƊIN

Shekaru aru-aru da suka gabata, Sarki Bor Mahaifin Odin ya taɓa gwabza wani baƙin gumurzu da sarkin baƙaƙen Rauhanai na wancan lokaci mai suna Malekith. Malekith yayi yunƙurin samar da muggan makaman ƙare dangi ne ta hanyar yin amfani da ɗaya daga cikin duwatsun al'ajabi guda shida wanda ake kira da Aether domin ya yaƙi ilahirin halittun da ke rayuwa a tsakankanin Dauloli tara da suka wanzu. Wannan dalili ne yasa Bor ya ƙaddamar da yaƙi a kan su. Bayan an yiwa sojojin Malekith Sambaɗe-baɗe, sai Bor yasa aka binne wannan dutse a ƙarƙashin ƙasa ta yadda ba mai iya tono shi.

Abinda Bor bai sani ba shi ne, Malekith tare da wasu tsirarun dakarunsa sun samu damar arcewa bayan da suka ɓoye a wani jirgin yaƙi.

Yanzu kuma, a Ƙasar Asgard, an kulle Loki a magarƙama saboda rikichin da ya haifar a daular mutane, yayin da Thor, Fandral, Volstagg da kuma Sif suka je yaƙi da wasu 'yan sumame a Ƙasar ɗaya daga cikin abokan su mai suna Hogun wato Vanaheim.. Wannan shi ne faɗa na ƙarshe da akayi don ganin an Samar da zaman lafiya a tsakanin Daulolin tara tun bayan sabunta gadar da ke baiwa mutanen Asgard damar ziyartar sauran Lardojin mai suna Bifrost. Bugu da ƙari, a daidai wannan lokaci ne kuma jama'ar Asgard suka fahimci cewa kawalwalniya tana dab da faruwa a tsakanin Daulolin tara, kuma faruwar hakan shi zai baiwa dukkan Daulolin damar kasancewa a jere kai tsaye, wannan zai sa ƙofofin shiga sauran Lardunan suma su kasance a jere kuma a kusan ko'ina.

A can birnin Landan kuwa, Dakta Jane Foster tare da Mataimakiyar ta Darcy Lewis sun gano wani tsohon gini wanda ɗaya daga cikin irin waɗannan ƙofofi ya bayyana a cikin sa. A garin dube-duben wannan wuri ne Jane Foster ta faɗa wata Daular daban bayan ta shiga cikin irin waɗannan ƙofofi ba tare da ta sani ba, a nan ne fa wannan dutsen al'ajabi wanda ya narke izuwa wani jan hayaƙi ya shige cikin jikinta. Kasancewa Heimdall yana da baiwar ganin kusan komai dake tsakanin daulolin tara, sai ya zamana yana baiwa Thor labarin Jane foster Lokaci Bayan Lokaci. Amma tunda wannan hayaƙi ya shiga cikin jikin ta, sai Heimdall ya daina ganin ta. Faruwar hakan ke da wuya sai ya sanarwa thor abinda ya faru.

Nan da nan Thor ya shigo wannan daula tamu domin ya duba ta, haɗuwar su ke da wuya sai ta saki ƙarfin wannan dutse ba dake cikin jikinta bisa kuskure. Wannan dalili ne ya tilastawa Thor ɗaukar ta zuwa Asgard domin Odin yayi mata magani. Odin na ganin ta, sai nan da nan ya gane cewa Aether ne a cikin jikinta kuma ya bayyana cewa bayan kashe Jane foster da wannan tsafi zai yi, bayyanarsa wata alama ce ta gabatowar wata babbar masifa.

Can kuma a gefe, ashe fitar wannan dutse daga maɓoyarsa yasa Malekith ya farfaɗo daga dogon Suman da yayi a cikin wannan jirgin yaƙi nasa. Ai kuwa farfaɗowarss ke da wuya sai ya Jagoranci mayaƙansa tare da mataimakin sa mai suna Algrim suka kaiwa Asgard wani mummunan harin sumame. A yayin wannan hari, Malekith yana ta neman Jane foster Domin ya fahimci cewa Aether ɗin yana tare da ita, a wannan yaƙi da akayi ne dai aka kashe mahaifiyar thor wato Frigga Yayinda tayi yunƙurin kare Jane foster. Da yaƙi yayi zafi, dole ta sa Malekith da Algrim suka fece ba tare da samun biyan buƙata ba.

Duk da cewa Odin ya hana thor barin Asgard, sai da Thor ya tafi ta hanyar neman taimakon Loki wanda dama ya san wata ɓoyayyiyar hanya ta zuwa daular Rauhanai wato Svartalfheim. Volstagg da Sif sai suka tare dakarun Asgard, shi kuma Fandral ya taimaka wajen tserewar su. A yayin da suka je Svartalfheim, sai Loki ya yaudari Malekith har ya kai ga cire Aether ɗin daga jikin Jane foster, Shi kuma Thor sai yayi yunƙurin lalata aether ɗin da gudumarsa amma bai samu nasara ba domin Malekith ya riga ya haɗe da Aether ɗin.

Loki ya samu mummunan rauni da ya jawo masa mutuwa a yayinda ya kashe Algrim. Daga nan sai thor da Jane suka bi ta ɗaya daga cikin waɗannan ƙofofi suka isa Landan kai tsaye. A can ne suka iske Dakta Erik Selig ya samu ɗan ƙaramin taɓin hankali tun bayan afkuwar rikicin New York.
A nan ne suka fahimci cewa Malekith so yake yi ya dawo da martabar baƙaƙen rauhanai ta hanyar sakin aether a tsakiyar mahaɗar daulolin tara dake Greenwich.

Thor da Malekith sun yi gagarumar fafatawa inda a ƙarshe su Dakta Erik suka taimaka masa wajen tura Malekith izuwa Svartalfheim inda jirgin yaƙin sa ya danne shi ya mutu. Bayan ƙura ta lafa sai thor ya koma Asgard inda ya ƙi amsar tayin da Odin yayi masa na hawa kan karagar mulki, tare da faɗa masa irin ƙoƙarin da Loki yayi. Bayan ya tafi ne sai aka nuno Odin ɗin ya rikiɗa ya zama Loki. Ashe ba mutuwa yayi ba.

A wata fitowa ta ƙarshe, an nuno Volstagg da Sif yayin da suka ziyarci wani mutum da ake kira 'the Collector', inda suka miƙa masa aether domin ya aje, Kasancewar akwai dutsen al'ajabi ɗaya a Asgard a matsayin 'tessaract', bai kamata a ajiye duwatsun al'ajabi guda biyu a waje guda ba. Bayan sun tafi ne sai mutumin yake bayyana sha'awar sa ta son ganin ya mallaki dukkan duwatsun al'ajabi guda shida. Sai kuma thor da Jane waɗanda aka nuno su suna holewar su.

JARUMAN FIM ƊIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO A CIKIN SA

* Chris Hemsworth - Thor

* Natalie Portman - Jane Foster

* Tom Huddleston - Loki

* Anthony Hopkins - Odin

* Stellan Skorsgard - Erik Selvig

* Idris Elba - Heimdall

* Christopher Eccleston - Malekith

* Adewale Akinnuoye Agbaje - Algrim

* Kat Dennings - Darcy Lewis

* Ray Stevenson - Volstagg

* Zachary Lewis - Fandral

* Tadanobu - Hogun

* Jaimie Alexander - Sif

* Rene Russo - Frigga

* Alice Krige - Eir

* Chris O'Dowd - Richard

* Benicio del Toro - collector

* Tony Curran - Bor

 * Chris Evans - Captain America



<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________

●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees 

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees 

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees 
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...
Post a Comment (0)