TUN KAFIN AURE 47

TUN KAFIN AURE💐47




Dole ta ajiye fushin ta koma kan kujera ta zauna. Tana zama ya soma dariya ai na zata kinyi short service ne shiyasa kika dogare a tsaye kamar soja. Dan turo baki tayi tana harararsa... shafa kansa yayi yace God how i missed that. Hafsi don Allah dan dawo nan ki zauna. Kujerar  gaban gadon ta kalla daya nuna ta kawar da kai gefe sai hawaye. Kamar tana kara masa ciwo da kukanta ya taso a hankali ya dawo kusa da ita akan wata doguwar kujera. Janyota yayi ya rungume ba tare da yayi magana ba sai saukar hawayensa taji a wuyanta. Tayi saurin dago kanta kukanta ya kara tsananta. Fuskokinsu ya hada suna kallon juna yana shaqar daddadan kamshin jikinta. Ki yafe min Hafsa, ki yafe...bakinsa ta rufe da hannunta daya wanda yasha lalle mai kyau tace Allah Ya yafe mana baki daya. Hannun nata ya zare ya cigaba da magana. Nasan na zalunci kaina da irin rayuwar danayi adopting tun kafin nayi aure. Na janyo ma kaina da duk wanda ya rabeni bacin rai da bakin ciki. A yau nayi dana sanin duk wani shaye shaye da bin mata dana yi, rashin kyautatawa iyaye da keta dokokin Allah. Kuka Junaid yake sosai da sauti Hafsi ta kara rungume shi sosai tana share masa hawaye. Kasan lesson din dana dauka a rayuwarmu? Ya girgiza kai tace Allah Yana bawa bayinsa chance din tuba da dama don baa makara da tuba sai an mutu. Kaddarar aurenka tasa nayi abinda ban taba tunanin yi ba kaima kuma kabar abinda kake yi. Ni bazan dauki fushi da kai ba don idan Allah Ya yafewa bayinSa baya rike su ko Ya cigaba da kamasu dashi. Ni da kai duk da sauran musulmi duk muna bukatar inganta imaninmu mu tsayar da zukatanmu wuri guda a hanyar neman lahira. Kudi ba hauka bane face wani nau'i na jarabawa daga Allah. Sai dai munyi rashin saa da yawa cikinmu musammam 'ya'yan musulmi idan muka ganmu ko iyayenmu  a madafan iko a kasar nan sai muyi ta barna da dukiyar da ba tamu ba. Yace hakane kuma gashi da sanin iyayenmu muke yi. Zanyiwa Alhaji magana kinga duk abinda nayi a da bai taba hanani kudi ba. Nagode da Allah Ya hadani dake Allah Ya yi miki albarka tace amin. Dago fuskarta yayi yana kokarin kissing dinta ta sake sunkuyar da kai. Au bayan duk kin gama zance ni shine zaki wani sunkuyar da kai kasa. Dama fa na gano ki tun dazu abinda kike jira kenan shiyasa kike ta wani shige min jiki. Hararar nan mai burge shi tayi masa ta tashi da sauri. Kada ka manta ni amarya ce samuna sai anyi da gaske. Yanzu ma don baka da lafiya ne. Yayi mata murmushi me kashe zuciya Hafsi Hafsi tawa Allah Ya barmu tare.




Batul Mamman💖

Post a Comment (0)