TUN KAFIN AURE 49

TUN KAFIN AURE💐49





Kana ganin Hafsi kaga amarya sai zuba kamshi take. Hamida ta kalli agogo tayi dariya kinga Hafsi karfe takwas ta wuce ki tashi ki tafi wurin mijinki don yau babu mai raka ki. Sunkuyar da kanta tayi kasa don kuwa mummy na falon. Mikewa tayi itama tana dariya rabu dasu kinji Hafsa ni sai na raka ki da kaina. Ba shiri Hafsi ta tashi da gudu ita kuma mummy ta haye sama tace bari kiga ni na tafi wurin nawa tsohon. Ku kuma kowacce ta tashi ta tafi gidanta a barni na huta. Tana bace musu Nafisa tace to nidai nayiwa Hadiza alkawarin kaiki da kaina so wuce mu tafi. Haka suka je side din Junaid ana ta hira.  Hamida na sallama ya bude yana wani harare harare sai yanzu kuka ga damar kawota. To sai da safenku yaja hannun hafsi ciki. Nafisa tace yaro kaci bashi mu kwana lafiya.

Kallon dakin take wanda ya kawatu da kayan more rayuwa kala kala. Zauna mana Hafsi Hafsi ko kauyancin ne ya motsa. Ta sha kunu yau wacece bakauyar eyye. Toooohhh ni kike zarewa idanu? Duk mace mai zarewa mijinta ido fa hukuncinta.......mamaki da jindadi ne suka ziyarci zuciyarsa da gangar jikinsa  lokacin da yaji ta hade bakinta da nasa. Sai da suka jima a haka ya rinka kokarin su hada ido taki. Kaji wani sabon salon gulmar kina wani kasa da kai kamar mutuniyar kirki. Ita kanta tayi mamakin abinda tayi. Ya kama fuskarta da hannayensa biyu...Hafsi ki fada min abinda zai karasa cika min farinciki na. Kunnensa ta kama tace I love you J dear. Tana gamawa ta hada da cizo a saman kunnen sannan ta gudu. Binta da zaiyi yaji an buga musu kofa ga wayarsa dake aljihu tana ringing. Hafsi ta dawo tace ni na ga ta kaina. Menene ya tambaya a firgice ta nuna masa hanyar kofa. Kullum aka kawoni sai wani abu ya faru. Kanne mata ido yayi kaga su Hafsi ke kuma kina bukatar kadaicewa da mijinki ko. Dundu tayi masa har yayi kara sannan ya duba mai kiran wayar. Ya nunawa Hafsi kinga ma sis ce. Yana dauka tace fito falo kai da Hafsi.

Hankalinsu duk ya gama tashi ta dauki mayafi suka tafi falon. Suna ganin Tilly Junaid ya kama hannun Hafsi zo mu tafi don yau bansan dame tazo ba. Muryar Senator suka ji yace duk su zauna. Sai a lokacin Hafsi ta gane baby ne a bayan Tilly. Nafisa tace a bakin gate muka ganta securities din wurin sun hanata shigowa. Mummy tace shine kika kwaso mana ita ko. Wasikar da Tilly ta bata ta mikawa Senator ya karanta sannan aka bawa kowa ma ya karanta. Hafsi tana gamawa taje ta rungume Tilly cike da tausayawa tace Allah Ya jikanta. Amin Hafsa nagode don Allah ku yafe mana. Kowa jiki yayi sanyi aka ce an yafe. Mummy tace to yanzu me ya kawoki? Cikin kuka ta fadi matsalarta harda labarin rayuwarta dana Samira wanda ta sani. Duk mai imani zaiji tausayin yadda aka yiwa marayun mugun riko musamman Tilly wadda kanin babanta ya bata ta kakarta kuma ta karyata zancen sai da aka ganta da ciki suka koreta.

Bayan ta gama bada labarin senator yace kinyi karatu ne. Tace eh abinda ya fara sasu bin maza kenan neman kudin makaranta. Yace to ina takardunki? Tace suna gidan da aka koro mu. To gobe kije ki dauko da murna tace to ta sunkuya zata kwance goyon senator yace ah ah ki tashi yanzu zansa dreba ya kaiku asibiti a duba lafiyar yaron. Tayi musu godiya ba adadi Hafsi ta karbi Abdallah ta rungume tana kuka. Tilly tace musu sunanta Safiya yaron kuma ga sunan da mahaifiyarsa ta zaba amma baa yi masa radin suna a kunne ba. Junaid yace khudba aka cewa. Senator ya miko hannu alamun a bashi yaron. Hafsi ta mika shi Senator Rufai yayi masa Khudba. Sannan dreba ya kaisu asibiti inda suka kwana.

Junaid ya kalli fuskar Hafsi bayan sun idar da sallar nafila yace to yau dai Allah yayi ga Hafsi Hafsi ga Junaid a daki daya saura me? Yadda yake mata wani irin kallo tace saura karatu ko. Eh haka ne fa ya mike tsaye zai cire riga bari ki sha darussa kala kala. Can na jiyo dariyarsu suna cike da farinciki.

Washegari kamar yadda yayi alqawari a gaban iyalinsa yace ko bayan ransa su kula da karatu da rayuwar Abdallah. Visa ya tura su aka yi saar samu saboda sunan senator cikin sati daya aka gama komai ya tura su Saudia inda ya samawa Safiya Jibo aiki a Nigerian embassy dake can.
Tayi musu godiya kamar ta ari baki da sake basu hakuri akan laifin da suka yi.
******************

Kowa a gajiye saboda yadda taron yayi jamaa Hafsi bata samu kanta ba sai can dare ta dauki baby Rufai junior suka shiga dakin Junaid. Tana shiga ya rungumeta cike da farin ciki haba maijego ya zaki min rowar matata da baby na. Tayi masa kiss a kumatu sorry my dear J kaga akwai mutane a gidan kuma duk saboda mu suka zo. Yace haka ne ya karbi junior to yi sauri ki min tausa kada su mama suce me nake miki. Kayi ka gama kai da tausar i just came to say goodnight. Haka zaman su ya cigaba cikin farin ciki da kwanciyar hankali. Watan Junior shida Hafsi ta fara wani laulayi ga bikin Anisa da Imran abokin Junaid.

Bayan shekara 25

Rahma ce zaune tana koyawa Al-Amin auta assignment amma rabin hankalinta yana kan tv zaa fara musabaqar karatun alquran na duniya baki daya. Ana zuwa kansa ta fara kabbara har su Junior, Ummi da Aisha suka fito. Ta kalli yayyen nata tace kunga Yaya Malam. Duk zama suka yi suka bada attention basu san sadda iyayensu suka zo suka zauna ba. Karatu yake da murya mai tsuma zuciyar mai sauraro. Ga larabci tamkar balaraben gaske. Lokacin da ya gama gaba daya falon ya kaure da kabbara. Hafsa ta kalli yaranta zuciyarta sai hamdala take tace to ku tashi muyi sallah mu taya shi addua. Junaid ya mike da sauri Mama Hafsi nine first ina fata zaki bani kyauta. Al amin yayi saurin tashi Allah nine first yau Abba don tun dazu nayi alwala. Sauran yayyen ma suka tashi kowa yace yau yayi alwala da wuri. Junaid yace kaga yan nema da baban naku kuke tsere? Duk dariya suka yi Hafsi tace zo nan babana yau kyautar taka ce. Junior yace mama dama yau tun safe kike nuna mana wariya akan wannan dan kalen. Filo ta jefa masa duk suka tashi yin nafila su taya Abdallah Muhammad adduar samun saa. Bayan sun idar Junaid yace kullum kyautar mama kuke so to nima ga tawa. Tickets ne na zuwa saudia. Zamuje umra tare da taya Abdallah murna ko baiyi na daya ba zaman nasa ma abin alfahari ne gare mu. Nan da nan gidan ya kaure da murna.

Safiya ta cire glasses din idonta ta share hawaye. Ina ma Samira nada rai ta ga danta gaban manyan malaman musulunci. Mijinta Muhammad Aswadiy yace mata cikin harshen larabci ki cigaba da yi mata addua Safiyya. Allah shine mai gafara da jin kai. Nagode sosai Abu Musab ta fada tare da murmushi. Shekararta biyu a saudia suka yi aure bayan rasuwar matarsa. Ta sanar dashi komai na rayuwarta ya ce Allay shine mai gafara da jinkai. Tare ta hada Abdallah da yaransa uku ta rike. Bayan ya shiga ciki ne Safiya ta tashi tayi sujjada tana kuka tace Ya Allah Ka yafe mana ni da Samira da dukkanin musulmi ka sakawa iyalan Alh Rufai da mijina Muhammad da alkhairi. Amin







Alhamdulillah👏🏾
Batul Mamman💖
Post a Comment (0)